Yadda Ake Yin Cuwa-cuwar Yin Katin Zama Dan Kasa A Kano

Katin Zama Dan Kasa

Tun bayan da hukumar sadarwa ta kasa ta tsiro da tsarin hade rijistar dan kasa da kuma layin riistar kanfanonin wayoyin hannu a kokarin matsalar barazanar tsaro.da ake fama da shi a sassan kasarnan, ta bada wa’adin duk wanda baiyi riistar ba za a rufe masa layin wayarsa.

Hakan ta sa jama’a da mafi yawansu ba su yi katin dan kasar ba baza ma cibiyoyin da da ake gudanar da katin domin su yi domin tsira daga toshe musu layukansu.

Sai dai hakan tasa wuraren da ake gudanar da yin katin dan kasar a nan jihar Kano yake yin cikar kwari da jama’a domin su samu ayi musu rijistar.

Hakan kansa wasu su share dinbin awanni, har wuni ake a dogon layi da ake soma kafawa tun da sanyin safiya.

Sai dai wannan tsari na lallai kowa sai ya hade layin wayarsa da lambar katin dan kasa da tasa mutane zuwa domin yin.katin dan kasarnan ya bude kofar yin cuwa-cuwar yin katin dan kasa duk kuwa da sanarwar da hukumar katin ta bayar na cewa yin katin dan kasar kyauta ne.

Sai dai bincike da muka gudanar da ya nuna mana akwai wasu daga ma’aikatan hukumar yin katin da suke amfani da wasu wakilai suna karbar kudade daga mutane da suka zaku ayi musu katin ko koma wadanda ba za su iya zuwa bin layin jira ayi musu ba, sukan karbi kudi a kajensu daga N2,000 zuwa uku zuwa hudu domin kawo musu takardar rijistar katin dan kasar.

Wani da ya nemi mu sakaya sunansa ya tabbatar da cewa shima irin wannan tsarin aka tallata kuma ya biya aka dauki bayanansa aka kawo masa takardar shaidar rijistar mai inganci.

Wasu na danganta irin wannan cuwa-cuwa da a ke a yawanci cibiyoyin rijistar ita take kawo lakaki da jinkiri da a ke samu wajen yi wa wadanda su ke bin sahihiyar hanya dan samun yin katin shaidar dan kasar.

Exit mobile version