Yadda Al’ummar Mahaifar Kwamishinan Ruwa Na Gombe Ke Shan Ruwan Kududdufi

Daga El-Mansur Abubakar, Gombe

Shekara da shekaru al’ummar garin Pindiga da ke yankin karamar hukumar Akko a jihar su na rayuwa ne da ruwan wani kududdufi da ke gabar garin, inda a cewar jama’ar garin shi ne ruwan da su ke sha su ke rayuwa kuma da shi, duk da cewa nan ne mahaifar kwamishinan ruwa na jihar, Hon Dan’azumi Adamu.

Wakilinmu ya yi tattaki na musamman zuwa garin Pindiga inda ya samu zantawa da wasu da suka zo dibar ruwa a wannan Kududdufi ko Rafi inda ya samu jin bakin su kamar haka.

Wani mai suna Malam Abubakar ya bayyana cewa shi dan wannan gari ne na Pindiga kuma ya ce a gaskiya ba su da ruwan sha da ya wuce wannan domin shekara da shekaru shi su ke sha su ke rayuwa.

Malam Abubakar ya kara da cewa, da wannan ruwa su ke dafa abinci su ke sha da shi kuma su ke wanka da wanki da duk wani abu da a ke yi da ruwa da wannan ruwan kududdufi su ke yi.

Ya kuma tabbatar wa Leadership A Yau ta Lahadi da cewa, ba su da wata hanyar samun ruwa sai a wannan kududdufi shi ya sa ma su ka mika wuya kawai su ke shan wannan ruwa, domin idan ba su sha ba babu yadda su ka iya.

Malam Abubakar ya yi amfani da wannan damar wajen mika kokensu ga gwamnatin jihar Gombe da cewa ta yiwa Allah ta samar musu da ruwa domin su sami tsabtataccen ruwan sha kamar kowanne dan jiha, saboda a halin da a ke ciki yanzu ba su san dadin ruwan famfo ba idan ba wannan ba.

Shi ma Aliyu Shu’aibu wani mai sayar da ruwan a kuskus da ya zo diba dan sayarwa cewa ya yi addu’arsu dai Allah ya kawo ranar da za su sami ruwan famfo, saboda suma su san cewa sun shaida ribar mulkin siysa.

Aliyu Shu’abu ya kara da cewa akwai garuruwa kamar su garin Sabon Kaura da cikin garin Pindiga duk a nan su ke zuwa dibar ruwa safe da yamma da shi su ke girki da sha da sauran aikace-aikace.

Da wakilinmu ya ke sake tambayar Aliyu ko su na da wani waje da suke samun ruwa banda wannan kududdufi sai ya ce ba su da shi, su na rokon gwamnati ne da babbar murya, don ta samar mu su da ruwa.

Ya kuma bayyana min cewa su na sayar da kuskus daya a kan Naira 150 ne kowacce jarka kuma Naira 20 a kowacce rana, ya ce, ya na sayar da kamar amalanke biyar

Amina Idris wata matashiyar budurwa ce da na tarar tazo wanki a bakin wannan ruwa ta shaida min cewa ita wanki ta zo ba dibar ruwa ba, amma dai ita ma tana shan wannan ruwan domin yar garin ce ita.

Amina ta kuma ce a unguwarsu can Yamma da Pindiga da suna samun rowan, amma yanzu ya kare basu da wata hanya ta samun ruwan sai a nan.

Ta kuma ce su a unguwarsu suna samun ruwan Famfo idan an kawo wuta wani lokacin sau daya a sati.

Daga nan sai tayi roko ga gwamnati da ta samar musu da ruwan sha inda tace su a garin Pindiga shi ne matsalarsu.

Garin Pindiga dai bai wuce kilomita biyar ba zuwa Kashere garin su Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya Danjuma Goje, wanda kuma ya yi gwamna har sau biyu a Gombe sai ga al’ummar yankinsa su na shan ruwan kwari wanda duk lokacin da zai je Kashere garinsa na haihuwa ta wajen zai bi dole kuma ya ga wannan ruwa tunda a kusa da hanya ya ke.

Garuruwan da su ke shan wannan ruwa sun hada da garin Galadima da Pindiga da Sumbe da sabon Gari da wasu kananan kauyuka dake kewaye da wajen.

Da wakilinmu ya je ma’aikatar ruwa ta jihar Gombe, don jin ta bakin kwamishinan ruwan wanda dan wannan gari ne na Pindiga, Hon Dan’azumi Adamu, bai same shi ba amma da su ka hadu a wajen wani aiki sai ya ce kasar wajen ba a samun ruwa, amma da su na da famfo mai aiki da hasken rana wanda yanzu haka ya lalace amma za a gyara.

A bangaren karamar hukuma kuma wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban karamar hukumar Akko, Alhaji Jani Adamu Bello, ta wayar salula, sai ya ce ba zai ce komai a kai ba.

Exit mobile version