Yadda Hauhawar Farashin Kayan Abinci Ya Jefa Ýan Nijeriya Halin Tsaka-mai-wuya

Farashin

Tsadar rayuwa na dada karuwa wa ‘yan Najeriya sakamakon hauhawar farashin kayan abinci da sauran abubuwan yau da kullum. Matsalar tsaro, rage albashi da korar maáikata ya jefa mutane da dama cikin mawuyacin hali, kamar yadda su ka bayyana a cikin wannan rahoton rahoton.    

Matsalar tsaro ce da korar aiki a Kaduna

Kayan abinci da hatsi na dada hauhawa a kasuwannin Kaduna ga kuma rashin abin hannu ga mutane. Wasu manoman sun alakanta hauhawar farashin kayan abincin da karin kudin kayan noma irin su taki, magani, iri da sauran su.

A bayanin wasu manoman kuwa,  matsalar rashin tsaro ce ke babban dalilin hauhawar farashin, wanda yasa mafiya yawan manoma gujewa zuwa gonakinsu saboda tsoron rasa ransu a hannun ýan bindiga ko kuma yin garkuwa da su.

A zanatawa da ýan kasuwar Bakin Dogo da ke Kaduna da wakilinmu ya yi yayin ziyara, sun shaida masa karin farashi na kayayyaki, kamar wake, shinakafa da masara da karin kudi mai yawa, sabanin watannain baya.

Ibrahim Birnin Yero, ya nemi gwamnati da ta shawo kan matsalar tsaro domin samun ci gaba da noma domin samun saukin farashi, wanda ya ce yanzu haka ba ya iya zuwa gonarsa saboda matsalar tsaro.

A Filato an koka da karin farashi

Auwalu Yatata, dan kasuwa a Anguwan Rogo, Jos, ya koka kan hauhawar farashi, inda ya ce ba a taba tsammanin abubuwa za su kai haka ba.

Buhun suga, wanda muka saba saye 12,000 a baya, yanzu ya koma 19,500. Haka ma fulawa, daga 10,000 ta koma 16,000. Haka abin ya ke a sauran kayayyaki, kuma a koína, in ji shi

Matsalar tsaro a Neja

A Naija ma haka lamarin yake, duk da albarkatun kasa da jihar ta shahara da shi, a nan din ma, farashin kayayyaki ya yi tashin gwabron zabi.

Bincikenmu ya nuna cewa, hauhawar farashin na da alaka da matsalar tsaron da ke addabar jihar tsawon shekaru, kamar yadda wasu ýa kasuwa su ka bayyana.

Mutane da dama ba sa iya zuwa gona saboda ýan bindiga sun tashe su, kuma ga barazanar masu garkuwa, in ji Umar Abdullahi dan kasuwa a Minna.

Malamar makaranta, Madam Mercy Deola, ta koka da rkarancin albashin da ake fama da shi, wanda albashin ba za ya iya ciyar da mutum ba, a cewar ta.

Matan aure sun koka a Kano da Katsina

Duk da hauhawar kayan abinci, ba a samun karin kudin cefane da sauran ayukkan gida  ba daga mazajensu, a cewar wasu matan auren a jihohin Kano da Katsina.

Hajiya Hauwa Sani, matar wani dan maáikacin gwamnati, ta koka da cewa, “rashin samun karin albashin mai gidana, ya sa ba zai iya karawa kan kudin da yake badawa na cefane ba, hakan ya sa kudin ba za su iya sayen kayayyaki ba a yanzu saboda tashin farashi”

Wata matar, a Kano, Hajiya Amina, ta koka kan farashin kayan itace, inda ta ce, yanzu babu kanakana ko abarbar 50, sabanin a baya. Haka ma ta koka kan sauran kayan abinci kamar wake, shinkafa da sauran su.

Haka lamarin yake a Katsina

Malama Naímatu Abdullahi, ta ce alámarin sai kara tsanani yake, ind kullum kayan abinci kara tashi su ke.  Hatta abin 20, ya kara kudi zuwa 50 mafi ban tsoro kuma shi ne, babu alamar yaushe abubuwa za su daidaita, in ji ta.

Wani mai sanaár acaba (mashin), wanda ya ya dogara da ita domin ciyar da iyalinsa, ya ce masara ce ya saba saye don ciyar da iyalinsa, amman yanzu ta kara kudi wanda hakan ya kara wa rayuwa tsanani.

Yakubu Muhammad, dan kasuwa a babbar kasuwar Katsina, ya ce abubuwa da dama ne su ka haddasa hauhawar farashin, inda ya ce wasu daga yanayin rani ne wanda hakan ke sa tsadar kaya koyaushe, sai kuma matsalar tsaro.

Kasuwannin da muka saba dauko kaya, kamar kasuwar Dandume, Batsari, da Kankara, ýan bindiga sun addabi garuruwan.

“A kwanan baya, masu garkuwa sun yi garkuwa da  ýan kasuwarmu yayin da su ke kan hanyar tafiya dauko kaya, sai da muka hada kusan miliyan 30 kudin fansa,”in ji shi.

 A Benuwai mazauna sun koka

Mazauna sun koka da hauhawar farashi, wanda hakan yasa dayawa rashin iya ci gaba da rayuwa kamar yadd aka saba.

Rose Oche cewa ya yi,”Gaskiyar magana ni bansan ma ya nake ina rayuwa ba, mamaki ma nake da har na iya  kawowa haka. Komai ya kara farshi fiye da aljihun talakka. Komai ya kara kudi in banda albashi,”in ji shi.

Da take zantawa da wkailinmu kan yanayin, Madam Biola Adeyemi, ta ce, talakawa ne su ka fi cutuwa da karin hauhawar farashin kayan abinci.

“Idan gari da ake gani da sauki wanda talakka ke iya siya yanzu ya zama abinda ya zama, to lalle akwai babbar matsala a kasar nan,”in ji ta

Ta ci gaba da cewa, “ a da, sau 3 a ke abinci kullum a gidaje, ba a ma tunanin yiyuwar rashin yin hakan, amman yanzu ba haka lamarin yake ba, gidaje da dama ba sa wuce sau 1,” in ji ta

Madam Basoyo Sulaiman, ta koka ita ma, inda ta ce, dayawan gidaje na mutuwar mummuke saboda rashin iya sayen abinci, a cewar ta, kudi sun rage kadari saboda tsadar kayayyaki.

 

Bauchi ma haka lamarin yake

Wani mai aikin sayar da jarida a Bauchi, Babayo Adamu, ya ce shi ida iyalina na cikin mawuwayacin hali sakamakon yanayin da ake ciki.

Ya bayyana cewar, ya saba sayen mudun shinkafa da masara 20, 30, amman yanzu ba haka lamarin yake ba, baya wuce sayen iya mudu 5.

Wani dan kasuwa a kasuwar Wunti, Sabiú Aliyu, ya ce karin farashin ya taba cinikinsu.

“Ba ma farin ciki da karin farashin kayayyaki, sanadiyar haka cinikinmu ya ragu, za ka iya yini ba tare da ka samu ciniki ba, kuma kana bukatar ka samu ka sayar domin ciyar da iyalanka,”in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Idan ba a dauki mataki ba, to lalle akwai yiuwar dakushewar ýan kasuwa masu karamin karfi.”

A Abuja, biyu ce ta hadu

Dai daga cikin matsalolin da ýan kasuwa ke fuskanta a Abuja shi ne, karin kudin abin hawa. Sun koka da cewar, karin kudin safarar kayayyaki ya sa dole sai sun kara kudin farashi don gudun faduwa.

Mazauna Abuja da dama na kokawa kan  farashin kayan abinci da ya yi tahsin gwabron zabi a garin, wanda hakan ya sa wasu sai dai kallo.

Wani dan mai sanaár nama a Kasuwar Wuse da ke Abuja, ya ce, kwastomomi na yawan korafi kan karin kudin kilon nama, wanda ya koma 2,500 a maimakon 1,500  da yake a baya.

 

Iliyasu mai sayar da kaji a kasuwar Utako kuwa, cewa ya  yi, yana kokarin ganin ya daidaita da kwastomomi, kodayake kudin kaji ya hauhawa, amman dai ya kan samu daidai da kudin mai saye ya ba kwastoma domin gudun yawan na-ce ka-ce, in ji shi

Exit mobile version