Yadda Ake Kula Da Marayu A Gidan Marayu Na Anwarul Faidah Da Ke Jos

Marayu

Daga Mohammed Ahmed Baba,

Sheikh harisu salihu wanda ake kira da kakakin faidah, shine mai gidan marayu daya tilo wanda bana gwamnati ba, ya bayyanna cewa, Allah ya bashi ikon gina wannan gida ne don tallafawa al’umma.

 

Ya ce, akwai marayu guda arba’in wanda ishirin daga cikin daga Jos suke, guda goma kuma daga Maiduguri, guda goma daga adamawa, akwai maza ishirin mata ishirin, sannan gurin zaman maza a kasa gurin zaman Mata a sama, sannan akan dafa musu abinci kullum inda buhu ke karewa a kwana uku.

 

Sannan akwai ruwan sha da suke amfani dashi, akwai kuma ruwan famfo da suke wanka da wanki dashi, akan yi masu a wanki sau uku a sati amma manyan da kansu sukeyi, akwai ma aikata kusan goma sha daya a gidan, inda mata biyar ne suke Lura da bangaren abinci.

 

A ofis akwai mutane hudu sannan masu gadi mutum biyu, sannan ya ce, sama da shekara biyu da watanni bai taba fashin biyan aikata ba ko da an yi jinkiri sannan sukan sami kyautar abubuwan sha kamar juice da biskit, daga sauran jama’a wadannan basu cika saya ba.

 

Sannan idan wasu abubuwan sun kare kafin suje saya sukan karba, kuma yaran akan yimusu dinki sau uku a shekara, kamar karamar sallah da babbar sallah da kuma maulidi, sannan akan samu mutane da suke koyawa yaran dinki.

 

Amma idan an samu yaduddukan daban-daban akan canja a sami iri daya, a kasuwa don dinka musu iri daya.

 

Ya kara da cewa, a bangaren mata kamar kayan kwalliyar su basu cika siya ba, akwai mata da suke yawan kawo musu irin wadannan kayan, inda takalma kuma akan sayo masu.

 

A bangaren zaman takewar yaran, ya ce, suna son juna ba a yawan samun fada a tsakanin su, sannan suna karatun islamiyya dana boko, sannan suna kokari gurin yawan ibada, bayan sunyi sallar azahar sukan yi addu’a na tsahon awa daya,

don yiwa kasa addu’a akan abinda ke faruwa.

 

Allah ya dauke musamman wadanda suka fito daga yankin Maiduguri da adamawa, wanda suka ga abinda yake faruwa sannan su yiwa iyayensu addu’a da wadanda suke tallafa masu, sannan ta hanyar da suke bi gurin neman marayu kuma malamin ya ce, sunbi ta hanyar.

 

Farfesa Ibrahim makari ne shine aka samu ta hannun malamin sa sharif Ibrahim sale, da ke Maiduguri, ya ce sunbi ta hanyoyi har ta gurin gwamnati amma basu samu yadda suke so ba, sannan akwai wadanda suke kawo ‘ya’yan su da kansu sannan ya ce, sukan bi matakai.

 

Tun daga karamar hukuma jiha zuwa tarayya,

sannan duk yaron da aka karba, akan rubuta

bayanai daga inda aka karbe shi sannan duk wata akan tura rahoto gurin ‘yan sanda bayan haka, ya kuma bayyana yadda masu karbar haraji suka taba zuwa akan a dinga biyawa gidan haraji.

 

Ya ce, sun gaya musu cewa gwamnati bata taba tallafa musu ba,sai suka ce ai dokar kasa ce shine suka dakko musu bayanan banki, da suke ajiya suka ga ba wani kudi da yake shigo musu a susu, ya ce, tunda suke sau daya gwamnatin jiha ta basu shinkafa.

 

Buhu biyar sai karamar hukuma buhu biyu a lokacin korona, daga nan babu wani kudi ko abinci na wata-wata da gwamnati ta ke basu, sai dai daidaikun mutane da suke kawo tallafin su kuma duk wanda ya kawo ana rubuta sunan shi ana bashi risit, a rubuta bayanai saboda nan gaba.

 

Abinda ya shafi tsahon lokacin da yaran suke dauka a gidan, ya ce, idan yaro ya kai shekaru goma sha takwas sai a maida shi, in kuma yayi kusan hakan aka kawo shi zai yi shekaru biyar ne, akwai kuma yanzu haka akwai gini da akeyi a saman gidan inda za a rinka koya musu sana’a.

 

Kamar dinki da sarrafa na’ura mai kwakwalwa wato (computer), akwai kuma masu kaisu su makaranta su dawo dasu, a bangaren kiwon lafiya ma akwai asibiti mallakinshi da ake Kira (anwarul faidah hospital) da ake duba lafiyar su, ya kara da cewa, yana samun karfin gwiwa.

 

Da addu’o’i daga jama’a da yabon da yake samu ganin shi kadai ya ke irin wannan aiki a garin jos, bai sa ya taba jin wani abu a ransa ba, ya ce, duk abinda yake nema a gurin Allah ya ke bukatar, a bangaren yaran akwai wani yaro mai suna Jidda sale abubakar daga Maiduguri.

 

Ya ce, farko yana karatu ne a gidan sharif Ibrahim sale shine ya fada masu cewa za a kawo su gidan marayu a jos, sannan suna samun abinci da kulawa ya ce mahaifinsa ya rasu, mahaifiyarsa kuma bai san inda take ba sai daga baya ya samu lambar yayarsa.

 

Sannan ya ce, an sami mahaifiyarsu akwai wata yarinya mai suna nusaiba haladu daga adamawa, ta ce, takai kusan shekaru biyu a gidan kuma ta yaba da yadda suke samun Kula, akwai kuma yara biyu daga Jos wadanda suma sunyi jawabi abdurrahman Auwal da rahina inuwa.

 

Daga layin majema cikin garin Jos duk sun yaba da kulawar da suke samu, na ilmi da abinda za su ci da sutura sannan, sun ce ‘yan uwan su sukan zosu duba su tunda su a gari suke, daga karshe suma sun nuna farin cikinsu ga sheikh harisu salihu daya dauki nauyin mai addu’a

Exit mobile version