Umar A Hunkuyi" />

Yadda EFCC Ta Yi Kwanton Bauna A Kotu Don Kama Ajumogobia

An yi wata ‘ya kwarya-kwaryar dirama a harabar babbar kotun da ke Ikeja, a sa’ailin da jami’an hukumar EFCC suka yi kwantan bauna a kokarin da suke yi na kama tsohuwar Alkaliyar babbar kotun tarayya, Mai Shari’a Rita Ofili Ajumogobia.
Hakan kuwa ya faru ne bayan da Mai Shari’a Hakeem Oshodi, ya yi watsi da dukkanin tuhumomi 30 da ake yi wa ita Mai Shari’a Rita Ofili Ajumogobia.
Ajumogobia, tana fuskantar tuhuma ne a kan cin hanci da rashawa da kuma yin amfani da kujerarta ta hanyar da ba ta dace ba.
Kotun ta yi hukunci da cewa, abin da hukumar ta EFCC ta yi, kokari ne na batawa kotun lokaci kawai.
Alkalin kotun ya kaniyanci hukumar ta EFCC a kan neman da ta yi na a yi watsi da shari’ar, a kan wani hukunci da kotun daukaka kara ta yi, inda ta goyi bayan wani Alkali da ake tuhuma da cin hanci.
Ajumogobia, ta fita ta bar kotun, amma sai ta sake dawowa cikin kotun, ta ma haye can sama a lokacin da ta ga wasu dakarun hukumar ta EFCC suna ta zare idanu, suna jiran ta taka kafarta a wajen kotun su sake yin awon gaba da ita.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Ajumogobia, tana boye a cikin kotun, sa’ilin da su kuma jami’an hukumar ta EFCC suke bakin kofar shiga kotun suna jiran fitowarta su kama ta.

Exit mobile version