Yadda Ake Renon Irin Gwanda

Gwanda

Daga Abubakar Abba,

Duk da irin dimbin ribar da ake samu a fannin noman gwanda a Nijeriya, sai dai akasarin ‘yan kasar, sun yi watsi da damar da za su samu a fannin noman gwanda, sai dai, masana a fannin na ganin  hakan na faruwa ne saboda rashin wayar musu da kai dangane da amfanin da ke tattare da noman gwanda, musamman ganin cewa, fannin bai bukatar  sai ka tandi kudade masu yawa kafin ka shiga cikinsa ba.

Babbar hanyar kuma mataki na farko a noman gwanda shi ne, ka fara renin irin da za ka shuka na gwandar.

Ka Tabbatar Ka Sayo Ingantaccen Irin Da Za Ka Shuka:

Ka samu gurin da ya fi dace wa, ka yi gyaran gurin tare da kone sharar da ke gurin sai ka shuka Irin mita biyar tsakanin kowanne Iri haka, yana kai wa kimanin satuttuka kafin ya fara nuna ko kuma wuce haka.

Bayan watanni biyu da shuka sai a nome ciyawar da ke gurin ka da a kuma zubar da ciyawar, a bar ta ta rube a gurin yadda za ta zama takin gargajiya.

Bayan wata daya zuwa biyu, sai ka canza wa mata waje, inda kake ganin zai fi, inda kuma bayan watanni uku, sai ka sayo maganin feshi ka yi wa kasar feshi, inda hakan zai saka ta yi saurin girma.
Har ila yau, bayan watanni shida sai ka kara yin feshi, inda a cikin sati uku masu zuwa za ta kara yin kwau, haka ka bar ta zuwa wata uku ko fiye da haka don ta kara yin karfi.

Kasar Noman Da Ta Fi Dacewa :

Ka tabbatar da ka yi shukar a kasar noman da ta fi dace wa,  musammn domin ka samu amfanin mai yawa,  haka kuma ana son ka yi shukar a kasar noman da ke da lema.

Matakan Shuka Gwanda:

A wannan matakin, ana bukatar ka ciro ta daga wadanda suka fara fito wa daga cikin abin da ka shuka irin tun farko sai ka haka rami ka dasa ta.

Lokacin Da Ya Fi Dacewa A Dasa:

Babu takamaiman lokacin da aka kebe na dasaata, donin ako wanne lokaci na kakar noma za iya iya yin nomanta, har Ila yau, kuma tana jure wa ko wanne irin yanayi.

Kwanuka Nawa Take Yi Kafin Ta Fara ‘Ya’ya?

Ya danganta da ingantaccen irin da aka shuka da kuma yadda nau’in gwandar yake wasu, na kai wa tsawon shekaru hudu kafin su girma tun daga lokcin da aka dasa irin,  haka wasu na kai wa tsawon shekaru takwas kafin su girma.

Lokacin Girbinta:

Yayin da jikinta ya fara canza wa zuwa yalo sai dai, wasu nau’in gwandar, ba ya canza wa zuwa yalo idan sun nuna suna kuma kai wa watanni tara bayan an canza wa irin matsuguni daga inda aka dasa shi.
Bishiya daya ta gwanda, za a iya samar da kimanin gwanda daga  75 zuwa 100 a shekara haka, tana iya kai wa tsawon shekaru dari ana cire ‘ya’yanta, amma an fi fara samun amfaninta daga shekaru uku zuwa shekaru hudu

Kasuwancinta:

A yayin da kake jiran ta kammala kai wa a girmanta, sai ka fara tuntubar masu bukatar saye ko kuma kasuwar da za ka kai, don sayar wa, haka za ka iya tuntubar kamfanoni, musamman wadanda ke sarrfa ta zuwa wasu nau’uakn yin kayan sha ko kayan lemon Kwalba,sarrafa magunguna da sauransu.

Exit mobile version