Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Zagayan Maulidi na gari duka a garin Katsina, shi ne taro mafi girma da daraja da cikar mutane da bunkasa tattalin arziki da nuna tsatsan soyayar Annabi Muhammadu (SAW) ta gaskiya da Gaskiya tare da nuna hadin kai a tsakanin al’ummar Musulmi.
Babu mutumin da zai yi musun abinda na ambata a sama, domin ya zuwa yanzu wannan biki ko in ce taro, ya zama daya tamkar da miliyan, ya kara bunkasa fiye da tunanin mai zuwa kallo, balanta wanda ya ce ba zai je ba, sai ya fi kowa cizon yatsa.
Haka kuma, duk wani taro da ake yi a Katsina ko dai na siyasa ko na sarauta ko na Addini kai koma na menene yanzu dai yana bayan taron zagayan gari duka da ake yi duk shekara a satin karshen watan Rabi’ul Awwal ko kuma farkon watan Rabi’ul Sani
Wani abin burgewa shine yadda jama’a daga wasu jahohi da suke daukar kaso mai tsoka wajan gudanar da wannan biki na tarihi da nuna kauna da soyayyar fiyayan halita Annabi Muhammadu (SAW) a birnin Katsinan Dikko mai masoyan Annabi (S)
Mutane daga jihohin Kano da Zamfara da jamhuriyar Nijar da Gombe da Jigawa da sauransu na daga cikin manyan manyan tawagogi da suke kara kayata wannan biki, saboda yadda suke hadewa da masoya Annabi Muhammadu (SAW) na Katsina da kewaye.
Wannan bikin ne kadai yake tsaida garin Katsina tsak, a yi yin da kowa ke bada hadin kai domin ganin wannan zagaye ya samu tagomashin da ya kamata, musamman wajan bada kyauta da cin hado da kwaliya irin ta kure adaka.
Duk wani matashi masoyin Annabi Muhammadu (SAW) a garin Katsina baban gurunsa shi ne, lokacin zuwan wannan zagayen domin kuwa ado abinda ake kira ado yana bayyana muraran a wannan rana saboda nuna kauna da soyayya ga fiyayyan halita Annabi Muhammadu (SAW).
Haka kuma duk wata basira ko hikima tana bayyana ne a wannan rana domin irin yadda tiloli da sauran masu aikin kawata taro ke amfani da tunaninsu wajan samar da sabon abu saboda wannan rana ya ishe mutun misalin cewa wannan biki ko zagaye na daban ne.
Anan gaba kadain zan yi bayanin irin bangarori daban-daban da suke cikin wannan ayari na zagayan Maulidi da suka hada da likitocin Manzon Allah da Arifai da Madihai da zakiran da Yarabawa da Buzaye da Fulani da Inyamurai da sauran nau’in mutane domin suma sun tabbatarwa da duniya kaunar ma’aikata.
Ina da tabbacin wadanda ke hade fuska da bata rai a wannan rana, a cikin garin Katsina ba su da yawa, kuma duk dibararka baka isa ka gansu a fili ba, kila a cikin gidajansu suke nuna rashin jin dadin da wannan biki.
Kamar yadda kowa ya sani, ana yin wannan zagaye a garin Katsina a karshen wannan watan Rabi’ul Awwal ko kuma farkon watan Rabi’ul Sani kamar yadda na fada a farko, wannan kuma ya samo dadadan asali wanda ba akan shi zanyi magana ba, amma dai idan a wannan karon ka fara jin labarin wannan zagaye da ake yi Katsina ina da tabbacin shekara mai zuwa da ke za a yi shi, Insha’Allahu.
Tun da farkon safiya bisa al’ada baban limamin Masallacin juma’a na Katsina ne ke fara fitowa tare da ‘yan tawagarsa domin fara wannan zagaye, sai dai shi a mota yake fita tare da doguwar tagawarsa mai albarka, sune kamar mafarin wannan biki.
Akwai tsare-tsare da kwamitici daban-daban domin ganin wannan biki bai hadu da cikas ba, saboda haka da zaran baban limamin ya yi na shi zagayan, kwamitoci za su fara na aikin tabbatar da komi yana tafiya cikin tsari kamar yadda aka tsara shi.
Wannan zagaye kamar yadda aka sani mawaka sha’irai sune suke fitowa fage da damar watayawa so sai domin ranar ta zamo tamkar ranar su ce, saboda daman ‘yan isalamiya tuni sun rigaya sun yi na su zagayan, saboda haka sai dai su zo kallo a wannan rana.
Kamar yadda na fada akwai tsare-tsare sannan suma jami’an tsaron ‘yan sanda suna cikin wannan babar sabga saboda sun dinga yin sintiri ke nan har sai an kammala da sauran jami’an tsaron da ‘yan agaji da ‘yan sa kai sauran su.
Duk wanda yasan anan wannan kasaitaccen biki, to na wannan shekarar daban yake domin kowa ya bada shaidar cewa duk da irin matsin tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta hakan bai hana su kashe kudi ba wajan kara burge masoyan Annabi Muhammadu (SAW) da suka yi dafifi wajan wannan kallo.
Bayan wucewa Baban limami da tawargarsa, wadanda ke biyo bayansa sune, zakirai inda zaka rika jin tashin zikiri daga Zakarai sannan akwai tawagar Madihai suma suna tafiya suna ishiriniya da karatun Al’kurni mai girma, abin burgewa shi ne yadda suke cin ado da kwaliya ta kaya iri daya saboda haka ana gane bako da zaran an rabe su.
A wannan zagaye dai har tawagar likitoci maosya Annabi Muhammadu (SAW) ke akwai sannan akwai tsarin Sha’irai masu jan gayya, tarihi ya nuna cewa babu wani sha’iri da ya yi fice wajan yabon Annabi Muhammadu (SAW) da bai taba halartar wannan biki ba a garin Katsina.
Saboda haka yanayin yadda ake cin ado da kwaliyya ta anko na kaya irin daban-daban kai kasan madinka masoya Annabi Muhammadu (SAW) sun kure tunaninsu a wannan shekara domin kara faranta ran masaya har ma da makiyan, idan mutun ya isa ya fito fili ya bayyana kanshi mana.
Wani abinda zai fara sawa ka ninka tunainka shine yadda tattalin arzikin garin Katsina ke bunkasa a lokacin guda kuma ga karin soyayyar ma’aiki, babu wani nau’in abin saidawa da zaka gani ba a saida ba.
A wannan rana kamshin turare da jama’a ke bin wadanda suka zo kallon suna fesa masu saboda Annabi (S) kaiwa ya isa wata guda kana kamshi, sannan duk wani mai sana’a da ta shafi harkar lema ko ruwan sanyi ko kek da wani abinci, ya saida a wannan rana.
Wannan fa ina fadin abubuwa da suka fatu ba duka, a’a ina fadin dan abinda na iya gani domin akwai wuraran da ban samu zuwa ba, sannan akwai abubuwan da ban gani ba, saboda haka nasan wani zai ce komi ban fada ba, to ba komi na gani ba kuma ba komi na sani ba, na fadi iyakar abinda idona wanda shima masoyin Annabi (S) ne ya gani.
Sannan kadda mai karatu ya ce wannan shi kadai zagayan da aka yi a garin Katsina idan watan Maulidi ya kama, ana wasu zagayan domin a wannan karon an yi guda uku kafin ayi na gari duka wanda shine sha kurukundum.
Zagaye na farko da aka fara yi shine, na ‘yan uwan Musulmi da aka sani da ‘yan shi’a sun gudanar da su ne ranar sha biyu ga watan Rabi’ul Awwal ranar da mahukunta a Najeriya suka ware a matsayin ranar hutu.
Sun gudnar da wannan zagaye na su cikin kwaciyar hankaili da caba ado da kwaliya inda suka zagaye kusan cikin garin Katsina domin nuna kaunarsa ga Annabi Muhammadu (SAW) kuma gaskiyas magana sun burge jama’a fiye da yadda suke yi a baya.