Yadda Gwamnatin Nijeriya Ta Tsara Zuba Jarin Naira Biliyan 20 Akan Hako Ma’adanai – Minista

Ministan ma’aikatar Ma’adanai Mista Ayo Fayemi ya sanar da cewar gwamnatin tarayya ta tsara zata zuba jarin naira biliyan ashirn don hako da ma’adanai a kasar nan.

Mista Fayemi ya sanar da hakan ne a  ranar Alhamis data gabata a birnin tarayyar Abuja a yayin da yake gabatar da aiki da ake kira (MinDiber) wanda za’a bayar da tallafi ta hanyar  raba kafa akan tattalin arzikin kasa ta hanyar yin  hadaka da Bankin Duniya.

Minstan ya ce, zuba jarin zai taimaka wajen samar da gamsassun bayanai wajen aikin na hakar ma’adanai a kasar nan.

Mista Fayemi yaci gabada cewa ma’aikatarsa ta karbi binciken da aka gudanar na karshe wanda aka gudanar a shekarun da suka shige, wanda kuma ba gwamnatin tarayya bace ta biya ba.

Da yake tsokaci akan akain na (MinDiber) Feyemi ya jinjinwa Bankin na Duniya akan yin amfani da tsarin da zai taimaka wajen zamar da tsare-tsare akan aikin, sabanin yadda masu bayar da tallafi suka saba yi a baya.

Ya ce, “ba’a saba da hakan ba kuma abinda aka sheda mana shi ne, masu bayarda tallafin sai abinda suke so ne kawai, ba wai abida masu karba suke da matukar bukata ba, amma ina son in baku tabbacin cewar tallafin na tawagar Bankin na Duniya, ya nuna cewar ba’a hakan ne aka

saba yi a baya ba.”

Ya bayyana cewar,“ Bankin na Duniya ya ya saurare mu ya kuma yi tsari akan  shiga cikin wannan aikin kuma bankin, ya nuna mana hanya da kuma sanar damu kwarewar sa da sauran kasashe.”

A cewar sa, “dukkan bayanan da suke kunshe a cikin kundin na shirye-shiyen, akan wannan fannin mune muka kirkiro dashi a saboda haka baza mu zargi bankin ba in munci nasara ko kuma muka gaza ba akan aikin ba, kuma dole mu zargi kawunan mu akan sakamakon da aka samu.”

Mista Fayemi ya ce, makasudin aikin shi ne, don a samar da harkar ma’adanai wacce zata zamo ta daya a duniya da kuma tabbatar da an habaka harkar a cikin gida harda kuma wanda za’a dinga fitar dasu zuwa kasuwannin dake kasashen duniya.

Ministan ya ce,“mun tsara samun cin nasara akan wannan ta hanyar mayar da hankali akan ma’adanan kasa da dangogin su don sarrafa su zuwa kashi uku.”

Ya ce,” kashi na farko shi ne yadda za’a sake gina kasuwar ta ma’adanai don tabbatar da an dawo da martabar hakar ma’adanai da kuma shawo kan masu amfani da ma’adanai da suke fitar dasu zuwa kasuwannin kasashen duniya.

Ya kara da cewar,“ a lokacin gudanar da kashin na farko, Nijeriya za ta  kara neman da a fadada yin amfani da ma’adanan mu kamar Kwal, kuma a wannan kashin zai kai tsawon shekaru biyu ko uku masu zuwa.”

Fayemi ya ce,“ a kashi na biyu kuwa na aikin, zai fuskanta ne akan fadada ma’adanan mu na cikin gida da kuma tabbatar ana sarrafa ma’adanan (ore) a masana’antun mu.”

A cewar sa, da jimawa, abinda muke dashi akan abinda ya shafi albarkantu, ana daukar tsurar sune kuma akan abinda muka yanke shawara akai shi ne, zasu fi yin amfani ga masana’antu masu zaman kansu na cikin gida da kuma  a bangaren gwamnati a dangane da ma’adanan mu na (ore) don a sarrafa su a gida Nijeriya yadda zasu kara daraja kafin a fitar dasu zuwa kasuwannin dake kasashen duniya, in harma za’a fitar dasu din.”

Ministan ya yi nuni da cewa, “a wasu lokutan ma’adanan ana samun su da dama don tattara abinda muka samar, amma a wasu lokutan, zamu iya bayar da kwarin gwiwa wajen fitar da ma’adanan.”

Akan kashi na uku kuwa, ministan ya ce,“ a wannan zasu nemi dawo da Nijeriya a cikin hada-hadar kasuwar ta (ore) a duniya da  kuma yadda za’a samar ta farashin da ya yi daidai dana  kasuwannin duniya kuma muna san ran wannan zai hada da samar da kayan domin ma’sana’antar ta ma’adainai, kusan daidai take da masana’antar mai.

Ya kara da cewa, daidai take da farashin masana’antu da kuma farashin.

Ya ce, “ayayin da muke dakon dawowar martabar kasuwar ta ma’adanan, munyi imani da cewar, zamu yin amfani da lokacin don yin shiri akan hanyar sadarwa ta duniya.”

Fayemi ya ce, wannan kokarin a bisa ka’ida yake  a bisa tsarin mu na iyakar kasa da kasa don  farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Ya godewa Bankin na Duniya akan tallafin wanda yazo yazo akan gaba, inda ya kuma ya sanar da cewar, a  ganawar da ya yi da takwarorin kasar jamhuriyar Nijar a ranar Lititinin din data gabata don a haka ma’aikatar ta hanyar yin hadaka da kasashen dake nahiyar Afrika.

 

Exit mobile version