Yadda Ake Ittikafi Da Kuma Hukunce-Hukuncensa  

Ittikafi

Daga S.P Imam Ahmad Adam Kutubi,

Kafin mu zo kan batun Ittikafi, za mu karasa bayani a kan karya azumi da muka dauko yi a makon da ya gabata.

Idan mutum yasan cewa bayan kowane kwana uku ga misali zaiyi rashin lafiya, ko kuwa mace ta saba da haila ta zo mata ranar bakwai ga ko wanne wata, to, da ranakunnan sukazo sai suka ki daukar azumi suna jiran faruwar wadannan uzurai. Zasu yi ramuwa game da kaffara koda kuwa rashin lafiyan ko hailar sun auku. Yadda shari’a ta ce su yi shine su dauki azumin, a locin da dalilin karya shi ya zo, su ka gan shi zahiri sai su karya.

Makaruhi ne mutum ya dandani abinci dan ya ji ko maggi ko gishiri ya yi sosai a cikin abinci ko miya. Idan ya yi sauri ya tufar azumi bai baci ba. Idan kuwa ya hadiye azumi ya baci zaiyi ramuwa da kaffara. Haka kuma makaruhi ne mutum ya tattauna abinci acikin baki saboda kananan yara, idan ya zubar da tukan ko kufan gishirinnan ko na abincinnan azumi bai baci ba. Idan kuwa ya hadiye shi da mantuwa ko bisa ga rinjaye zai rama daya, idan kuwa da ganganne zaiyi ramuwa game da kaffara. Haka kuma wanda ya lika magani acikin kogon hakorinsa idan bai hadiye maganin ba azumi bai karye  ba.

Idan mutum mai janaba ko mace mai haila da daddare basu samu damar yin wanka ba sai da rana, azumi yana nan. Haka kuma idan mutum ya aikata sabon Allah da daddare, komai girman zunubinnan, wajibi ne washegari ya tashi da azumi, domin zunubin sabo daban ladar yin azumi kuma da ban.

Sunnah ne mutum ya kame bakinsa daga dukkanin maganganun alfasha a cikin watan ramadana kuma anaso ya yawaita ibada ga ubangiji Allah. Kamar yin sallar asham da karatun alkur’ani da zikiri da tasbihi da zuwa wajen tafsiri.

Dukkan azumin da mutum ya karya da mantuwa ko bisa ga rinjaye, to, ba zai kara cin komai da gangan ba har rana ta fadi don alfarmar watan ramadan, ko da yake zai rama azumin nan. Idan kuma ya sake cin wani abu da gangan, bayan wannan na mantuwa to zaiyi ramuwa game da kaffara.

Sunnah ne mai azumi ya gaggauta yin bude baki bayan ya tabbata lalle rana ta fadi. Anso yayi bude baki tun gabanin yin sallar magariba. Kuma sunnah ne ga mai yin azumi ya jinkirta sahur gwargwadon lokacin da zai isa ya karanci ayar Alkur’ani hamsin bayan kare yin sahur kafin alfijir ya fito.

Sunnah ne ga mutum wanda ba mai hajji ba yayi azumi ranar tara ga zulhajji, haka kuma mustahabbi ne mutum yayi azumi cikin kwana tara na farko ga watan zulhajji. Sunnah ne kuma yayi azumi a rana na tara da ran goma ga muharram, da sauran kwanakin muharram, da watan rajab dana sha’aban, da kwana uku a cikin kowane wata, da kwana shida a cikin shawwal. Ana kiran wadannan da azumin Tadawwu’i, wato na sa kai.

Sunnah ne mutum ya gaggauta ramuwar azumin ramadana daya sha. Amma Ya hallata agareshi ya jinkirta ramuwa amma kuma dole zai rama kafin wani azumin watan ramadana yazo. Idan kuma jinkirinsa yayi muni har ya tsallake ramadana na gaba to zaiyi sadaka da mudu daya a kowane maraice da ya rama dayan azuminsa.

 

  Ittikafi

Ittikafi shine musulmi ya zauna a cikin masallaci domin yin zikiri da tasbihi da sallah da karatun Alkur’ani, yana mai yin azumi, mai kamewa daga yin jima’i da magabatan jima’i,  har kwana daya ko abinda yafi haka da niyyar yin ittikafi

Hukuncin ittikafi sunnah ne mai lada da yawa, wajibi ne ittikafi yazamo a cikin masallaci, mai yinsa kuma ya zamo yana mai yin azumi ko da farilla ko na tadawwi’i, kuma da sharadin kwanakin yinsa su jeru ba a yanke ba. A kallan kwanakin ittikafi kwana daya, mafi yawansa kuma kwana goma, a wani kauli kuwa ance a kallansa kwana goma mafi yawansa wata daya.

Idan mutum zai fara kwanakin ittikafi da ya dauki alkawarin yi, zai shiga masallaci gabannin faduwar rana. Idan kuma ya kare zai bar masallaci zuwa gida bayan magariba. Wajibi ne mutum ya cika adadin kwanakin da ya dauki alkawarin yi. Bai halatta ya ragesu ba ta kowanne hali.

Mai ittikafi ba bazai fita wajen masallaci ba sai domin larurar dan Adam. Kamar tafiya cin abinci, da zuwa fitsari ko bayan gida ko wanka ko alwala. Kuma idan ya fita domin dayan wadannan abubuwa ba zai shige wuri mafi kusa da inda zai iya biyan bukatarsa ba. Idan yaje wuri mafi nisa ittikafi ya baci, sai ya faro tun daga farko. Amma idan rashin lafiya yakama mutum , ko kuma jinin haila ko na biki yazo wa mace, lokacin da suke yin ittikafi, to, zasu fita su koma gida domin dayan wadannan uzurori. Amma da gushewar uzurinsu sai su dawo masallaci maza-maza su cigaba da  ittikafinsu. Wato zasuyi lissafi da kwanakin baya.

Kuma a lokacin zamansu a gida da uzuri, duk suna cikin hakkin ittikafi na barin yin jima’i da makamantansu.

Idan mai ittikafi ya ci abinci da rana da gangan ko yayi jima’i da rana ko da daddare da gangan ko da mantuwa ittikafi ya baci, sai ya faro shi tun daga farko.

Mai ittikafi ba zai fita masallaci don gaida marasa lafiya ba, sai idan dayan iyayensa ne. Kuma ba zai fita don sallah a kan mamaci ba, ko don yin ciniki ba.

Idan karshen kwanakin ittikafin mutum ya dace da daren sallah, to, anaso ya dakata har zuwa washegari, daga nan masallaci ya zarce zuwa masallacin idi, sannan daga nan ya taho gida.

Zakatul Fidr

Zakatul fidr wato zakkar fidda kai sunnah ce mai karfi tana wajaba akan kowanne musulmi babba da yaro mace dana miji da ko bawa da sharadin akalla sa’i guda ya ragu daga cikin abincin da mutum ya mallaka a ranar data wajaba akansa. Yawanta sa’i guda ne akan kowanne mutum (Sa’i kuwa shine mudun nabiyi hudu ga kowanne mutum) lokacin take wajaba akan wanne mutum shine da faduwar rana, a yinin karshe na ramadan. A wani kauli kuwa ance bata wajaba sai wace garin sallah. Amma dai akowanne hali sunnah ne ayi saurin fitar da ita da fitowar alfijir na ranar sallah. Ana bada ita ga musulmi fakiri ko miskini, kuma ba’a bayar da ita ga bawa ko kafiri, da mawadacin mutum. Mutum shi zai fitar da zakkar nan ga wanda ciyar da shi tawajaba akansa da sababin zumunta ko aure ko bauta. Idan tawajaba akan mutum amma yayi jinkirin fitar da ita to bata faduwa akansa, saboda haka zai fitar da ita ko bayan watanni masu yawa. Baya halatta a fitar da ita sai daga daya daga cikin nau’in abincinnan;

 1. Alkama
 2. Sha’ir
 3. Sultu
 4. Dabino
 5. Zabib
 6. Cuku
 7. Gero
 8. Dawa
 9. Shinkafa
 10. Alasu
 11. Masara ko garin masara
 12. Wake
 13. Maiwa.

Amma idan an rasa daya daga cikin wadannan ya halatta a fitar da ita daga irin abincin da mutanen wajen suke ci.

 

Exit mobile version