Ibrahim Sabo">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KIMIYYA

Yadda Ake Ajiye Lambar Waya a Email

by Ibrahim Sabo
December 6, 2020
in KIMIYYA
3 min read
Yadda Ake Ajiye Lambar Waya a Email
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A wannan makon za mu kawo yadda ake ajiye lambar waya Email da kuma muhimmancin ajiye lambar waya a akwatin sako na Email (Gmail) din.
Yadda Ake Ajiye Lambar Waya A Email
Mutane da dama basu damu da ajiye lambar wayarsu a kan Email dinsu na cikin wayoyinsu ba. Amma kuma za ka ji suna koka wa a kan yadda idan wayarsu ta bata, ko kuma aka sace, shikenan sun rabu da lambobin mutanen da suka ajiye a cikin wayar kenan har abada. Duk muhimmancin lambar a wajenka to ka rabu da ita kenan. Amma manhajar Gmail din tana aiki ne a kan manyan wayoyi kawai, wato Android, iPhone da sauransu.
Duk wayar Android tana dauke da manhajar Gmail a cikin ta. Hatta ‘play store’ ba ya bude wa sai ka je Gmail din ka yi rijista. Idan daman ka yi rijista, to dora wa kawai za ka yi. Idan kuma ba ka yi rijista ba, kuma ba ka bude akwatin sako na Email din ba, to dole sai ka bude. Ba sai mun yi bayani a kan yadda ake bude Email din ba, kasantuwar kusan kowa yana dashi. Wasu ma Cafe suke zuwa a bude musu. Amma mafi yawa basu san yadda ake ajiye lambar waya a kan Email din ba. Wasu kuma suna ajiye wa a kai, amma idan sun canza waya, basu san yadda za su dawo da lambobin wayar tasu a kan sabuwar wayar da suka canza ba.
To yadda za ka ajiye lambar waya a kan Gmail dinka shi ne, idan lambobin suna kan Sim dinka na waya ne, to sai ka shiga ‘phone contacts’ wato inda lambobin wayarka suke. Idan ka shiga, a can sama, daga bangaren hagu, za ka ga wasu digo guda uku a jere (option kenan). Idan ka taba shi, zai bude. To a can kasa za ka ga setting, sai ka taba shi. Idan ka taba shi, zai bude, sai ka duba a hankali, za ka ga import. To idan ka taba import din nan, zai bude, ya nuno Email dinka, da phone contacts, Sim 1 da Sim 2. Da kuma internal storage da kuma SD card. To a samansu za ka ga an rubuta ‘copy contacts from’. Idan lambobin da za ka kwashe suna kan Sim 1, to sai ka taba Sim 1 din. Idan kuma a Sim 2 ko phone suke, sai ka taba. Za ka ga alamar ‘mark’ ya dawo kan inda ka taba din.
To a can kasa za ka ga Nedt, sai ka taba shi. Idan ka taba shi, zai kai ka mataki na gaba. Zai nuno maka ‘copy contacts to’ sai ka taba kan Email (Gmail) din naka. Idan ka kara duba can kasa za ka kara ganin Nedt. Idan ka taba nedt din, zai nuno maka lambobin da suke kan Sim dinka duka. A can sama za ka ga an rubuta selected. Idan ka taba selected din, zai nuno maka ‘select all’ sai ka taba shi. A gefen select all din za ka ga OK, sai ka taba shi. To sai ka dan jira, lambobin zasu sauka a kan wayarka. Idan suka kammala sauka, zai sanar da kai. Zai nuno maka alamar sun sauka. Zai rubuto maka ‘Contacts copied successful’. (Notification). Idan ka koma cikin contacts na wayarka za ka gansu.
Muhimmancin ajiye lambobin waya a kan Email (Gmail) shi ne, ko da wayarka ta bata, ko ka canza waya, to lambobinka suna nan a ajiye a kan email din. Babban abin da ake so shi ne, kar ka manta email da password din naka. Duk lokacin da ka canza waya, to cikin sauki za ka dawo da lambobin naka. Yadda za ka yi shi ne, a kan wayar, za ka je wannan manhajar Gmail din, sai ka saka email da password din naka da kake amfani da shi a waccar wayar taka. Idan ka saka, sai ka tafi kan setting na cikin wayar. A cikin setting din, za ka ga ‘account’ sai ka taba shi. Idan ka taba shi, zai nuno maka manhajoji (applications) da yawa ciki har da email dinka. To sai ka taba email din. Zai nuno maka abubuwa kamar haka, email dinka, Google account da account sync. To sai ka taba account sync din. Zai sake bude wa, sai ka duba, za ka ga contacts, sai ka taba shi sau biyu. Wato ka kashe, ka kunna kenan. To idan ka dan jira na minti daya, duk lambobin da ka ajiye a kan email din nan za su dawo cikin wayarka. Idan ka koma kan phone contacts dinka duk za ka gansu.
Sai mun hadu a mako mai zuwa, a kan wani sabon maudu’in.

SendShareTweetShare
Previous Post

Haduwar Jini

Next Post

Shugaban Kungiyar AFGSAN Reshen Jihohin Arewa Maso Yamma Ya Yi Kira Ga Gwamnatin Tarayya

RelatedPosts

Fasahar Zamani

Ma’anar Wasu Sabbin Fasahar Zamani (I)

by Ibrahim Sabo
2 days ago
0

A matsayinmu na wadanda muke rayuwa a wannan zamani na...

Tsokaci Kan ‘WI-FI’ Da Yadda Ake Amfani Da Shi

Tsokaci Kan ‘WI-FI’ Da Yadda Ake Amfani Da Shi

by Ibrahim Sabo
4 weeks ago
0

Mafi yawan mutane suna ganin Wi-Fi a wayarsu, amma wasu...

Miyagun Hanyoyin Mu’amala A Dandalin Sada Zumunci (Social Media)

by Ibrahim Sabo
1 year ago
0

Ga wadanda suke bibiyar wannan shafi tun farkon samuwarsa a...

Next Post
Shugaban Kungiyar AFGSAN Reshen Jihohin Arewa Maso Yamma Ya Yi Kira Ga Gwamnatin Tarayya

Shugaban Kungiyar AFGSAN Reshen Jihohin Arewa Maso Yamma Ya Yi Kira Ga Gwamnatin Tarayya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version