Mohammed Bala Garba" />

Yadda Ake Jefa Rayuwar Ma’aikatan Zabe Na Wucingadi Cikin Hatsari A Borno

Lokoja

Aikin zabe aiki ne da dubun-dubatar daliban ilimi maza da mata da ke gudanarwa a lokacin zabe a Najeriya. Aikin ba a iya dalibai kawai ya tsaya ba, saboda ma’aikatan gwamnati ma kan shiga a dama da su.
Hatta matan aure da ke gidanjen mazajensu su na fita gudanar da aikin, don su samu abin batarwa. Wasu daga cikin matan auran sha’anin yau da gobe ne ke sa su fita domin gudanar da aikin, yayin da wasu kuma rashin kishi na mazajensu ne da rashin godiyar Ubangiji ke sanya su.
Wasu kan bar gidajen iyayyensu domin zuwa duk inda a ka tura su gudanar da aikin.
Duk da cewa wasu daga cikin ma’aikatan kan dogara ne da ladan da hukumar zabe ta tanadar mu su, amma kaso mafi yawa daga cikin ma’aikatan sun fi karkata ne da sa ran abinda za su samu a hannun ’yan siyasar kasar. Kalilan ne ke gudanar da aikin a matsayin bauta wa kasa.
Jihar Borno ita ce jihar da ’yan kungiyar Boko Haram su ka fi kai hare-harensu, domin nan ne tushen kugiyar kuma cibiyarta. Wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI ya kewaya, domin ganin yadda rayuwar wadannan ma’aikatan zabe na wucingadi ke kasancewa a lokacin zaben nan na 2019.
Wakilin namu ya fahimci cewa, duk da wadannan hare-haren da a ke fama da su a jihar, amma wannan bai hana maza da mata zuwa kananan hukumomin cikinta domin gudanar da aikin zabe ba.
Duk da wannan sadaukarwar da jarumtar da wadannan ma’aikatan su ka nuna, amma wannan bai sa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta jihar Borno sama mu su motoci masu inganci da ba su tsaro a hanyarsu ta zuwa kananan hukumomin ba, inda ta kawo mota kirar Fikok ta ke zuba su a bayanta ba tare da jami’an tsaro ba, su nufi kananan hukumomin jihar domin gudanar da aikin zaben.
Ya kamata hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa da ta jihar su san cewa wadannan ma’aikatan nata dai dalibai ne, wasu sun kammala jami’a, yayin da sauran kuma dalibai ne daga jami’ar Maiduguri (UNIMAID) da sauran manyan makarantun jihar irin su Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Ramat (Ramat Polytechnic) da College of Agriculture da Sir Kashim College of Education da College of Health Technology da College of Nursing Midwife da kuma Mohammed Goni College of Islamic and Legal Studies da dai sauransu.
Wadannan matasan, samari da ’yan mata, su ne magina kasar, domin kuwa duk wata kasa da ta cigaba a wannan duniya idan a ka dubi sirrin da ke tattare da samuwar wannan cigaba, za a ka ga a hannun matasansu ya ke.
Saboda haka bai kamata su yin sakaci a fannin kulawa da rayuwar matasan ba. Kamata ya yi hukumar zabe ta kasa ta tanadar da motoci masu nagarta wadanda za su dauki ma’aikatanta izuwa kananan hukumomin kasar domin zuwa gudanar da ayyukan zabe tare da hada su da jami’an tsaron da za su ba su kariya ta musamman a hanyoyi, musamman wadanda su ke jihohin Adamawa da Borno da Yobe da kuma Zamfara da ke fama da tsananin matsalar tsaro.
Amma abin takaici da rashin sanin muhimanci dan adam shi ne yadda hukumar zaben jihar Borno ta dauki wadannan ma’aikatan nata a bayan Fikok ba tare da jami’an tsaro ba izuwa kananan hukumomin jihar.
Siyasa na da mahimmanci a kowacce kasa ta duniya da ke bin tafarkin dimukradiyya. Dalili kuwa shi ne siyasar tsarin dimukradiyya na bai wa jama’a damar zaben wadanda su ke ganin sun dace da su, za su biya mu su bukatunsu da kuma share mu su hawaye.
Wannan ya sa iyaye ke barin ’ya’yansu musamman ’ya’ya mata domin zuwa duk inda a ka tura su domin zuwa gudanar da aikin zaben.
Ko a ranar Juma’a 15 ga Fabrairu, 2019 a birnin Maiduguri dab da lokacin da a ka yi niyyar gudanar da babban zaben kasar a makon jiya kafin a dage shi an debi wasu ma’aikatan a bayan irin waccan mota daga bakin ofishin NULGE da ke kan titin Pompomari izuwa karamar hukumar Monguno, kowacce mota ta dauki kusan kimanin maza da mata 25 a bayanta ba tare da jami’an tsaro ba.
Wannan ya sa su ka ci bakar wahala a hanyarsu ta zuwa karamar hukumar, saboda takurar da su ka yi a bayan motar, ga rashin kyan titin, ga fargaba, ga rana da yunwa da kishirwa, ga binciken da su ka sha a hannun jami’an tsaro a kan hanyarsu, saboda rashin shaida daga hukumar zabe da za ta nuna cewa su ma’aikatan zabenta ne na wucingadi.
Da farko dai ya na da kyau hukumar zaben jihar Borno ta san cewa hanyar karamar hukumar Monguno ta na daya daga cikin hanyoyin da kungiyar Boko Haram ta ke bayyana. Shin yanzu idan wani abu ya faru da wadannan ma’aikatanta a hanya, me hukumar zabe za ta fada wa iyayensu?
Shin ta san wane irin koma-baya za ta kawo wa jihar Borno da kasar Najeriya a dalilin sakacin da ta yi a kan wadannan ma’aikatan? Me ta tanadar wa iyayensu da al’ummarsu?
A nan za a iya cewa, ya wajaba a yi kira da babban murya ga hukumar zabe ta kasa da ta binciki hukumar zabe ta jihar Borno a kan yadda ta gudanar da sufurin daukar ma’aikantan izuwa kananan hukumomin jihar, domin INEC ta tanadarwa kowacce jiha kudi isasshe wanda zai ishe ta gudanar da komai na zabe cikin kwanciyar hankali, sai dai watakila wasu masu manyan aljihai ciki sun rufa a kan kudaden su yi ruf-da-ciki da su.
Za a gudanar da wani zaben a mako biyu masu zuwa na gwamna da ’yan majalisa a jihar ta Borno. Don haka akwai bukatar a yi kira ga shugaban hukumar zabe ta jihar Borno da ya dubi Allah a kan wanna al’amarin, domin bai kamata ma’aikata su bada rayuwarsu domin ganin an gudanar da zabuka a cikin kananan hukumomin cikin lumana, amma kuma a rika gangaci da rayukansu ba.
Kamar yadda ba za ka yadda a debi iyalanka a bayan Fikok ko da a cikin garin ne a kai su unguwa ba, haka bai kamata a debi wadannan ma’aikatan ba, balle kuma a ce wata karamar hukuma za a kai su, musamman kananan hukumomin jihar Borno masu cike da matsala ta fargabar tsaro. Idan kuwa matsala ba a wajenka ta ke ba, to ka yi bincike a kan yadda a ka gudanar da lamarin.
Bayan haka, akasarin wadannan ma’aikantan da su ka baro gidajen iyayensu izuwa kananan hukumomin jihar bayan dage zabe da a ka yi wasu sun samu Naira 4,500 a matsayi alawus, wasu kam yadda su ka je, haka su ka dawo ba tare da an ba su ko sisi ba.
Ya zama dole ta sama mu su abubuwan hawa masu inganci tare da ba su jami’an tsaron da za su ba su kariya a hanya da kuma rage mu su matsalar bincike da bata lokaci da jami’an sojoji ke yi a shingayen bincike. Idan kuwa ta ki, to za ta iya rasa ma’aikatan da za su gudanar ma ta da ayyukan zabe a ranar Asabar ta sama!
Mohammed Bala Garba (Alh Bawayo), wanda marubuci ne mai zaman kansa, ya aiko ma na da wannan rahoton ne daga Maiduguri.

Exit mobile version