- Tuni Mu Ka Kaddamar Da Bincike, Cewar FFS
A jiya Laraba ne ofishin Akanta Janar na kasa ya kama da wutar gobarar da ta babbaka wani sashe na ofishin, inda hakan ya janyo asarar kadarori masu tarin yawa wadanda har zuwa yanzu ba a kai gama gano adadin asarar da gobarar ta haifar ba.
Ofishin da a ke yi wa inkiya da Baitul Malin Nijeriya (Treasury House) ya kama da wutar ne bayan da gobarar ta fara ci daga hawa na uku da ke gidan, inda wutar ta fantsama zuwa sassa daban-daban na cikin ofishin. Sai dai rahotonni sun tabbatar da cewar jami’an kashe gobara na Abuja sun yi matukar kokarin kashe ta ba tare da yin mummunar barnar da ta zarce kima ba.
Hukumar ‘yan kwana-kwana ta kasa, wato Federal Fire Serbice (FFS), ta sha alwashin binciko musabbabin tashin gobarar da ya barke da tsakar ranar a jiyan.
Mai magana da yawun hukumar FFS, Ugo Huan, ta shaida wa majiyarmu cewar tuni su ka kaddamar da fara bincike kan musabbabin tashin gobarar.
“Tashin wutar gobara a ofishin Akanta Janar na kasa da ke Abuja mun kashe wutar sannan tunin binciken musabbabin tashin wutar ya fara kan-kama nan take,” a cewarta.
Kawo yanzu dai babu wanda ya san makasudin tashin wutar sakamakon cewar ma’aikatan hukumar suna gida domin bin dokar zama a gida da gwamnatin tarayya ta sanya don kare kai daga yaduwar cutar Koronabairus, sai dai bincike ya nuna cewar akwai wasu ma’aikata da suke zuwa aiki a sakamakon bukatar hakan.
Wakilinmu ya rawaito cewar a lokacin da wutar ya tashi fal-fal, cikin hanzari Jami’an kashe gobarar suka kai dauki domin kashe wutar inda suka samu nasarar hakan bayan wutar ya kone kadadodi da daman gaske.
A bincikenmu mun gano cewar ayyukan inganta ma’aikatar na cigaba da gudana a harabar ofishin kafin tashin wutar da suka hada har da na’urorin wutar lantarki da sauransu.
“Akwai aikin da ke ci gaba da gudana a harabar ma’aikatar. Kamar yanda aka saba dai ma’aikata suna aiki dare da rana.”