Yadda Ake Ajiya Lambar Waya A Email

Daga Ibrahim Sabo,

Mutane da dama basu damu da ajiye lambar wayarsu a kan Email dinsu na cikin wayoyinsu ba. Amma kuma za ka ji suna koka wa a kan yadda idan wayarsu ta bata, ko kuma aka sace, shikenan sun rabu da lambobin mutanen da suka ajiye a cikin wayar kenan har abada. Duk muhimmancin lambar a wajenka to ka rabu da ita kenan. Amma manhajar Gmail din tana aiki ne a kan manyan wayoyi kawai, wato Android, iPhone da sauransu.

Duk wayar Android tana dauke da manhajar Gmail a cikin ta. Hatta ‘play store’ ba ya bude wa sai ka je Gmail din ka yi rijista. Idan daman ka yi rijista, to dora wa kawai za ka yi. Idan kuma ba ka yi rijista ba, kuma ba ka bude akwatin sako na Email din ba, to dole sai ka bude. Ba sai mun yi bayani a kan yadda ake bude Email din ba, kasantuwar kusan kowa yana da shi. Wasu ma Cafe suke zuwa a bude musu. Amma mafi yawa basu san yadda ake ajiye lambar waya a kan Email din ba. Wasu kuma suna ajiye wa a kai, amma idan sun canza waya, basu san yadda za su dawo da lambobin wayar tasu a kan sabuwar wayar da suka canza ba.

To yadda za ka ajiye lambar waya a kan Gmail dinka shi ne, idan lambobin suna kan Sim dinka na waya ne, to sai ka shiga ‘phone contacts’ wato inda lambobin wayarka suke. Idan ka shiga, a can sama, daga bangaren hagu, za ka ga wasu digo guda uku a jere (options kenan). Idan ka taba shi, zai bude.

To a can kasa za ka ga setting, sai ka taba shi. Idan ka taba shi, zai bude, sai ka duba a hankali, za ka ga import. To idan ka taba import din nan, zai bude, ya nuno Email dinka, da phone contacts, Sim 1 da Sim 2. Da kuma internal storage da kuma SD card. To a samansu za ka ga an rubuta ‘copy contacts from’. Idan lambobin da za ka kwashe suna kan Sim 1, to sai ka taba Sim 1 din. Idan kuma a Sim 2 ko phone suke, sai ka taba. Za ka ga alamar ‘mark’ ya dawo kan inda ka taba din.

To a can kasa za ka ga Nedt, sai ka taba shi. Idan ka taba shi, zai kai ka mataki na gaba. Zai nuno maka ‘copy contacts to’ sai ka taba kan Email (Gmail) din naka. Idan ka kara duba can kasa za ka kara ganin Nedt. Idan ka taba nedt din, zai nuno maka lambobin da suke kan Sim dinka duka. A can sama za ka ga an rubuta selected. Idan ka taba selected din, zai nuno maka ‘select all’ sai ka taba shi. A gefen select all din za ka ga OK, sai ka taba shi. To sai ka dan jira, lambobin zasu sauka a kan wayarka. Idan suka kammala sauka, zai sanar da kai. Zai nuno maka alamar sun sauka.  Zai rubuto maka ‘Contacts copied successful’. (Notification).

Muhimmancin ajiye lambobin waya a kan Email (Gmail) shi ne, ko da wayarka ta bata, ko ka canza waya, to lambobinka suna nan a ajiye a kan email din. Babban abin da ake so shi ne, kar ka manta email da password din naka. Duk lokacin da ka canza waya, to cikin sauki za ka dawo da lambobin naka. Yadda za ka yi shi ne, a kan wayar, za ka je wannan manhajar Gmail din, sai ka saka email da password din naka da kake amfani da shi a waccar wayar taka. Idan ka saka, sai ka tafi kan setting na cikin wayar. A cikin setting din, za ka ga ‘account’ sai ka taba shi. Idan ka taba shi, zai nuno maka manhajoji (applications) da yawa ciki har da email dinka.

To sai ka taba email din. Zai nuno maka abubuwa kamar haka, email dinka, Google account da account sync. To sai ka taba account sync din. Zai sake bude wa, sai ka duba contacts, sai ka taba shi sau biyu. Wato ka kashe, ka kunna kenan. To idan ka dan jira na minti daya, duk lambobin da ka ajiye a kan email din nan za su dawo cikin wayarka. Idan ka koma kan phone contacts duk za ka gansu.

A mako mai zuwa Insha Allah za mu yi magana a kan yadda mutum zai kare kansa daga kwacen Facebook da WhatsApp, kasantuwar yanzu kwacen account din ya dawo ruwa tsundum

Exit mobile version