Connect with us

TASKIRA

Yadda Ake Dafa Kazar Amare Da Hada Maganin Sanyi Sadidan – Fareeda Abdullahi

Published

on

Kowa ya san ba irin dahuwar da aka saba da ita ake wa kazar amare ba, akwai yadda ake yin ta ta musamman, to amma yaya ake yi? Sannan sanyi yana daga cikin abin da yake ci wa ma’aurata tuwo a kwarya a zamantakewarsu ta aure, shin akwai yadda za a yi su ma’auratan su samar wa kansu mafita da kansu? Amsoshin wadannan duk suna cikin tattaunawar da muka yi da bakuwarmu ta wannan makon har ma da kari musamman kan abin da ya shafi kasuwanci ga ‘ya mace. Ga hirar kamar haka:

Da farko za ki fada wa masu karatu cikakken sunanki da sunan da aka fi saninki da shi…
Sunana Fareeda Abdullahi Ibrahim wasu na kirana Princess Feedy lokacin da ina budurwa amma yanzu an fi sanina da Feedy Bash.

Ko za ki fada wa masu karatun dan takaitaccen tarihinki?
Ni haifaffiyar garin Kano ce Marmara ‘yan walda, na yi makarantar firamare da sakandare duk a garin Kano daga bisani na yi aure a Bachirawa Waziri Gidado Street, mijina na zaune a Legas daga baya na koma can gaba daya, a yanzu ina da shekaru 25 da haihuwa. Amma ina zuwa Kano akai akai.

Shin yanzu kina ci gaba da karatu ne ko yin wata sana’a ko kuma zaman gida kawai kike?
Gaskiya ban cigaba da karatu ba, sana’o’i nake da dama dan ba abun da ba na siyarwa in dai zan siyar na samu riba ko yaya na yi.

Kamar wadanne irin kaya kike siyarwa?
Less, Atamfofi, Shaddodi, Takalma, Jakunkuna, Fashion, Humra, Turaren wuta, Kayan yara maza da mata, Mayafai, Hijabai, Kayan kitchen. Sauran sun hada da Maganin sanyi, Maganin gyaran nono, Maganin mata kala-kala, Maganin kara girman mazaunai, Maganin kwayoyin cuta na al’aura, kai da sauransu da yawa sosai, gaskiya duk abun da ya samu siyarwa na ke.

Za ki kamar shekara nawa kina wannan sana’ar?
Gaskiya na dade ina yi tun ina budurwa na ke yi to daga baya sai jarin ya dan yi baya kin san ‘yammata sai a hankali anko kadai ya wawashe jarin
To bayan na yi aure mijina kuma ya kuma bani jari shi na yi, abun dai ya habaka gaskiya yafi na da sosai.

Me ya ja hankalinki har kika fara wannan sana’ar?
Gaskiya abun da ya ja hankali na na fara Sana’a saboda na dogara da kai na ba na san na rabu da wani musamman akwai lokacin da kake bukatar abu mai yi maka bashi da hali amma in dai kana juya dari da kwabo ba zaka rasa na kashewa ba musamman da ya kasance ‘yammata muna da yawan bukatu anko kayan kyale kyale to in dai ka rabu da saurayi tabbas wani ba zai ma dan Allah ba, shi ya sa na bukaci aban jari a gida kuma ban sha wata matsala ba a kai ban. Bayan na yi aure ganin ban da wasu bukatu na mike kafa amma mijina abun alfaharina dan aljanna ya dage sai na ci gaba haka ko aka yi, Alhamdulillah na ci gaba kuma na samu ci gaba fiye da baya sosai.

A cikin abubuwan da kika jero su wanda kike siyarwa ciki akwai wanda kike sarowa akwai kuma wanda naga kamar ana iya hadawa musamman magungunan da kika ambata da turaruka shin ke kike hada su da kanki ko kuwa suma saro su kike yi?
A’a magani ina hadawa da kaina dan wasu ma itatuwan nake hadawa sai kai kuma ka hada kayanka musamman na sanyi da na nono da sauransu. Turare da kaina nake hadawa, ragowar kuma ina sarowa ne gaskiya.

A Ina kika koyi ita wannan sana’a har kika iya hadawa?
Na koye ta ne a wajen mahaifiyata Hajiya Abu tana nan a Marmara ‘yan walda dan a kofar gidan mu ake waldar duka a wajen ta na koya kuma har yau tana nan ta na yi tana saidawa tana kuma koyawa, musamman Humra da turaren wuta tana na amare dana jego dana tsuguno dana kaya dana daki dukansu muna yi.

Daga Lokacin da kika fara ita wannan sana’a kawo iyanzu wanne irin nasarori kika samu game da sana’ar?
Gaskiya na samu nasarori da dama Alhamdulillah na samu abun da nake rufawa kai na asiri duk wani abu daya taso mun cikin ikon Allah ina samun damar kau da shi kuma Alhamdulillah na hadu da mutane da dama daga garuruwa da ban wanda ban taba tunanin gamuwa da su ba a rayuwata alhamdulillah ba abun da zan ce da Allah sai godiya.

Shin kin taba fuskantar wata matsala ko wani
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: