Yadda Ake Sauke Video Daga Facebook Da YouTube

Video

Daga Ibrahim Sabo,

A wannan makon za mu dan yi bayani a kan yadda ake sauke Video daga Facebook da kuma yadda ake sauke video din daga YouTube. Sannan za mu bayani a kan yadda za ka dauki audio na sama da awa daya kuma ka tura shi a WhatsApp.

YADDA ZA KA SAUKE VIDEO A WAYARKA DAGA FACEBOOK

Idan kana so ka sauke video daga Facebook a wayarka, to ka tabbatar a wayar ta ka akwai manhajar Xender. Idan ka ga video din da kake so ka sauke daga Facebook, to akwai hanyoyi guda biyu da ake bi. Hanyar farko shi ne, idan ka ga video din da kake so ka sauke din, sai ka duba saman video din, ta santar sunan wanda ya dora video din, za ka ga wasu digo guda uku, kamar haka …

To sai ka taba wadannan digo guda ukun (option kenan). Idan ka taba, zai nuno maka wasu rubututtuka a jere, sai ka duba za ka ga ‘Copy Link’ sai ka taba shi. Idan ka taba shi, ka yi kwafi din video din kenan, sai ka tafi inda za ka sauke shi, wato xender kenan. Sai ka je ka bude xender dinka. Idan ka bude xender din, a kasa za ka ga rubututtuka, to za ka ga social, sai ka taba shi. Idan ka taba shi, zai nuno maka wasu rubutu a sama kamar haka Status, Facebook, Instagram, Tiktok. To sai ka taba Facebook din. Wani xender din kuma zai nuno maka ‘paste and download’ sai ka taba shi kawai, za ka ga video din ya fara sauka.

Idan ka taba Facebook din, zai nuno maka wani waje an rubuta ‘paste Facebook link here’ wato ka ajiye link din da ka yi kwafi a nan. Sai ka danne yatsanka na dan wasu sakanni a wajen da aka rubuta ‘Paste Facebook Link here’ Za ka ga ya nuno ‘Paste’ sai ka taba wannan paste din. Kana taba wannan paste din, to wannan kwafi din da ka yi na video din zai sauka a wajen. To a kasan wannan waje, za ka ga wani koren rubutu, an rubuta paste & download. Sai ka taba shi, to za ka ga video din ya sauka. Sai ka dan jira kadan, za ka ga ya sauka.

Wannan yadda ake sauke video ta Xender kenan.

Hanya ta biyu kuma da ake bi wajen sauke video daga Facebook shi ne, ta hanyar Facebook Video downloader. Za ka je play store ka nemi manhajar ‘Fb video downloder’ zai nuno maka su da yawa, sai ka zabi daya daga cikinsu. Sai ka sauke shi a kan wayarka. Idan ka sauke shi, sai ka bude shi, zai nuno ka saka Email ko lambar waya da password din da ka bude Facebook dinka dashi. Idan ka saka, za ka ga Facebook dinka ya hau. To shi a cikin wannan Facebook video downloader din, duk video din da ka gani kana so ka sauke, to a tsakiyar video din za ga alamar play, sai ka taba shi, zai nuno maka abubuwa guda uku, kamar haka; Cancel, Watch, Download. To kana taba download zai fara sauka a wayarka. Idan ka dan jira kadan zai sauka a wayarka duka.

YADDA AKE SAUKE VIDEO DAGA YOUTUBE

Da yawan mutane suna koka wa a kan ba sa iya sauke video a kan wayarsu daga manhajar YouTube. To idan kana so ka sauke video daga YouTube, sai ka je play store ka sauke manhajar Bidmate a kan wayarka. Idan ka sauke shi, sai ka bude shi, to zai nuno maka WhatsApp, Facebook, YouTube da sauransu. Sai ka taba kan YouTube din, zai bude, zai nuno maka wasu videos din.

To a sama akwai wajen nema (searching), sai ka rubuta sunan video din da kake nema din. Idan ka taba wajen nema din, to zai nuno maka video din da kake nema. Idan ya nuno maka, sai ka taba kansa, ta ke zai fara magana. To a kasa, za ka ga wani arrow ja. Idan kana so ka sauke video din a kan wayarka sai ka taba wannan video din. Kana taba shi, take zai fara sauka a kan wayarka. Cikin sakanni, zai sauka a kan wayarka.

YADDA ZA KA DAUKI AUDIO NA SAMA DA AWA DAYA KA TURA SHI A WHATSAPP

Sau da yawa wasu suna koka wa, musamman ‘yan Media masu yin recording a wajen tarurruka, a kan  yadda idan sun dauki jawabi (recording) yana yin nauyi (MB din) ba zai yi yu a tura shi a WhatsApp ba. To hanya mafi sauki shi ne, ka shiga ‘play store’ ka sauke manhajar ‘Easy Voice Recorder’ idan ka sauke shi a kan wayarka, to duk lokacin da za ka dauki murya (audio) to da wannan ‘easy voice recorder’ din za ka yi amfani. Bayan ka sauke shi a kan wayarka, sai ka bude shi. Idan ka bude shi, zai nuno maka RECORD da LISTEN a can sama.

Idan ka taba Record, zai nuno maka alamar recording a can kasa, idan za ka fara daukan murya, shi za ka taba. Idan ka gama daukar murya din, akwai alamar good a can kasa a gefen dama, sai ka taba shi, zai maka sabing ya ajiye maka shi. Sai ka taba LISTEN, to a nan za ka ganshi. Kuma daga nan ne za ka tura shi zuwa WhatsApp din. Idan ka taba kan audio din da ka yi recording din, zai fara playing. Sai ka tsayar da shi ‘paused’. A nan din, saman recording din, za ka ga alamar tura shi wani wuri (share). Sai ka taba shi, zai nuno maka su Bluetooth, Xender, WhatsApp da sauransu. To sai ka taba WhatsApp din.

A nan a lura da kyau. Idan ka taba kan WhatsApp din, zai nuno maka ‘compressing for share’, a kasa kuma zai nuno maka cancel da kuma skip compression. To kar ka taba komai ka jira ya gama compressing din nan. Yana gama compressing zai nuno maka groups dinka na WhatsApp, sai ka zabi group din da kake so ka tura shi. Kana taba kan group din shikenan zai sauka a group din. Wannan compressing din da yake yi, a nan yake rage yawan MB din.

 

Exit mobile version