Connect with us

ADABI

Yadda Baraka Ta Kunno Kai Ga Taron Ranar Marubuta Ta Duniya

Published

on

*Akwai Munafurci A Tafiyar – Fatima Danborno

Taron na Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya Karo Na Biyu da a ka yi a jahar Katsina cikin watan Maris da ya gabata ya zo da sammatsi da ya haifar da tazgaro saboda yawan rikice-rikice da su ka dinga kunno kai cikin babban kwamitin shirya taron da har iyuwar taron ya zama kila wa kala, saboda matsalar rashin samun kudaden da a ke hasashen za a iya kashewa, da rashin nagartaccen tsari, daga baya kuma lokacin da kudaden suka samu a kwamitin sai wata gawurtacciyar matsalar ta sake bulla ta zargin handame kudaden da kwamitin ya soma baratowa.

Wannan da wasu dalilan ne suka sa sai a daddafe aka ganganda a ka yi wannan taro a ranakun 16 zuwa 18 ga watan Maris 2018.

To haka a wajen yin taron ma, ba a wanye da marubuta a ta dadi ba saboda ayyana su da makaryata da mai gabatar da taron ya yi, wanda hakan ma ya fusata tawagar Kano har suka fice daga dakin taron gaba daya, saboda ganin yadda bambadanci ya sa taron marubutan ke neman rikidewa zuwa taron cin zarafin marubuta.

Wannan ya sa marubutan suka yi ta rubuce-rubuce a kafafan sadarwa na zamani don mayar da martani da kuma yin Allah wadai. To haka abubuwa suka ci gaba da tafiya a murde har bayan kammala taron ba a zauna lafiya ba, wata kila saboda rashin kyakkyawar manufa, da jagoranci, da kuma mutunta juna, da kuma uwa uba wuru-wuru da muna-muna. Wutar rikici dai ta ci gaba da ruruwa a tsakanin membobin kwamiti kullum sai fada kamar kaji.

To a ranar Lahadin da ta gabata ta 12/8/2018 kuma sai ga wata sabuwa ta sake bayyana wacce ita ma ta sake haifar da wani sabon rikicin na ce da ku ce wanda ya karade duniyar rubutu da marubuta, inda marubuci Malam Kabiru Yusuf Anka ya fitar wani rubutu da ya yi mai taken ‘An Ci Kudin Rubutu Da Marubuta’.

A cikin rubutun ne marubucin ya fayyace yadda wasu tsiraru daga cikin kwamitin suka yi watandar kudin da gwamnatin jahar Katsina ta ba marubutan don gudanar da wannan babban taro wanda yawansu ya kai Naira Miliyan Biyar, duk da dai rahotanni sun tabbatar da cewa Naira Miliyan Uku da rabi ne ta shiga hannunsu, ke nan jami’an gwamnatin da kudin ya biyo ta hannunsu su ma sun dauki kashi 30 cikin 100 ke nan, la’alla dokar aikinsu ce ta ba su damar hakan ko su ma gaban kansu suka yi don ganin ta fadi gasassa.

Wannan ne ya sa wasu marubutan ma suka soma fitowa suna tofa albarkacin bakinsu a kan wannan badakala, yayin da wasu ‘yan kwamitin kuma suka soma fitowa suna nisanta kansu da wannan aika-aika da aka aikata domin su ba su ma san da zuwan kudin ba ballantana watandar da aka yi.

Amma shugaban kwamitin Malam Rabi’u Na’awwa, a jawabinsa da ya wallafa da nufin kare kai, ya yi ikirarin cewa ai a kasafin ma da aka yi kasonsa N750,000 ya kamata a ba shi, amma N500,000 ya samu.

Wani abun zargin ma ga wancan kwamiti shi ne, rashin bayyanawa duk masu hakki cewa an karbo kudin, domin ba wai marubuta da suke nesa ko wadanda da ma suka nisanta kansu da taron ba, hatta ‘yan kwamitin da suka tsaya tsayin daka don ganin an yi taron cikin nasara ba kowa ne ya san da an karbo kudin ba balle a yi watandar da su.

Wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI ya tattauna da marubuciya Fatima Ibrahim Garba Dan-Barno, wacce mamba ce a wancan kwamiti ta ma gaba-gaba, sai ta ce “a gaskiya a lokacin farko da na fahimci akwai munafurci a cikin tafiyar, ba a son kowa ya ji maganar kudin nan, sai na watsar da komai na cigaba da tafiyata. Daga baya kwatsam sai a ke tambayata wai dubu dari nawa aka ba ni kasona? Na sha mamaki kwarai, don a sanina duk kudin da ake tafiya a kungiyance da shi, ba a cika amfani da su ba, sai dai a yi ta bunkusa tafiyar.

“Mutane da yawa daga cikin wadanda suka ci kudin ban yi mamaki ba, amma akwai wanda a na ambata min sunansa na ji hantar cikina ta kada. A nan kuma sai na fahimci duniyar nan ta gama lalacewa, domin a na zaton wuta a makera ne sai aka samu a masaka. Kawai sai na gane fadin gaskiyar da ya ke tinkaho da ita ashe duk talauci ne ya sanya ya ke maida kansa ustazu. Amma sauran kam babu wanda na yi mamaki, don za su yi fiye da hakan ma.”

Wakilin namu ya tambaye ta ko a matsayinsu na marubuta akwai matakin da za su dauka don a dawo da wani abu, sai ta ce, “babu shawarar da ba a yi ba a kan hakan, domin wasu su na cewa wai kudin wasu ne su ka fita su ka nema. Mu kuma mu na ganin kudin nan hakki ne na kwamiti, domin a cikin kwamitin nan akwai wakilan kungiyoyi wadanda aka yi amfani da logonsu wajen buga takardar da za a fita neman kudin. Idan so su ke su tsame marubuta, me zai hana kowannansu ya buga ‘letter headed’ dinsa ya fita neman kudi shi daya? Ba na tunanin duk wanda ya ci kudin nan, hakkin jama’a zai bar shi ya zauna lafiya. Mataki kuwa mun fara shirin mika wannan magana har zuwa kotu. To, ganin maganar ta cikin gida ce, mu ka yanke shawarar shirya zama na musamman da manyan marubutanmu, domin a kirawo wadanda su ka yi wannan aika-aikan domin kare kansu.”

Kan yiwuwar cigaba da yin taron duk bayan shekaru biyu da matakin da za a dauka don kaucewa hakan a gaba, Fatima ta ce, “ko wacce kanwa ja ce. Ba mu da bakin da za mu iya kallon wani mu ce shi ne na Allah. Amma a yanzu mu na shirya mataki, wanda nan ba da jimawa ba, za mu fito mu gayawa duniya matakin da mu ke shirin dauka.”

Wakilin namu ya ce dai zai cigaba da bibiya da bin diddigin lamarin, don jin yadda ta kaya har karshe.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: