Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na kara fuskantar kalubale a kakar bana, bayan da ‘yan wasanta da dama ke yin jinya kawo yanzu wanda hakan yana daya daga cikin matsalolin da suka addabi kungiyar.
Real Madrid wadda take rike da gasar La Liga, ba ta kare kofinta na Spanish Super Cup ba a shekarar nan, an kuma yi waje da ita a gasar cin kofin Copa del Rey bayan karamar kungiyar Alcoyano ta doke ta a watan daya gabata.
Kungiyar ta mayar da hankali ne yanzu kan lashe La Liga wanda take ta uku a kan teburin wasannin bana da kuma gasar cin kofin zakarun turai na Champions League da za ta kara da kungiyar Atalanta cikin watan nan na Fabrairu.
To sai dai da yawan ‘yan kwallon Real Madrid na fama da jinya da hakan zai iya zama barazana kan kokarin da take na ganin ta tsira da kofi a kakar nan duk da cewa kungiyar bata kokari musamman idan tana buga wasa da karamar kungiya.
Ranar Talata Real Madrid ta kara da Getafe, kuma daman Albaro Odriozola da kuma Eder Militao ba su buga karawar ba saboda jinya sannan kimanin ‘yan kwallon Real Madrid 10 ne ke jinya kuma Toni Kross na hutun hukuncin katin da aka bashi.
Sau 38 ‘yan wasan Real Madrid guda 20 suka yi rauni a kakar bana mai cike da kalubale sai dai daman Real Madrid ba ta dauki dan kwallo ba a kakar wasa ta 2020 zuwa 2021, kuma cutar korona ta kawo tsaiko da ta kai ana buga wasanni da yawa a karamin lokaci.
Real Madrid wadda take ci gaba da fuskantar barazanar rashin nasara za ta fuskanci kalubale a watan Fabrairu, wadda za ta yi wasanni shida har da daya a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League a bana.
Real Madrid ta kai zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai, sai dai tana ta uku a teburin La Liga da maki 43 iri daya da wanda Barcelona keda shi ta biyu a teburi kuma Atletico Madrid ce ta daya mai kwantan wasa daya da tazarar maki 9 tsakaninta da Barcelona da Real Madrid.
A cikin watan Janairu aka fitar da Real Madrid daga gasar Spanish Super Cup da kuma Copa del Rey na bana wanda hakan yasa yanzu gasar La liga da kofin zakarun turai ne kadai gasar data ragewa kungiyar da zata iya lashewa.
Saboda haka ya zama wajibi Real Madrid ta saka kwazo a watan na Fabrairu, idan ba haka ba ta fuskanci kakar bana ba tare da ta lashe kofi ba kuma Real Madrid za ta fara wasan farko cikin watan Fabrairu ranar Asabar, inda za ta ziyarci kungiyar Huesca domin buga gasar La Liga.
Sannan kwana uku tsakani Real Madrid za ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Getafe a kwantan wasan tun na makon farko da basu buga ba sakamakon dage wasan da akayi saboda nisan da sukayi a gasar zakarun turai na kakar data gabata.
Real Madrid za ta ziyarci kungiyar kwallon kafa ta Atalanta domin buga wasan farko a zagaye na biyu a gasar Champions League ranar Laraba 24 ga wata sannan kungiyar za ta karkare watan Fabrairu da gasar La Liga da za ta karbi bakuncin Real Sociedad.
Wasannin da Real Madrid za ta kara a Fabrairu:
Ranar Asabar 6 ga watan Fabrairu La Liga
Huesca vs Real Madrid
Ranar Talata 9 ga watan Fabrairu La Liga
Real Madrid vs Getafe
Ranar Lahadi 14 ga watan Fabrairu La Liga
Real Madrid vs Balencia
Ranar Lahadi 21 ga watan Fabrairu La Liga
Balladolid vs Real Madrid