Yadda Garkuwa Da Dalibai Ke Haifar Da Koma-baya Ga Ci Gaban Ilimi A Arewa
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Garkuwa Da Dalibai Ke Haifar Da Koma-baya Ga Ci Gaban Ilimi A Arewa

byIdris Aliyu Daudawa
2 years ago
Dalibai

Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta nuna rashin jin dadinta akan yadda ‘yan ta’adda suke samun damar  shiga makarantun da suka hada dana Sakandare  da kuma  manyan makarantu wadanda ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka da suka hada da har da garkuwa da mutane.

Wata sanarwar da aka rabawa amnema labarai a Abuja da ke dauke da sa hannun Shugaban kungiyar Farfesa. Dokta D.D. Sheni,ya bayyana an kusa shekara goma tun lokacin da aka dauki ‘yan makarantar mata ta Chibok masu yawa ta Jihar Borno, sannu a hankali sai al’amarin garkiwa da ‘yan makaranta yake daukae  wani sabon salo.

  • Shawarar Kasar Sin Ta Gina Al’ummar Duniya Mai Mokamar Bai Daya
  • Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Wa Matar Da ‘Yan Bindiga Suka Raba Da Muhallinta Shatara Ta Arziki

“ Yayin da ake ci gaba da fuskantar al’amarin na garkuwa da ‘yanmakaranta wanda kuma hakan ya nuna gazawa ta gwamnati wajen ceto yawancin ‘yan matan na Chibok daga wurin wadanda suka yi garkuwa da su, ana cikin hakan ne kuma sai ga maganar na ‘yan makarantar Dapchi  wani abin ban takaici bayan an dauke sum ranar da za a maido dasu su ‘yan ta’addar ne suka maido su makaranta aka ce kada a yi masu wani abu. Hakan abin ya ci gaba da faruwa dar ya kai Kankara, Kagara,Kaduna da Kangebe, zuwa Yawurin Kebbi daga nan sai can sai dai fatar Allah ya kara kiyaye mu gaba daya.

Maganar awon gaba na’yanmata 46 da suke karatu a jami’ar tarayya ta Gusau wadanda ‘yan ta’adda suka dauka wannan ba shi bane lokaci na farko, kusan wannan zuwan ‘yan ta’addar na uku ne a jami’ar gwamnatin tarayyar.

“Irin yadda aka ci mutunci wajen kai farmaki wurin kwanan dalibai mata yadda aka shiga wurin kwanan na su haka aka shiga wurin kwanan dalibai na makarantar Dapchi,wanda shi an samu rasa rayuka da raunuka masu muni wajen daukar ‘yan makaranta da basu ji basu gani ba,yawancinsu matasa ne masu shekara goma sha”.

Dattawan na Arewa sun ce abin akwai ban takaici na yadda ake yawan daukar dalibai ‘yan makaranta ana garkuwa dasu,wannan aikata laifin ‘yanta’adda ne suke yin hakan saboda an samu rashin halin ko in kula na wasu jami’an tsaro da suke nunawa kan aikin nasu, irin hakan ne su ‘yan ta’addar suka yi amfani da  damar da suka samu.

Sun ci gaba da bayanin “Abin yana  daure mana kai,mu yadda da cewa lokacin da gwamnati take bugun kirjinta tana maganar ta sawo sabbi kayan fada har ma da jirage masu saukar angulu,wadanda aka samar masu da isassu,sai dai kash! rashin kishin kasa sai ga ‘yan ta’addar suna ta  shige da fici suna abinda suka dama a Arewa babu mai  ce masu ko uffan.

“’Yan Nijeriya baki daya da al’ummar Arewa shekarubn da  suka gabata rayuwarsu da harkokin kasuwancinsu na yau da kullun al’amarin tabarbarewar tsaro da ya  shafi amfani da tsattauran ra’ayin addini, ta’addanci, matsala tsakanin manoma da makiyaya,ga kuma garkuwa da al’umma kamar yadda kungiyar ta bayyana.

Kungiyar ta yi kira da gwamnatocin tarayya, Jihohi, kananan hukumomi da su hada kai wajen daukar dukkan matakin daya dace wajen tabbatar da samarwan al’ummarsu  tsaro ta hanyar samar da wadanda za su sa ido kan al’amarin daya shafi tsaon al’umma  a duk inda suke domin kulawa dasa ido kan al’amarin tsaron lafiya da dukiyar al’umma.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce
Manyan Labarai

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya
Rahotonni

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

October 4, 2025
Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin
Rahotonni

Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin

October 3, 2025
Next Post
Pushpa Kamal Dahal

Pushpa Kamal Dahal: Gasar Wasannin Asiya Na Da Muhimmiyar Ma’ana Ga Al’ummomin Kasar Nepal

LABARAI MASU NASABA

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version