Nasir S Gwangawazo" />

Yadda Gwamnan Bauchi Ya Bai Wa Kansa Kwangilar Naira Biliyan 3.6

Wani bincike ya nuna cewa, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya saki layi sakamakon bai wa kamfaninsa mai suna Adda Nigeria Limited kwangila ta zunzurutun kudi har Naira Biliyan 3.6, lamarin da ya saba wa dokar kasa a matsayinsa na jami’in gwamnati.

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin rahoton da jaridar Premium Times ta wallafa a ranar 22 ga Fabrairu, 2020, bayan ta gudanar da wani zuzzurfan bincike. Idan dai za a iya tunawa, Premium Times ce ta gudanar da binciken da ya kai ga tsohuwar Ministar Kudi a Nijeriya, Kemi Adeosun, ta sauka daga mukaminta ba a cikin shiri ba sakamakon karyar takardar hidimar kasa da ta sheka. A wannan karon jaridar ta bankado zargin aikata wata ta’asa ne da gwamnan na Bauchi ya tafka jim kadan bayan darewarsa karagar mulkin jihar.
Tun kafin ya zama gwamnan jihar Bauchi, EFCC ta rika tusa keyar Sanata Bala Mohammed din a bisa zargin watanda, cin hanci, karbar rashawa da wawushe kudin gwamnati a lokacin ya na Ministan Abuja. Ba a kai ga kotu ta yanke ma sa hukunci ba ne, kwatsam sai ya zama gwamnan jihar Bauchi, inda ya kada gwamna mai ci a lokacin, wato Mohammed Abubakar na APC, a zaben 2019. Hakan ne ya tilasta wa EFCC dakatar da shari’ar da ta ke yi ma sa sakamakon rigar kariya da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba shi a matsayin gwamna.
To, amma binciken Wakilin Premium Times ya nuna cewa, daga darewarsa mulkin jihar, sai Gwamna Bala ya dumtsa hannunsa cikin baitilmalin jihar, inda ya bai wa kamfanin da shi ma ya na da hannun jari a ciki har na kashi 25 cikin 100 kwangilar sayen motoci guda 105, don raba wa manyan ma’aikata da ’yan majalisar jihar.
A wani binciken kwa-kwaf da Premium Times ta yi ta gano cewa, har yanzu dai a bayanan da ke kasa a rijistar hukumar kula da kamfanoni ta kasa, CAC, sunan Gwamna Bala na jerin sunayen masu mallakin wannan kamfani na Adda Nigeria Limited.
Jaridar ta gano cewa, ko a wadannan motocin da za a sayo sai da a ka kara kudaden farashinsu fiye da yadda a ka saka tun a farko za a siya.
Bayan kauce wa ka’idojin da doka ta gindaya na yadda za a bi wajen sai dole an tallata ire-iren manyan kwangiloli irin haka ne ya sanya tsohon kwamishinan kudin jihar, Nura Soro, ya sauka daga mukaminsa bayan ya ja kunnen gwamnati a kan batun, ita kuma ta yi ma sa kunnen uwar shegu, inda ta yi gaban kanta. Don haka ne Soro ya sauka, saboda kauce wa tsintar kansa cikin wannan cakwakiya, musamman ma da ya ke ko a cikin kasafin kudin jihar na 2019 Naira biliyan daya ne kacal a ka amince a sayo motocin da su, kuma a binciken jaridar ba ta samu hujjar cewa, an yi gyara a kasafin kudin jihar, don tanadin karin kudin da a ka samu har na Naira biliyan 2.6.
daya daga cikin ka’idojin da a ka karya sun hada da yadda gwamna ya sanya hannu a takardar amincewar bayar da kwangilar a ranar 9 ga Satumbe, 2019, wato kwana daya ma kenan kafin a rantsar da Majalisar Zartarwar Jihar, wacce ke da ikon dubawa da amincewa da kwangilar. Don haka ba a iya tattauna batun ba sai a ranar 11 ga watan, inda a nan wancan tsohon kwamishina ya yi jan kunne kan zargin karya ka’idojin.
Bincike ya nuna cewa, shi dai kamfanin Adda an kafa shi ne tun a 1996 da hannun jari na Naira 500,000, sannan da masu hannun jari hudu. Abdullahi Salihu Bawa ne ke da kaso mafi tsoka a jarin kamfanin na naira 200,000, sannan gwamna Bala da wasu mutane biyu na da hannun jarin Naira 100,000 kowannensu, inda a ke tsammanin sauran biyu ’ya’yan Abdullahi Bawa ne.
Gwamna Bala ya yi amfani da adireshin gida mai lamba 227 kan Titin Gombe a takardun yin rajistar wannan kamfani. A binciken da Premium Times ta yi game da wannan gida ta gano cewa, wannan gida na mahaifin Gwamna Bala, Sarkin Duguri, ne. Yanzu wasu ’yan uwansa ke zama a gidan, sai kuma idan wansa ya zo Bauchi Sallah, wanda shi ne ke rike da sarautar mahaifin ta Sarkin Duguri.
Bincike bai nuna ma na ko waye Abdullahi Bawa ba a Bauchi, domin kamfanin ba shi da shafi a yanar gizo da za a iya dubawa, don samun cikakken bayani a kansa ba har zuwa yanzu. Bugu da kari, bincike ya nuna cewa, kamfanin ya sake nada Gwamna Bala a matsayin darakta a kamfanin a 2006 a hukumar CAC. Amma kuma duka takardun da a ka bincika daki-daki ba a ga inda Gwamna Bala ya yi sallama da wannan kamfani ba.
Sai dai ganowa da a ka yi a takardun bayanai na kamfanin daga 2006-2018 cewa Gwamna Bala ya na nan daram a matsayin darakta a wannan kamfani har a lokacin da ya ke ministan Abuja, inda hakan ma karya doka ce.
A haka ne kuma, a daidai lokacin da za a ba wa wannan kamfani kwangilar, sai kamfanin ya sanar wa CAC a Agusta na 2019 nadin wani amini kuma makusancin Bala, mai suna Abdullahi Yari a matsayin Sakataren Kamfanin.
Premium Times ta nemi ji daga bakin kakakin gwamnatin jihar Bauchi, Mukhtar Gidado, inda ya tabbatar da lallai gwamnatin jihar ta ba da kwangilar sayo wadannan motoci har guda 105, sannan ya tabbatar da cewa, lallai kusan duka sun shigo Najeriya har ma an raba su, sauran da su ka rage su na sa ran za su iso Bauchi nan da kwanaki kadan masu zuwa.
Sai dai kuma ya gargadi Premium Times da ta je ma’aikatar yi wa kamfanoni rijista CAC, domin tantance ainihin sahihancin wannan kamfani da ta ce har yanzu Gwamna Bala na da hannun jari a ciki, domin a nan ta yi kuskure ba haka ba ne.
Daga baya da a ka aika ma sa da hujjojin da kuma takardun tabbacin haka da sai ya kauce, ya tsuke bakinsa ya yi shiru har yanzu bai ce komai a kai ba, sai dai ya kafe cewa, gwamnan ba ya cikin daraktocin kamfanin, duk da cewa, an aike ma sa da takardun shaidar da ke nuna hakan.

Exit mobile version