Abubakar Abba" />

Yadda Garkame Iyakokin Nijeriya Ya Sa Tattalin Arziki Karuwa – Nanono

Garkame iyakokin Nijeriya na kan tudu da Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin ayi, bai janyo wa tattalin arzikin kasar nan wani nakasu ba.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin Ministan noma da raya karkara Alhaji Sabo Nanono.
Ministan wanda ya sanar da hakan a hirarsa da manema labarai a babban birinin tarayyar Abuja ya ci gaba da cewa, garkame iyakon kasar nan hakan yama kara habaka tattalin arzikin kasar ne, musamman a fannin aikkn noma.
Ya cigaba da cewa, rufe iyakokin na kasar nan, bai saba yanjeniyar kasuwancin kasashen Afirka ba, inda kuma Ministan ya yi nuni da cewa, matakin na  gwamnati kan hakan, don ya kare kasar nan aiwatar da ayyukan barna da ake yi aikatawa akan iyakokinta.
Alhaji Sano ya kuma yi nuni da cewa, yarjeniyar kasuwanci ta kasashen Afirka ba ta ce Nijeriya ta zama abin dama, domin baza mu kara bari a mayar da Nijeriya wajen jibge kayan da ake shigowa dasu daga kasashen ketare ba.
Ya yi nuni da cewa, wasu kayan da ake shigowa dasu  daga kasashen ketaren, basu da wani inganci, musamman abincin yawanci duk sun gama aiki a kasashen da ake sarrafa sannan kuma a shigo mana dasu cikin Nijeriya, sam gwamnati, bazata kara lamuntar hakan ba.
A cewar Alhaji Sabo, ba a rufe iyakokin don a cutar da yan Nijeriya bane, saidai ma don a kara haka tattalin arzikin kasar, inda ya kara da cewa, bawai kawai an rufe bane, sai da aka natsu a ka duba abubuwa da dama kafin a rufe iyakon na kasar nan kima sai da gwamnatin ta dauki wasu matakai kafin ta yi hakan, musamman idan akayi la’akari da ayyukan barnar da makwabtan suke a kan iyakokin kasar nan ke tabkawa, inda ya sanar da cewa, an dauki matakin ne don a kare Nijeriya yan kasar.

Exit mobile version