Yadda Ake Sana’ar POS
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ake Sana’ar POS

byMaryam Ibrahim
3 years ago
POS

Assalamu alaikum. Masu karatu barkanmu da sake haduwa a wannan makon, makon  za mu duba yadda ake yin sana’ar PoS. Ita dai sana’ar ta PoS sana’a ce da ake samun kudi sosai kuma take da saukin shiga, ta wannan sana’a za ka iya samun 200,000 har zuwa 400,000 har ma fiye da haka a wata, gwargwadon jarinka da kuma wajen da kake gudanar da sana’ar.

Sana’ar PoS dai wata hanya ce da ke saukakawa jama’a mu’amala da kudi a madadin bankuna-wato ana tura kudi, ko a karbar, ko a bude sabon asusun ajiya na banki,har ma da yin lambar BVN a wasu wuraren. Yayin da mai PoS ke yi wa jama’a wannan hidima, shi kuma yana samun kamasho daga gare su.

  • Kofin Duniya: Iran Ta Lallasa Wales Da Ci 2
  • ‘Yan Nijeriya Na Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Sabbin Takardun Kudin Da Aka Kaddamar

Babban bankin Nijeriya wato CBN ne ya lamunce wa bankuna da wasu kamfanoni masu zaman kansu su gudanar da wannan sana’a ta hanyar samar da wakilai wadanda za su yi mu’amala da mutane a madadinsu.

Hanyar shiga wannan sana’ar PoS abu ne mai sauki matuka, akwai hanyoyi uku da ake shiga wannan sana’a, ta farko ita ce hanyar bankuna, mafi yawancin bankunan da ke tarayyar kasar nan na daukar dillalai su wakilce su.

hanya ta biyu ita ce, kamfanoni masu daman kansu da babban bankin Nijeriya ke ba su lasisin gudanar da sana’ar a madadin su.misalin wannan kamfanoni sun hada da PAGA, OPAY, da sauran su, kuma suna da yawan gaske a wannan kasa.

Hanya ta uku ita ce,idan kana da kudi za ka iya sayen PoS da kudinka sai ka je bankin da kake bukata su hada ma ka shi da asusun ajiyarka.

yadda za ka zama dillali a bankin da kake bukata ko kake sha’awa,abu ne mai sauki kawai ka shiga kowanne reshen bankin mafi kusa da kai,ka bayyana musu sha’awarka ta zama dillali na su.bankunan sun ware shashen dake kula da wannan bangaren, don haka za su hada ka da jami’in da zai ma ka cikakken bayani.

Abin da za su bukata a wajenka shi ne, ka bude asusun ajiya a wajensu da wani adadin kudi, bayan ka gama za su bukaci ka yi downloading din application din bankin da su ke gudanar da sana’ar, wanda da shi ne za ka fara kafin su ba ka naurar PoS.

Wasu bankunan za su ba ka wa’adi target wato yawan kudin da za ka yi hada-hadarsu a kowanne wata kafin su ba ka naurar PoS, amma wasu bankunan ba ruwansu da hakan.

Wannan PoS da za su ba ka, kyauta ne wato ba za su bukaci wani kudi daga gare ka ba, sai dai matukar ba ka aiki da shi za su kwace kayansu, don kuwa kudi mai yawa su ka sanya su ka saya, sannan ka san yawan aikin da ka yi da shi yawan ribar da za ka samu haka nan bankin, kudin da za ka yi mu’amala da shi ba kudin da za ka yi mu’amala da shi ba na banki bane, kai ne za ka samu kudinka a matsayin jarinka.

Idan ka na da bukatar zama fillali ka yi da OPAY don ya fi sauki. Za ka yi downloading Opay application, wanda aka rubuta opay agent app don opay din guda biyu ne za su tambaye ka tambayoyi kamar suna, adreshinka, email, NIN dinka da sauran su.

Bayan ka yi rajista sai ka sa ka kudi a cikin wallet dinka na Opay daga nan komai ya zama daidaita za ka iya sayar da Data, katin waya, da kuma rajistar NECO da WAEC da sauransu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC
Sana'a Sa'a

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

August 3, 2025
Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera
Sana'a Sa'a

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

February 1, 2025
Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi
Labarai

Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi

November 22, 2024
Next Post
Yadda ‘Hackers’ Ke Amfani Da Smishing Wajen Yin Kutse

Yadda 'Hackers' Ke Amfani Da Smishing Wajen Yin Kutse

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version