Yadda Ake Bikin “Ranar Girbi Ta Manoman Kasar Sin”

Daga Saminu Hassan

 

Bahaushe kan ce “Noma tushen Arziki”. A kan kuma yiwa noma kirari da cewa “Na duke tsohon cikini, kowa ya zo duniya kai ya tarar”, duk wadannan karin magana ana danganta su da sana’ar Noma ne saboda muhimmancin sa ga rayuwar bil adama a jimlace, kasancewar tun fil azal, dan Adam na dogaro ne ga nemo abincin da zai ci domin ya rayu da farko, kafin sauran bukatu na rayuwa su biyo baya.

A nan kasar Sin, sana’ar noma ta samu ci gaba mai armashi, tun daga yanayin da ake gudanar da ita a salo na gargajiya, zuwa sana’a da ta baiwa kasar gagaruwar gudummawar raya tattalin arziki da kyautata zamantakewar al’umma baki daya. Gwamnatin kasar da daukacin al’ummar Sinawa sun gamsu da tasirin noma ga ci gaban kasar su, don haka ne ma a hukumance, aka ware rana ta musamman domin yaba gudummawar manoman kasar, bikin da aka yiwa take da “ranar girbi ta manoman kasar Sin”.

Ana nuna fasahohin aikin gona yayin ranar girbi ta manoman kasar Sin

An kaddamar da wannan rana ne a shekarar 2018. Ana kuma gudanar da shi duk shekara a lokacin kaka, daidai lokacin da tsawon dare ke daidai da sa’o’in rana. Kuma manufarsa ita ce zaburar da miliyoyin manoman kasar ta yadda za su ji karin karsashi, da kara zage damtsen kirkire kirkire don bunkasa sana’ar ta noma. Kaza lika ranar ta samar da damar musamman ta martabawa, da jefa farin ciki a zukatan manoma, ta yadda za su rika tuna irin nasarori da suke samu a sana’ar su.

Gudanar da ranar girbi ta manoman kasar Sin na nuni ga irin nasarori da manoman Sin suka cimma a fannin raya karkara, da samar da sauye sauye na ci gaba, kamar dai yadda hakan ke kunshe cikin al’adun noma na kasar Sin tun fil azal.

Ana kayata sassan filayen noma domin yayata manufar ranar girbi ta manoman kasar Sin

Kafin ayyana wannan rana ta girbi a hukumance, manoman kasar Sin na gudanar da bukukuwa daban daban a irin wannan lokaci na kaka, amma bayan nazari mai zurfi, sai kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis (JKS) mai mulkin kasar ya amince da ware lokaci na musamman, bisa kalandar gargajiya ta Sin domin wanzar da shagulgulan bikin a hukumance, inda a bana ake gudanar da su a ranar 23 ga watan nan na Satumba, karkashin jagorancin ma’aikatar noma da harkokin yankunan karkara, da wasu hukumomin masu nasaba da harkar noma.

 

Tarihin Ranar Girbi

Manoma na sahun gaba a rukunonin al’ummar Sinawa mafiya rinjaye, su ne kuma tushen jagorancin jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin. Manoman kasar Sin sun ba da gagarumar gudummawa a fannoni da dama na ci gaba a tarihin kasar, ciki har da tallafawa manufofin juyin juya halin kasar, da gine-ginen raya kasa, da kuma aiwatar da sauye-sauye. Don haka ne ma babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Xi Jinping ya sha jaddada cewa, ba za a taba yin watsi da manoma ba, kana ba za a taba yin watsi da yankunan karkara ba.

Ana shirya shagulgula domin ranar girbi ta manoman kasar Sin

An dai amince da gudanar da rnar girbi ta manoman Sin a wata muhimmiyar gaba da kasar ta cimma nasarar yaki da talauci, a kuma lokacin da ake aiki tukuru don gina al’umma mai wadata a dukkanin fannoni, kuma mafari na aiwatar da manufofin farfado da yankunan karkara, wadanda suka dace da sabbin bukatu da muradu na sabon zamani da ake bukatar cimmawa.

A shekarar 2018 ne kasar Sin ta cika shekaru 40 da fara aiwatar da sauye sauye a cikin gida da bude kofa ga waje. Kuma an fara aiwatar da sauye sauyen ne daga sassan karkara. Don haka “ranar girbi ta manoman kasar Sin” tana baje kolin nasarori da manoman kasar suka cimma a fannin aiwatar da sauye sauye da samar da ci gaba, da baje kolin kirkire kirkire da manoman kasar suka samar, da karfinsu na ingiza gina al’ummar gurguzu ta zamani.

 

Alfanu Uku Na Bikin Girbi

‘Yan makaranta na samun damar ziyartar gonaki albarkacin ranar girbi ta manoman kasar Sin

 

Sanin kowa ne cewa, bukukuwa mafiya tasiri a tsakanin al’umma su ne wadanda ke da jigo a tarihin ta. Da farko, ranar girbi ta manoman kasar Sin tana da tasirin yayata muhimman ayyuka uku na bunkasa yankunan karkara. Hakan ne ma ya sanya babban sakataren JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada cewa, batutuwan noma da rayuwar manoman karkara, su ne kashin bayan raya tattalin arziki da inganta zamantakewar al’ummar kasar. Kuma wannan ranar ta girbi ta manoman kasar Sin da ake gudanarwa duk shekara, zai iya karfafa manufofi uku na ci gaban karkara, wadanda ke da muhimmanci a mataki na jam’iyya da gwamnatin kasar.

Kaza lika wannan biki yana ba da damar karrama manoma, da faranta ran su, da yaba kwazon miliyoyin manoman kasar Sin. A yayin bikin ana baiwa manoma damar nishadantuwa daga jerin shagulgula, da suka kunshi bikin al’adu, da nune nunen fasahohin kabilu daban daban, da ma nasarorin da sana’ar noma ya samu a sabon zamanin da muke ciki.

Ana shirya taruka musamman domin bitar nasarorin da manoma ke samu albarkacin ranar girbi ta manoman kasar Sin

Har ila yau, bikin na samar da zarafi na yayata ci gaban manoma da fayyace kyawawan al’adun su. A gabar da ake gaggauta bunkasa ayyukan masana’antu da raya birane, al’adun gargaji na manoma na gushewa sannu a hankali. Don haka wannan biki ya zamo tamkar wani jigo ne dake baiwa al’ummar Sinawa damar waiwayar tarihi, da tuna al’adun baya, domin magance gushewar abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni.

 

Tarihin Da Tasirin Ranar Ga Bil Adama

Ranar girbi ta manoman kasar Sin ba karamin biki ba ne. Domin kuwa ya wuce bikin da miliyoyin manoma ke murnar girbin amfanin gona kawai, duba da cewa albarkacin sa, jama’ar kasar Sin baki daya na amfani da shi wajen yin addu’o’in cin gajiya daga yabanyar da suka samu. A mahanga ta tarihin al’adu, kaddamar da irin wannan biki a mataki na kasa na taimakawa wajen jaddada gudummawar manoman kasar Sin, ta yadda hakan zai wanzu cikin sabon zamani da muke ciki, tare da martaba sana’ar noma, da gudanar da shagulgulan murnar samun yabanya.

Sin kasa ce babba a fannin noma, don haka samar da inganci a sana’ar noma na zamani muhimmin batu ne ga kasar. A hannu guda kuma, sanya batun ci gaban jama’a gaban komai, muhimmin jigo ne cikin tunanin shugaba Xi Jinping, karkashin salon gurguzu mai halayyar musamman a sabon zamani, kana hakan tushe ne da ya zama wajibi kasar ta nacewa a fannin noman zamani.

 

Gudummawar Yankunan Karkara

Da farko dai, ranar girbi ta manoman kasar Sin tana da tasirin kara zaburar da manoma, ta yadda za su kara maida hankali ga raya yankunan su. Manoma su ne babban ginshiki na ayyukan noma da raya karkara, su ne kuma ke ingiza manufofin kasa na farfado da yankunan karkara. Aikin farfado da karkara aiki ne na manoma, kuma ya zama wajibi a ba su wannan dama. Gudanar da bikin girbi na ba su damar shiga a dama da su, tare da sadaukar da kan su ga wannan aiki, har a kai ga cimma manyan nasarori da aka sanya gaba. Kari kan haka, bikin na girbi na karfafa gwiwar manoman kasar Sin wajen hada gwiwa da juna, da mayar da su tsintsiya madaurin ki daya, yayin da ayyukan su ke tafiya kafada da kafada da sauran muhimman ayyukan farfado da kauyuka.

Sana’ar noma ta samu babban ci gaban fasahohi a kasar Sin

Abu na biyu, wannan biki na kasancewa dama ta samar da kyakkyawan yanayin aiwatar da matakan farfado da yankunan karkara. Aikin da ke zama ginshikin farfado da tattalin arziki da zamantakewar al’umma, musamman ma manoman kasar. Har ila yau, bikin na karfafa yanayin aiwatar da dabarun raya karkara. Shekarar 2018 lokacin da aka kaddamar da bikin a hukumance, ta kuma yi daidai da shekarar farko ta aiwatar da dabarun raya karkarar kasar Sin. Kaddamar da bikin girbi a shekarar farko ya ingiza matakan shigar da albarkatu cikin aikin, hakan ya kuma bunkasa raya masana’antun dake yankunan karkara, da habaka kirkire kirkire. A hannu guda kuma, hakan ya kara fadada farfadowa, da raya al’adu, da kare muhallin halittu, yayin da kuma tsara dabarun farfadowa ke inganta ci gaban karkara.

Na uku, bikin na share hanyar zakulo bukatun manoma na samun karin ingancin rayuwa. Masana na ganin arzikin al’umma bai takaitu ga samun wadatar kayayyakin bukata kadai ba, maimakon haka ingancin rayuwa da samun walwala muhimman sassan ne da bil adama ke bukata. Gudanar da wannan biki na nuni ga ingancin rayuwar manoma. Kuma ta hanyar sa, Sin na nunawa duniya tarin nasara da sana’ar noma ke samarwa, da irin alfanu da manoman ke samu daga ribar sana’ar su, da karin ingancin ruhin rayuwar su ta fuskar bunkasa al’adu, da yayata karin yabanya da ake samu wanda hakan ke nuni ga ci gaba da sana’ar ke samu.

Ko shakka ba bu, sana’ar noma na kara samun karbuwa a Sin, ana iya ganin sabbin gidaje ingantattu a yankunan karkara, yayin da manoma ke zaune cikin su cikin lumana da wadatar zuci.

Cikin wuraren da aka gudanar da shagulgulan murnar ranar girbi ta manoman kasar Sin a bana, akwai birnin Changsha fadar mulkin lardin Hunan. An gudanar da bukukuwa iri daban daban a muhimman dandaloli biyu, ciki har da nune nunen wasannin gargajiya, da kayayyakin amfanin gona, da dandana nau’oin abinci dadan daban.

Manyan jagororin kasar Sin sun shiga an dama da su a bikin na bana, yayin da a bangaren manoma, dandalin manoman shinkafa da hukumar tabbatar da samar da isasshen abinci, da hukumar kasa mai lura da raya al’adun manoma da nune nune, suma sun taka rawar gani a bikin na lardin Hunan.

Yayin da duniya ke ci gaba da samun nasarori a fannonin kimiyya da fasaha, da harkokin kiwon lafiya da raya ilimi, da fannin binciken sararin samaniya, da fasahohin sadarwa, da kwaikwayon tunanin bil adama, kasar Sin na ci gaba da tafiya tare da zamani a wadannan fannoni, amma fa duk da haka bata manta da tushen ta ba, don haka ne ma mahukuntan Sin ke ci gaba da martaba noma, da al’amura masu nasaba da sana’ar, a matsayin ta na tushen bunkasar kasar tun daga kaka da kakanin. (Saminu Alhassan daga CRI Hausa)

Exit mobile version