Yadda Amharawa Ke Tarbiyyantar Da ’Ya’yansu Ta Hanyar Dabbobi

Daga Sabo Ahmad, Kaduna

‘Yan kabilar Amhara wadanda aka fi sani da Abyssinians, kabilu ne da ke a Arewa da Tsakiyar tsibirin kasar Habasha. A bisa wata kididdiga da aka gudanar ta kasa, a shekarar 2007, jimillarsu ta kai yawan sha tara zuwa dari takwas da bakwai da kuma dari takwas da sha bakwai, inda suka hada da, kashi ashirin da bakwai da digo sha biyu na yawan al’ummar.            Wadannan al’umma, ana kuma sa su a cikin jerin kwararrun ‘yan kasar ta Habasha da ke Arewacin kasar Amurka. Al’ummar, suna ikirarin su jinsin Sarki Solomon ne kuma su mabiya addinin Kiristanci ne. Suna magana ne da yaren Nahiyar Asiya da kuma maganar zaurance ta Habasha.

Al’umar Amhara, suna amfani ne da suturarsu ta al’ada da suke sanyawa mai dauke da farin gashi da yafa tawul da kuma bargo marar nauyi a kafadunsu. Mafi yawancinsu suna zaune a tsibirai a matsayin rigakafin wani tirniki da zai iya fada masu, sai dai, hakan yana haifar masu matsalar yin tafiye-tafiye da kuma samun wasu ababen da suke bukata na rayuwa.

Mazajensu, suna zama ne a fili matan su kuwa daura da gidajen mazajen nasu, ‘ya’yansu kuma a  cikin gida suna kula da dabbobi. Su kananan manoma ne, suna yin noman ne  ta hanyar sanya wani sanadari da suke sanyawa a kan irinsu in za su yi shuka, idan shukar ta kai lokacin  girbi, suna yi ne da  hannayensu.

Suna yin girki ne da kashin dabbobi da suka shanya a gona bayan sun bushe. Abicin da suke ci ana kiran sa Injera bo wot wanda ake sarrafa shi da wani hatsi na gida, sai dai ga mutanen Habasha, irin abincin, ba cimar su ba ce. Akan kuma hada abincin da wake da nama. Yadda ake sarrafa abincin akwai cin rai matuka da kuma cin lokaci ga masu sarrafa shi.   Rashin tsaftaccen ruwan sha da rashin shuke-shuke, suna daya daga cikin ababen da suka addabi al’ummar.

Bugu-da-kari, irin wadan nan matsalolin da ire-irensu, sukan jefa al’umar a cikin matsalar karacin abinci a tsibiran nasu. Irin wannan annobar ta yunwa ta taba addabar al’ummar a shekarar 1974 da kuma 1984. ‘Ya’yansu masu shekaru biyar zuwa shida, sukan shafe lokutansu ne wajen lura da dabbobi da tumakan iyayen su. Wani abin sha’awa shi ne, yadda yaran suke halartar makarantun gwamnati, sai dai suna zuwa darasin ne na rabin rana saboda dimbin daliban da ke halartar makarantun. Kimanin kashi goma bisa dari ne na al’ummar suke da hanyar wucewa, kuma suna zama ne a cikin matsananciyar rayuwa.

‘Yan kibilar ta Amhara mutane ne da suke takama da kansu da kabilarsu da addininsu a fadin duniya. Sun karfafa al’adarsu a karni da dama da suka shige, kuma ba su yarda wasu sabobbin al’adun duniya sun gurbata musu al’adu ko addininsu ba.

Matsugunansu, sun gina su ne a kan tsaunuka don kariya daga ambaliyar ruwa, haka gonakinsu, a kan tsaunuka suke don kauce wa zai-zayar kasa. Dakunan kwanan ‘ya’yansu maza na kusa da dakunan iyayensu maza, kuma suna aurar da ‘ya’yansu mata suna da shekaru sha hudu, inda angwayen amaren sukan dara su da shekaru uku ko shekaru biyar. Sai dai, wannan al’adar ta auren, ta tsaya ne kawai a karni na ashirin. Kodayake,  gwamnatin mulkin mallaka ta kasar, daga baya ta tilasta sai yarinya ta kai minzalin shekaru sha takwas za a iya aurar da ita.

Mafi yawancin auratayyar ana gudanarwa ne ta hanyar tattaunawa tsakanin iyayen ango da na amarya ta hanyar gudanar da shagulgula don kulla igiyar aure. A ka’idar daura auren, ba lallai ba ne sai inda limami mai daura aure, haka kuma an bada damar a yi saki, tare da yin yarjejeniya kafin a wanzar da shi.

Al’ummar sun yi  amannar kula auren wucin-gadi ta hanyar sanarwa da baki a gaban shedu, inda  amarya za ta bada sadaki ga mai mata hidima a gida, sai dai, ba maganar gado tsakanin angon da amaryar, amma ‘ya’yan da suka haifa, za su iya cin gadon iyayen nasu. Malamansu ns addini kan yi aure idan sun so sai dai, ba za su iya yin saki ba, idan an samu haihuwa a auren, malaman nasu za su je dangin matar tasu su yi wa abin da aka Haifa addu’a.

Abin da aka haifa da mai jegon, za su zauna a gidansu mai jegon har tsawon kwana arba’in don ita da abin da aka haifa, su samu karfin jikinsu. In namiji aka haifa  bayan kwana arba’in, za a kai shi Coci don a yi ma sa Baftisima, in mace ce kuwa, bayan kwana tamanin da haihuwa. Ma su jego suna shayar da ‘ya’yansu har tsawn shekara biyu, ana bai wa yara ladabi har zuwa shekaru biyar zuwa bakwai, inda daga baya, in sun balaga za su iya yin sharholiyarsu amma a bisa ladabin da aka ba su.

Yaran suna kula da shanu da tumakan iyayensu, su kuma ‘yan matan ke taimakon iyayensu mata wajen aikin gida, kamar reno da dauko itace. Al’adarsu cike take da amfani da karin magana da wake-wake da amfani da ka’idojin da addininsu ya tanada, inda wadannan halayen suke kara wa ‘ya’yansu darussa har ta kasance sun dore da su in sun balaga. Bugu-da-kari, ganin ilimin sanin kimiyya bai riske al’ummar ba, sukan fassara wani sabon lamarin da ya shigo ga al’ummar. Haila ita ce tilo babbar misali da al’ummar ba su iya bayani a kai ganin cewa ba su da ilimin kimiyya, sai suka kirkiro da tatsuniyoyi don  fayyace hailar. A al’adarsu, namiji ne ke gaba da mace, kuma bisa tarihi kauraye haka gwamnatinsu, jaruman mayakansu ke bai wa sojojinsu umarni. Tatsuniyoyin su ne ke nuna surar jarumansu da suka zubar da jinin makiyya.

A bisa tatsuniyoyin nasu, abin bautarsu yakan yi wa mace baki ko dibar jininta duk wata domin a tunatar da ita cewa wata rana za ta iya fakuwa kuma ita mai yi wa mijnta hidima ce ga mahaifinta da mijnta, inda sakamakon biyayyarta za ta haifi lafiyayyun ‘ya’ya da zuri’a mai yawa da kuma samun jajirtacce da zai kula da zuri’arta. Akwai labarai da dama a cikin al’ummar da suke koya darasi  na kin nuna wa makiyi muguwar kiyayya amma a rinka gode wa makiyin domin in ba makiyin, ta yaya ne jarumai sunansu da matsayinsu za su daukaka a cikin al’ummarsu?

Exit mobile version