Yadda Ake Noman Kankana A Nijeriya

Daga Abubakar Abba,

Shuka Kankana da dibanta na kai wa kimanin watanni uku, kuma za ka iya shukata da dibanta sau hudu a shekara haka a fuloti daya, za ka iya shuka Kankana sama da guda 1,596.

A yanzu haka, kasar China ce ke kan gaba a fadin duniya wajen noman Kankana haka kuma sashi ne da ke samar da riba ga wanda ya rungume shi, inda a Nijeriya da naira 50,000 ban da kudin hayar gona, za ka iya fara noman Kankana.

Za ka iya samun ribar naira 400,000 daga Kankanar da ka noma a kan fuloti daya a shekara haka ta na kuma jurewa ko wanna irin yanayi da kuma bijere wa cututtukan da ke harbin amfanin gona.

Tsara Yin Kasuwancinta :

Idan har ba ka tsara yadda za ka yi kasuwancinta ba, tabbas za ka iya tabka asara mai yawan gaske, domin bisa rashin yin ingantaccen tsarin ne, ke sa manomanta yin asara.

Tsarin Kasuwancinta ya hada da, yin kaafin kudin da za ka kashe wajen nomanta, inda hakan zai taimaka wa manominta samun riba masu yawa.

Zabar Ingantaccen Irin Nomanta:

Wannan na daya daga abubuwa masu mahimmanci a fannin nomanta a Nijeriya, haka akwai Irin kala-kala ya danganta da wanda kake bukatar kashuka.

Zabo Wajen Shuka Irin :

Shi ma wannan na da mahimmancin gaske duk da cewa, Allah ya albarkanci jihohin kasar nan 36 har da babban birnin tarayyar Abuja, da kasar noma.

Sharar Gona :

Mataki na karhe shi ne, yin sharer gona domin shuka Irin na Kankana, inda wannnan matakin ya kunshi nome ciyawa da zuba takin gargajiya ko na zamani.

Tsarin Yadda Ake Shuka Irinta:

Wannan ya kunshi yadda ake shuka Irin na Kankana da kuma gyaran gonar da za a shuka Irin, ana son ka shuka Irin nesa da juna.

Yi Mata Ban Ruwa:

Yana da mahimmanci a tabbatar da an yi mata ban-ruwa yadda ya kamata akalla sau biyu a sati, musamman ganin cewa,ta na daya daga cikin amfanin gona da ke da bukatar a yi ma ta ban-ruwa lokacin da aka shukata.

Kare Ta Daga Harbin kwari Da Yi Ma Ta Noma:

A nan ka tabbar da kana nome ma ta ciyawa da kuma yi ma ta feshi don ba ya kariya daga kamuwa daga cututtukan da ke harbin amfanin gona.

Tsarin Yadda Ake dibanta:

A nan, bayan ‘ya’yan sun girma sun kai munzalin cirewa sai a cire su ganin cewa, tana kai wa daga kimanin kwana 75 zuwa kwana 90 take nuna.

Adana Ta Bayan diba:

Yana da kyau bayan ka debe ta, ka tanadi guri mai kyau da za ka adana ta kafin ka kai ta kasuwa don sayarwa ko kuma samo wanda zai saya, saboda haka za ka iya adana ta har zuwa tsawon wata daya, ba ta yi komai ba,amma kar ka bari rana na dukanta.

Sayarwa:

Za ka iya sayar da Kankanar da ka noma baki-daya kuma a lokaci daya,musamman ga manyan shaguna ko kasuwanni ko kamfanoni ko ga dai-daikun mutane ko kuma ga masu safararta zuwa waje da sauransu.

Exit mobile version