Daga Khalid Idris Doya, Gombe
Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ya nada Malam Danladi Sanusi Maiyamba a matsayin sabon Mai Tangale, wanda zai cigaba da jagorantar babbar masarautar gargajiyar dake Billiri.
Zuwa yanzu, Malam Maiyamba shine ya zama Mai Tangale (sarki) na 16 da masarautar Tangale ta yi a bisa tarihi, hakan kuma ya faru ne sakamakon rasuwar wanda yake kai a watannin baya.
Kafin wannan ranar nadin da aka yi a jiya, karamar hukumar Billiri ta fuskacin tashin-tashina da fadace-fadace sakamakon btutuwan da suka shafi nadin sabon sarkin, inda wasu suka yi zanga-zangar da har ta juya zuwa tashin-tashina.
Alhaji Ismaila Uba Misilli, daraktan yada labarai na gwamnatin jihar Gombe, shine ya sanar da nadin sabon Mai Tangalen da gwamnan ya yi a jiya Laraba, 3 ga Maris, 2021, a cikin sanarwar da ya rabar wa ’yan jarida.
Sanarwar ta ce, “bisa ikon da doka ta ba shi a karkashin dokar masarautu ta Jihar Gombe ta shekara ta 2020, kuma bisa zabi da shawarin da masu nada Mai a kasar Tangale suka ba shi, Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da nadin Malam Danladi Sanusi Maiyamba a matsayin sabon Mai Tangale.”
Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi Da Masarautun Gargajiya, Hon. Ibrahim Dasuki Jalo, ne ya sanar da amincewar gwamnan tare da mika wa sabon Mai din wasikar nadin sa a Poshiya da ke Billiri, ya ce nadin na Malam Danladi Maiyamba ya biyo bayan dacewar sa ne da kuma cancantarsa.
An mika wasikar nadin ce kan idon shugabar karamar hukumar Billiri da masu zaban Mai na masarautar Tangale su tara, da ‘yan majalisar masarautar da sauran jiga-jigan yayan masarautar.
Sanarwar ta ce, “Nan ba da jimawa ba za a mika wa sabon Mai din sandar girma da za ta alamta rantsar da shi bisa karagar mulki.”
Idan za ku iya tunawa dai tun bayan rasuwar Sarkin Mai Tangale a watannin baya, karamar hukumar Billiri ta samu kanta cikin tashin hankali kan zabin sabon sarkin lamarin da ya kai ga gwamnatin jihar sanya dokar hana fita na tsawon awa ashirin da hudu kodayake an sassauta daga baya biyo bayan lafawar matsalar.
A kuma watan Fabrairun da ta shude ne gwamnan ya dakatar da shirye-shiryen zabin sabon Mai Tangalen dukka bisa ga rikicin da ya barke wanda aka samu asarar rayuka da dukiyar jama’an Billiri.
Wakilin LEADERSHIP A YAU ya labarto cewa, tun bayan nadin sabon Sarkin babu wani tashin hankali da ya sake faruwa, hakan bai rasa nasa da matakan da gwamnatin jihar ta dauka ne.
Shi dai marigayi Sarkin Mai Tangale na 15, Dakta Abu Buba-Maisheru ya rasu ne a ranar 10 ga watan Janairu, bayan ‘yar gajerun rashin lafiya da ta sameshi yana da shekara 72 a duniya. Masarautar Tangale dai na daga cikin manyan masarautu a jihar Gombe.