Daga Abdullahi Sheme,
A ranar Alhamis din data gabata ne da misalin karfe 9 da minti 15 gobara ta kara tashi a kasuwar bakin babbar Asibitin garin Funtuwa da ke jihar katsina a sanadiyyar dawowar wutar lantarki gobarar wadda ta dauki sama da awa 3 tana ci inda a ka yi asarar dukiya ta sama da Naira Miliyan 60, wannan gobarar ba ita ce karo na farko ba domin an samu wannan iftala’in kusan sau 3 kenan a na samun mummunar gobarar a wannan kasuwar sai dai ba a samu asarar rayuka ba ko a shekarar data gabata, sai da Gwamnatin jiha ta taimaki ‘yan kasuwar da gobarar ta shafa da taimakon Miliyoyin naira don taimakamasu A lokacin da Hakimin Funtuwa Sarkin Maskan Katsina Alhaji Sambo.Idris Sambo ya zagayawa da manema labarai tare da rakiyar mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwar jihar, Alhaji Musa Shugaba Funtuwa da shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na karamar hukumar Funtuwa, Alhaji Sule Garba da shugaban kungiyar ‘yan kasuwar na bakin Asibitin Alhaji Mujitaba sun jajanta wa ‘yan kasuwar da suka yi asara da Allah ya maida masu da mafi Alkhairi ya kara tsarewa, tun farko a nasa jawabin Sarkin Maskan Alhaji Sambo Idris Sambo ya tausayawa ‘yan kasuwar da fatan Allah ya mayar masu da mafi alheri ya ce, ya zama wajibi a hukumance su zauna su gano matsalar dake haifar da wannan gobara kusan a kowacce shekara kusan shekaru 3 kenan ana samun gobarar a wannan kasuwa ta bakin asibitin wannan abin bakin ciki ne kuma abinda yakamata a bincika ne don kawo karshen lamarin, Alhaji Sambo Idris ya ce, haka a baya a ka rika samun gobara a makarantar SBRS ABU dake nan Funtuwa kusan a koda yaushe saida hukuma ta tashi tsaye sannan lamarin ya zo karshe, Alhaji Musa Shugaba ya ce, ba shakka ‘yan kasuwar sun yi asara mai yawan gaske da fatan Gwamnatin jihar katsina a karkashin jagoranci Alhaji Aminu Bello Masari za ta kara taimaka wa wadanda suka yi asarar ganin yadda yadamu da ‘yan kasuwar jihar wajen taimakamasu da ya ke yi a kodayaushe.
A nasa jawabin, daya daga cikin manyan ‘yan kasuwar jihar Alhaji Bilya NAK ya tausayawa ‘yan kasuwar da fatan Allah ya maida masu da mafi alkhairi ya kara tsare wanman iftala in sannan ya yi kira ga Gwamnatin jihar da ta kara samar da jami’an kashe gobara a karamar hukumar Funtuwa daga karshe ya yaba wa jami’an kashe gobarar karamar hukumar don sun yi kokari sosai.