Yadda Baki ‘Yan Afirka Ke Shiga Takara A Zaben Amurka

Daga Rabiu Ali Indabawa

Yadda yanayin al’umar Amurka ke sauyawa ya karawa tsirarun al’umomi da ba fafaren fata ba kwarin gwiwar neman takarar mukamai – ciki har da sabbin zuwa.

“Wannan ya zamanto wani abu ne da jami’yyun biyu suka maida hankali akai cikin tsawon lokaci,” in ji Aled Contant, mazaunin birnin Washington da ya kware a fannin tsare-tsare a Jam’iyyar Republican wanda kuma ya taba zama sakataren yada labaran jam’iyyarsa a kwamitin kasa a 2008. Jam’iyyar Democrat ta fi maida hankali wajen nuna goyon baya ga tsirarun al’umomi, a cewarsa, ko da yake, kamar yadda jaridar Politico ta ruwaito a watan Yuli, sai da aka yi ca akan kusoshin jam’iyyar a shekarun da suka gabata kafin su fara amincewa da ‘yan takara bakaken fata a yankunan da bakaken fatar ba su da rinjaye. Mai yiwuwa jam’iyyar Republican “sai ta yi tukin tsaye a nan gaba,” a cewar Contant.

“Kasarmu na da girma da al’umomi iri-iri. Idan har za ka lashe zabe, zai yi kyau ka fito daga cikin al’umomi daban-daban ko kuma ka wakilci al’umomi da za su kada kuri’a. ………hakan kuma na nufin sai ka nemi karin ‘yan takara daga al’umar bakaken fata.” Amma ta yaya masu burin shiga siyasa wadanda ba fararen fata ba – musamman sabbin zuwa Amurka, za su iya samun tikitin takara? A cewar Nakuette Ricks, wacce na daya daga cikin ‘yan farko-farkon zuwa Amurka daga Afirka, da ke takara – a matakin karamar hukuma zuwa Majalisar Dattawa, samun horo, na da matukar muhimmanci.

Ricks tana takarar neman kujerar Majalisar Wakilai a Colorado. Kungiyoyi da dama sun taimaka mata wajen sa ta a hanya, ciki har da kungiyar New American Leaders, wacce ba ruwanta da jam’iyya, da kuma Emerge, wacce ke kimtsa mata don su tsaya takara a matsayin ‘yan Democrats. “Sun koya mana yadda za mu tara kudade, yadda za mu gabatar da kanmu, da yadda za mu rubuta jawabinmu. In ji Ricks tana mai cewa, “dukkan wadannan batutuwa suna da muhimmanci, saboda idan ka fita yin takara mutane za su san cewa ba wasa kake yi ba kuma mutane na sauraro.”

Ricks tana ‘yar matashiya, ita da iyayenta suka tsere daga kasarsu da sojoji suka yi juyin mulki.  A matsayinta na ‘yar kasuwa da ke renon ‘ya’yanta ita kadai kuma bakuwa, Ricks tana so a fito da matsalolin da ke addabar Gundumarsu, wacce ta hada da yankin Aurora da ke wajen birnin Denber. “Yankin ne mai al’umomi daban-daban,” a cewarta. “Mutum daya da cikin kowane mutum biyar zai ce maka daga wata kasa yake, ko daga China ko Burma kake ko kudancin Amurka ko Afirka, duk mun fito ne daga wurare daban-daban.”

A cewar Dabisha Johnson, masu aikin yakin neman zabe ma na bukatar a dora su a hanya. Shekara hudu da suka gabata, ta bude wani shagon sayar da kayan kwalliya a kusa da Atlanta da ke jihar Georgia. Wurin a karamar hukumar da ake kira Gwinnett yake, yankin da ya ga karin al’umar bakaken fata da bakin haure – ciki har da na Afirka ke karuwa tun daga shekarun 1990.

“Na lura cewa, ina bukatar na kirkiri hanyar da za a horar, a ilimantar da masu sha’awar ‘yan takarar,” in ji ta. Domin sanin mamakar yadda ake tafiyar da harkar yakin neman zabe, Johson ta shiga “wuraren da ake samun horo kan siyasa. ……….. hakan ya ba ni damar samun kwarewa sosai.” Johnson ta taimakawa wasu ‘yan takara samun nasarar lashe zabe, kama daga kwamitin karamar hukuma zuwa babbar kotun Georgia da majalisar dokokin jiha a jihohin Georgia da Tennessee.

 

 

Exit mobile version