Tasallah Yuan Ta CRI Hausa" />

Yadda Amurka Ta Tsoma Baki Cikin Harkokin Hong Kong Zai Illata Moriyarta Da Ma Moriyar Kasar Sin

A ranar Laraba ne kwamitin harkokin wajen majalisun kasar Amurka, ya zartas da shirin dokar shekarar 2019 kan hakkin dan Adam da dimokuradiyya a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, wanda wasu ’yan majalisu suka gabatar, inda da sunan “hakkin dan Adam” da “dimokuradiyya”, suka nuna goyon bayan masu tsattsauran ra’ayi da masu bore a Hong Kong.
’Yan majalissar sun kuma tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin, sun saba wa dokokin kasa da kasa, da manyan ka’idojin daidaita huldar kasa da kasa, abin da suka aikata ya tono sharin wasu Amurkawa, na yunkurin ta da kura a Hong Kong, da hana ci gaban kasar Sin.
Da babbar murya, kasar Sin ta yi tir da hakan, kuma ta ki amincewa da shi. Yadda Amurka ta zartas da wannan shirin doka, zai aike da munanan sakwani ga masu bore a Hong Kong, yadda za su kara ta da hargitsi, lamarin da zai illata moriyar Amurka.
Cikin shekaru 40 bayan da Sin da Amurka suka kulla huldar jakadanci a tsakaninsu, Sin ba ta taba tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Amurka ba. Don haka kamata ya yi Amurka ita ma ta yi hakan.
Harkokin Hong Kong, harkokin cikin gida ne na kasar Sin. Bai dace ba wasu su taba zaton za su dakile karfin zuciyar kasar Sin, da aniyarta game da kare ikon mulkin kasa, da tsaro, da moriyar raya kasa, da tabbatar da wadata da kwanciyar hankali a yankin na Hong Kong. Kamata ya yi nan da nan, wasu Amurkawa su dakatar da yunkurin ingiza manufar dudduba shirin doka kan Hong Kong, su dakatar da makarkashiyarsu ta ta da rikici a Hong Kong.
Ko shakka babu, kasar Sin za ta mayar da martani mai karfi kan dukkan aikace-aikacen da suke illata moriyar Hong Kong, da moriyar Sin.

Exit mobile version