Yadda Aka Taron Cika Shekara Daya Da Rasuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris

Sarkin Zazzau

Daga Isa Abdullahi Gidan Bakko,

A ranar Lahadi 20 ga watan Satumbar shekara ta 2020, rana ce al’ummar masarautar Zazzau a cikin zuciyarsu ba za su taba mantawa da wannan rana ba, domin a wannan rana ce marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya rasu a babbar asibitin sojoji da ke garin Kaduna.

A lokacin da labarin rasuwar mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ta fara bayyana duk inda ka duba a Zariya babu abin da za ka gani sai taruwan al’umma suna tattauna yadda suka ji labarin rasuwar, a yayin da kuma a wasu wurare, za ka ga al’umma a cikin hawaye su na kukar wannan babbar rashin da aka yi.

Inda babban labarin ya ke shi ne, yadda aka yi jana’izar marigayin, domin duk wanda ya kasance a wajen jana’izar, zai bayar da labarin al’umma sun cika fadar Zazzau makil, babu masaka tsinke, duk inda ka duba a fadar Zazzau, al’umma za ka yi arba da su a cikin juyayi da kuma yadda suke yin addu’o’i a bayyane wasu kuma a sirrance, domin neman rahama da kuma tsira ga marigayin.

Wani kuma abin trihi da ya faru a ranar da mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya rasu, duk kofofin da suke birnin Zariya, duk inda ka za ga za ka al’umma ne ke shigo wa birnin Zariya domin halartar jana’izar marigayi Sarkin Zazzau.

A wannan rana ta Lahadin da Allah ya karbi ran marigayin, cikin birnin Zariya ta cika– ta– batse da al’umma da suka hada da manyan sarakuna da manyan ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da masana ilimi da suka fito daga ciki da wajen jihar Kaduna, domin samun damar halartar wannan jana’izar marigayin, abin tarihin da ya faru a wannan rana shi ne, akasarin al’umma, sun bayyana taruwar jana’izar dasu a rayuwarsu, ba su taba gani ko kuma halartar mai kama da shi ba, na taruwar jama’a.

Wani batu na tarihi da al’ummar masarautar Zazzau ba za su taba mantawa da shi ba shi ne na yadda aka shafe rana fiye da goma sha biyar, duk lokacin da ka je Fadar Zazzau, sai ka sami fadar tamkar ba a yi jana’izar marigayin ba, wato tun safe a duk rana, jama’a ne ke turuwar zuwa fadar daga sassan Nijeriya da kuma wasu kasashe daban–daban na wannan duniya.

Halayensa Da Al’ummar Zazzau Ba Za Su Manta Ba

  1. Zaman lafiya, Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, shugaba ne abin koyi ga duk wani batu da ya shafi zaman lafiya, ba masararutar Zazzau kawai ba a Nijeriya baki daya, domin in marigayi zai furta kalamai uku, daya daga ciki shi ne kiran al’umma a yi tattalin zaman lafiya da kuma hakuri da juna.
  2. Hakuri, duk wanda ke kusa da marigayin su kan sifanta shi da mutum ne mai hakuri ga duk wasu abubuwa da suka taso masa, musamman abin da ya shafi shi kansa, amma abin da ya shafi al’umma, a nan ne ya ke nuna matukar damuwarsa kan matsalolin da al’umma ke ciki, baya tsayawa, sai ya warware wa al’umma matsalolin da suke ciki.
  3. Hikima, Allah ya azurta marigayi da hikimar gudanar da mulkin al’umma, ta yadda yake tafiya dai–dai da yadda al’ummarsa suke bukata, duk abin da suka ce ma sa kan wata matsala da yadda za a warware matsalar da suka shaida ma sa, zai yi yadda shawarwarin da suka kai ma sa, amma a lokacin da ya tashi warware matsalar, zai hada na shi hikimar da nasu, ya warware matsalolin da aka kai gabansa, nan take sai ya ce ai shawarwarin da ku ka bayar shi ne mafita.
  4. Iya Sulhu, Marigayi gwani ne wajen iya sulhu, musamman al’amarin da ya shafi addini, kamar ginin masallaci ko batun fili ko kuma rabon gado a tsakanin magada, a nan in batun masallaci ne, ‘yan Darika suka ce nasu kuma ‘yan Izala suka ce nasu ne, a nan bayan mai martaba ya saurari ko wane bangare, sai ya ce su je su saurare shi, a cikin dan lokaci kadan, zai sayi fili da kudinsa ya gina masallacin irin wanda ake magana akansa, sai ya tara su ya ce, ga masallaci nan guda biyu, kowa ya yi amfani da daya, ya kashe irin wannan wuta, babu wanda ya san iyakansa, a tsawon mulkin da ya yi a msarautar Zazzau na shekara 45.

In kuma matsalar gadon gida ne a tsakanin magada, a nan ma marigayi zai sayi gidan magadan, ya raba masu kudin da ya saya a wajensu, bayan an gama raba gidajen, sai kuma ya raba masu wannan gida kyauta, ya kuma umurce su da su zauna lafiya a tsakaninsu.

  1. Tallafi ga ‘ya’yan talakawaa fagen ilimi, mairigayi har kwamiti na musamman ya kafa a fadarsa domin bayar da tallafin ilimi ga ‘ya’yan talawkawa da suke son ci gaba da karatu a ko wane mataki na ilimi, domin har gida musamman ya saya a kasar Sudan, domin ‘yan masarautar Zazzau da suke zuwa karatu wannan kasa, in sun je a gidan suke zama har su kammala karatunsu a ko wane mataki na ilimi, kuma yadda ya tsayu wajen ba ‘ya’yansa ilimin addini da na zamani, mai martaba marigayi haka ya ke hada ‘ya’yansa da na talakawa zuwa kasashen waje, domin neman ilimi.
  2. Gina gidajen sarauta da suke masarautar Zazzau, a matsayin marigayin da ya fito daga gidan Sarautar Katsinawa, ya yi bakin kokarinsa na ganin duk sarautar da ta fadi a daya daga gidajen sarauta na Zazzau, ya gina gidan ta nada wani ko kuma wasu na gidajen ta nada su sarautu daban–daban,wannan batu a bayyane yake, duk wanda ya san halin da masarautar Zazzau ta ke a zamanin marigayin bai kawo nakasu a ko wane gida na sarautar Zazzau ba.

Ranar 20 ga watan Satumbar shekara ta 2021, rana ce da ta yi dai – dai da shekara daya da rasuwar Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, a dalilin haka ne al’ummar musulmi suka hallara a gidan Gidan Dan Isa, domin halartar addu’o’in cikarsa shekara daya da rasuwa.

Cikin malaman da suka yi addu’a a wannan rana sun hada da Limamin Zazzau, Shekh Dalhat Kasim Imam da Na’ibin Zazzau, Malam Lamido da Sarkin Ladanai na Zazzau da Babban Limamin Tundun Wadan Zariya da Sarkin Salati na Zazzau da dai malamai da dama, inda suka yi addu’o’in neman gafara da rahama da tukuici da Aljanna Firdausi ga marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.

Wadanda suka yi tsokaci a kan rayuwar marigayin a wajen taron sun hada da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu, Uban Garin Zazzau, Alhaji Bashir Shehu Idris, Hakimin Soba, Sarkin Dawakin Tsakar Gida Na Zazzau, Alhaji Ibrahim Shehu Idris da kuma Dan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris,

 

Exit mobile version