Abubakar Abba" />

Yadda Ambaliya Ta Yi Barna A Wasu Gonakin Shinkafar Taraba

Wasu daga cikin manoman shinkfa a jihar Taraba bana baau ji dadin noman ta ba a bana, musamman ganin yadda zaiyi wuya su samu wata babbar riba ko amfani mai yawa da auka saba samu a duk ahekara in sun noma shinkafar.
Hakan ya biyon yadda ambaliya ta yi barna a gonalan waau manoman dake shuka shinkafar.
Ambaliyar ruwa ta lalata daruruwan gonakin shinkafa a kananan hukumomin Gassol da Bali da ke Jihar Taraba.
Gonakin shinkafar wadanda suke a gefen Kogin Taraba dukkansu ruwa ya mamaye su tare da haifar wa manoma hasarar miliyoyin naira.
Rahotanni sun nuna cewa, wuraren da barnar ta fi muni su ne, yankin Bali da Tella da Sardirde; inda dubban manoman shinkafar suka yi hasarar shinkafa wadda ke gab da nuna.
A cewar wani manomi a yankin, Yakubu Yuguda, ya shuka buhunan shinkafa uku kuma ya kiyasta cewa zai samu sama da buhunan shinkafa 120, amma ambaliyar ruwar ta lalata gonarsa bakidaya.
Ya ci gaba da cewa, manoma sama da 50 da ke yankin Tella, su ma ambaliyar ta lalata gonakinsu.
Yakubu ya kara da cewa wadansu da suka yanke shinkafarsu, ruwa ya yi awon gaba da shinkafar kafin su gyara ta.
Bugu da kari, rahotani sun nuna cewa, dubban manoman na shinkafar su na noma ta ne a gabar Kogin Taraba mai tsawon kimanin kilomita 300 kuma ambaliyar ta mamaye daukacin gonakin da ke gabar kogin.
Shi kuwa wani manomin shinkafar Malam Bello Maigari, ya sanar da cewa a yankinsu na Sardirde dubban manoman shinkafa sun yi hasarar shinkafar wadda ke ganiyar nuna a sanadiyyar ambaliyar ruwan.
A cewar Yakubu, yankin na samar da shinkafa mai yawan gaske a duk shekara a jihar, inda ya kara da cewa, amma wannan matsalar ta ambaliya za ta haifar da karancin shinkafa a bana a jihar.
Ya ci gaba da cewa, akasarin manoman shinkafar da ruwa ya lalata gonakinsu sun karbi bashi ne don noma shinkafar, ga shi ruwa ya lalata ta.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar ta taimake musu da tallafi domin samun saukin radadin asarar da su ka tabka.

Exit mobile version