Abubakar Abba" />

Yadda Ake Magance Amosanin Kai

Daga Abubakar Abba

Amosanin kai wani yana yi ne da mutun zaiga kansa ya yi kamar farin gari wanda har yake zuba lokacin da ake taje kai kuma yana shafar jikin fatar mutum wani lokaci harda yin soshe-soshe.

Ba a san takamai-man abinda yake janyo shi ba, amma kawai abubuwa da dama da suka kara shi.

Ba wai rashin tsafta ke janyo shi ba, amma amfi ganin sa idan mutum baya wanke kansa ko taje kansa lokaci-lokaci.

Maganar Zahiri Akan Amosanin Kai:

Amosani wani yanayi da aka sani har kunya zai iya jefa mutum kuma yana da wahalar warkarwa kuma taje suma yana taimakawa.

Wasu daga cikin hadarin sa sune, yana shafar fatar jikin mutum ko kuma shafar kiwon lafiyar sa da kuma yin amfani da man gashi wanda ba a amince dashi ba.

Akwai hanyoyi da dama da ake magance shi, amma idan ya yi tsanani ya kamata a tuntubi likita.

Magance shi ya fi don kada ya shafi kwayoyin halittar jikin dan adam.

Yadda ake magance shi ya danganta da shekarun mai fama dashi da kuma yadda yanayin sa yake.

Sai dai, akwai wasu hanyoyin da ake magance a gargajiyance wadanda suka hada da, magance jin gajiya domin jin gajiya yana haifar da karuwar amosanin kai ga wasu mutane a saboda haka, magance shi yana taimakawa wajen wajen rage alamomin sa.

Gyara Gashi:

Yin amfani da man gyra gashi da wanke kai kullum yana taimakawa.

Tea tree oil:

Sai dai, akawai shedu ‘yan kadan domin wasu mutanen sun yi amana cewar, yin amfani da man tea tree oil don rage alamomin na amosani.

Ya kan sanya wa wasu masu fama dashi kyama.

Magance shi:

Yin amfani da man wanke suma da kuma ziyartar shagunan sayar da magunguna.

Yin hakan zai iya rage shi amma ba za su warkar dashi ba.

Yin amfani da man wanke suma:

Kafin yin amfani da man wanke suma don yakar amosani ya kamata a kiyaye wajen wajen fitar dashi yadda man zaifi yin aiki yadda ya kamata.

Sanadarin da dake yakar amosani yan dauke da a kalla sanadarin Ketoconazole wanda yana da karfi sosai wajen yakar amosani.

Man suma shi ma ya dauke wannan sanadarin kuma za’a iya yin amfani dashi a ko wane yawan shekaru.

Sanadarin Selenium sulfide:

Shi ma yana taimakawa wajen rage amosani.

Sanadarin Zinc pyrithione:

Wannan yana rage yawan sanadarin(yeast).

Dawo da sumar ka yadda take ada.

Yin amfani (Coal tar):

Wannan ma yana taimakawa wajen yakar amosani.

Rina suma ko gyaran suma har zuwa tsawon zangi.

Yin amfani da sabulun Tar shi ma yana taimakawa wajen yakar amosani in an yi amfani dashi, ana son a sanya hula in za’a shiga Rana.

Sanadarin (Coal tar) yana da karfi sosai.

Sanadarin Salicylic acids:

Wannan yana baiwa kwayoyin halitta kariya kuma baya rage yadda ake sarra kwayoyin halitta na fatar jikin mutum.

Magance shi shine a wani lokaci akan bari sai idan kan mutum ya bushe don kada ya shafar da illa ga fatar jikin mutum.

Sanadarin Tea-tree oil:

Ya samo sunan sa ne daga kasar Australian da suke kira da yaren su (Melaleuca alternifolia),kuma mafi yawanci man wanke suma a yanzu yana kunshe da sanadarai.

An kuma jima ana amfani dashi wajen yakar amosanin suma.

Wasu mutanen suna kyamar sa, amma hanyar da tafi dacewa itace, a zabo man wanke gashi dake dauke da daya daga cikin wadannan sanadaran don a rika wanke kai a kullum don shawo kan amosanin.

Bayan wannan, ana iya amfani dasu ako da yaushe.

Ana yin amfani da man wanke gashi akoda yaushe don ya taimaka.

Sai dai, wani man wanke suma da daya da aka ware, yakan daka ta yin aiki bayan wani lokaci.

A saboda haka, yana da kyau a koma yin amfani da wani sanadarin.

Wasu man wanke sumar, ana barin su su kai kimanin mintuna biyar saboda wanke wa da wuri, yana sanya wa sanadaran basa yin wani aiki.

Yana da kayu a rika bin saharuddan da aka rubuta a jikin robar ta man.

Abin da Ke Janyo Shi: Ba a san takamai mai ko me yake janyo shi ba, amma wani nazari guda daya da aka yi,ana danganta amosani da sarra wasu kwayoyin halitta kamar yadda yake a zagaye da matsurar da gashin kai yake fitowa.

A nan zamu yi dubi akan hanyoyi goma da ake ganin sune suke janyo shi.

Seborrheic dermatitis:

Amosani ya shafi matsurar da gashi yake fita.

Wadanda suke da (seborrheic dermatitis) suna jin zafi kuma sune suka fi kamuwa da shi.

Masu irin wannan yana shafar bangarorin fatar jikin su harda bayan kunuwan su nonon su girar idon su da gafen hancin su.

Jikin mutum yana yin ja.

Seborrheic dermatitis kusa yake da sanadarin(Malassezia) wanda yawanci suke rayu a kai suna kuma ciyar da mai.

Bai cika kawo matsala ba, amma ga wasu mutanen yana wuce iyaka har a rika jin zafi don sarrafa sauran kwayoyin hallita.

Wannan karin na kwayin hallitar in sun mutu suka fado ana hada su da mai.

 

Exit mobile version