Yadda Ginin Majalisar Kasa Ya Yi Yoyu Sakamakon Ruwan Sama A Yau

Yoyon

Rahotonni daga zauren Majalisar Tarayya sun shaida yadda rufin Majalisar ya dinga yoyo sakamakon saukar ruwan sama marka-marka tunda safiyar yau Talata a birnin Tarayya Abuja. An ga hotonan ma’aikatan majalisar sun aiki kwashe ruwa a tsakar majalisar.Ruwan

Hotunan sun jawo muhawara a kafafen sada zumunta, inda al’ummar Nijeriya suke ta cece-kuce kan faruwar lamarin, kamar dai yadda aka saba, in wani abu ya faru ‘yan Nijeriya suna tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada Zumuntar.

Lamarin ya hana zaman Majalisar gaba dayanta, wato majalisar Dattawa da ta wakilai, a daidai lokacin da suke zaman muhawara a kan wasu kudirori da aka gabatarwa Majalisar, an dau lokacin kafin membobin Majalisar su dawo zaman muhawarar.

Exit mobile version