Babu shakka masu kula da makabartu a nan Jihar Kano su na bakin kokarinsu karkashin kwamatin gyaran makabarta, a wani locacin kuma ana dora laifin kan gwamnati, dalili kuwa shi ne samar da kwamati guda a kan gyaran duk makabartar data lalace wannan ya sa mutane su ka zuba ido kawai gwamnati ta yi musu gyaran duk makabartar da ta lalace, wannan ba karamin kuskure ba ne, domin wancan kwamiti na kula da duk makabartar Jihar Kano sai fa an bashi zai zo ya yi aikin da ya kamata a duk makabarta, amma mutane sun manta cewa wannan guri ne da kowa nan za a kai shi .
Zan yi magana a kan al’ummar Jihar Kano da ma na wasu jihohin a kan makabartunmu, abin na ke so na ce shi, Allah ya azurta mu da masu kudi da dama, ku fidda ranku cewa wai gwamnati sai ta zo ta gyara muku makabartunku. Wannan lokaci ne na damuna, idan ka je ka shiga duk makabartar dake yankinmu na Arewa zaka ga abin ta kai ci kuma wannan lalacewar bata gagari mutanen yankin su yi maganin ta ba, akwai mutum daya wanda zai iya ba da gudunmawar tifa 50 kuma bai girgiza ba, duk matsalar makabarta abin da yake da munta shi ne zaizaya ko idan an yi ruwa kabari ya rufta, amma wannan taimakon sai ya gagara, bayan makabartar nan tabbas idan ka mutu nan fa za a kai ka, amma wannan taimakon ya gagara, kowa ya na jiran gwamnati ta zo ta gyara.
To, a gaskiya kirana ga al’umma mu sake tunani domin duk makabarta ta kowa ce mu hadu mu gyara domin na tabbata yanzu da al’ummar ko wacce unguwa za su bayar da tallafin ko da Naira 50 ce kawai, to za a sha mamaki irin kudin da za a tara wajen gyaran makabartar a ko wanne yanki. Mu daina cewa muna jiran gwamnati ta zo ta yi mana, domin abubuwa sun canja.
A yi taimakon kai da kai shi ya kamata mu sa a gaba domin yanzu babu wani da zai saurari kukan duk wani kwamiti dake neman tallafin gyara makabarta, saboda yanzu babu mai neman mukamin komai a wajan talakawa sai nan gaba ka dan idan wani zabe ya matso za ka ji kai tallafi iri-iri, domin lokacin bukatarsu ya zo wasu daga cikinsu ke nan.
Kirana ga masu wadata wanda su ke neman lada domin zuwa gobe ranar lahira su dauka su je makabartun da ke fadin Jihar Kano akwai wanda lalacewar abin ta kaici ne kwarai da gaske za su ga kabari a waje ko a kusa da ruwa ko da yaushe ruwa yana iya tafiya da shi Allah ka tsare mu.