A gasar cin kofin Afrika na ‘yan shekaru 17, an buga wasanni da dama a tsakiyar wannan satin inda kasar Togo ta lalasa jamhuriyar Nijar da ci 2 da 1, haka ma kasar Burkina Faso ta doke Jamhuriyar Benin da ci 5 da 1, sannan a ranar laraba Nijeriya ta yi wa Cote D’Ivoire ci daya mai ban haushi.
A yau Juma’a 8 ga wannan wata na Janairu kuma, ‘yan wasan jamhuriyar Benin ‘yan shekaru 17 ke fafatawa da kungiyar kwallon kafar Togo, yayin da jamhuriyar Nijar za ta kara da kungiyar kwallon kafar Burkina Faso.
Wadannan wasanni na gudana ne a wani lokaci da hukumomin kwallon kafar Afrika ke fatan jama’a za su yi aiki da matakan kare kai daga kamuwa da cutar Korona wadda ta addabi duniya kuma ta sa aka tsayar da wasanni daban-daban a duniya a sassa da dama.
Publicité