Wakilinmu" />

Yadda Hon. Bobboji Ya Taka Rawar Gani A Jalingo Kan Ilimi – Nazari

A rayuwar duniya ta wannan lokaci, babu wani abu da a ke bukatar dan Adam ya samu kamar ilimi na zamani da kuma na addini. Wannan ya sa kasashen da suka ci gaba saka dauki bangaren ilimi da muhimancin gaske ta yadda su ke ba shi kyakyawar kulawar da ta dace, domin kuwa ana samun al’umma, masu ci gaba ta hanyar bunkasar ilimin su ta kowanne bangare. Domin masana sun ce babu wata al’umma da za ta ci gaba tana cikin duhun jahilci, don haka ne duk wata Gwamnati walau ta tarayya ko ta karamar Hukuma da ta ke son cigaban jama’ar, to dole ne ta tashi tsaye wajen samar da hanyoyin da jama’ar ta za su samu ilimi domin su zama a sahun wadanda suka ci gaba.

Shugaban karamar Hukumar Jalingo da ke jihar Taraba Alhaji Abdulnaseer Bobboji yana. Daya daga cikin shugabannin da suka tashi tsaye wajen nemar wa jama’ar su hanyoyin da za su samu ilimi da kuma gogewa a dukkan al’amuran rayuwa na yau da kullum.
Tun bayan zuwan sa shugabancin karamar Hukumar Jalingo a karo na farko ya samar da hanyoyin bunkasa ilimi tun daga tushe da kuma yadda abin zai Dore ba tare da samun tsaiko ba idan an samu tsawon lokaci. Wannan ya sa ko da ya dawo a karo na biyu sai ka ya Kara inganta hanyoyin da kuma fadada su.
Babbar hanyar da ya bi don samar da ingantaccen ilimi, shi ne yadda ya mayar da hankali wajen samar da kayan karatu a makarantun firamare da makarantun Islamiyya na karamar Hukumar Jalingo, wannan ya sa duk wata makaranta walau ta boko ko ta Islamiyya da ta ke karamar Hukumar Jalingo ta samu kayan aiki na koyarwa. Sannan su kan su Daliban sun samu kayan tallafi na littattafai da sauran su.
Baya ga haka, ya samar da tsarin horas da Matasa a kan hanyoyin dogaro da kai wanda su ma Matasa a wannan bangaren da daman su sun samu aikin yi domin su dogara da kan su, kuma ba an tsaya ga horas da su ba ne kai ba, domin duk matasan da aka horas a duk wani fanni na sana’a to sai da aka raba musu kayan da za su je su rike kan su da shi a kan sana’ar da suka koya.
Ta bangaren Matasa masu neman ci gaba kuwa a Fannin karatun su. Da dama sun samu rabon daukar nauyin su da Karamar Hukumar ta yi a karkashin shugabancin Alhaji Abdulnaseer Bobboji, in da suka samu damar ci gaba da karatu a manyan makarantu na gaba da Sakandare, don haka kullum Matasa su ke yabon sa tare da yi masa kirari da Jagoran ci gaban Matasa.
Duk da cewar karamar Hukumar Jalingo, ta yi fice a fagen ilimin boko tsawon shekaru masu yawa da suka gabata, amma ana ganin a wannan lokacin ta fi samun ci gaba mai yawa idan aka kwatanta da shekarun baya, wannan kuma kamar yadda jama’a su ke fada ya samo asali ne daga tsayuwar daka da Alhaji Abdulnaseer Bobboji ya yi na ganin Matasa sun samu kyakyawan tsarin ilimi wanda zai sa su zama sun rike kima da martabar da karamar Hukumar ta ke da shi a shekaru masu zuwa.
Wani tsari da Shugaban karamar Hukumar Jalingo Alhaji Abdulnaseer Bobboji ya samar da shi domin Kara wa Matasa karfin gwiwar yin karatu shi ne nuna musu da na gaba a ke ganin zurfin ruwa, kuma magabata su ne abin koyi. Wannan ta sa aka shirya wani taro na musamman in da aka karrama manyan ‘yan boko ‘ yan asalin karamar Hukumar Jalingo da suka yi fice a duniya, kumu suka bayar da gudummawar da za a ci gaba da amfanar ta tsawon shekaru masu zuwa.
A karshen shekarar da ta gabata ta 2020, wato 31 ga watan Disamba an shirya wani babban taro in da aka karrama manyan masu ilimi da kuma basu tasowa na karamar Hukumar, wadanda suke da mataki na Kololuwa wato Farfesoshi da masu takin Dakta, da masu matakin kammala Digiri na farko, wanda a taron an karrama mutane sama da 80 ‘yan asalin karamar Hukumar Jalingo. Cikin wadanda aka karrama har da wadanda Allah ya karbi ran su, amma kuma har yanzu ana amfana da ilimin su a fannin ci gaban rayuwa, cikin su akwai, Farfesa Abubakar Sa’ ad. Farfesa Ahmad Umar Jalingo, da Farfesa Musa Kalamullah Omar.
Sai kuma wadanda su ke da rai kuma suke ci gaba da bayar da gudummawar da su ma aka karrama su, kamar Farfesa Tukur Baba, Farfesa Abdulmumini Sa’ad, Farfesa Abbas Bashir, Farfesa Noku Michael, Farfesa Inuwa Muhammad da Farfesa Abubakar Jika.
A lokacin da ya ke jawabi a wajen taron, shugaban karamar Hukumar Jalingo Alhaji Abdulnaseer Bobboji ya yi kira ga Matasa da wandanan mutane da su zama abin koyi a gare su domin su ma su zamo abin alfahari a nan gaba, domin kuwa a cewar “Mutum yana zama abin alfahari ne ta hanyar samun Inganci a rayuwar sa, kuma Inganci ba zai samu ba sai da ilimi, don haka muke yin kokari don ganin jama’ar mu sun samu ilimi don su zama abin koyi, wanda kuma za su yi alfahari da abin da muka dora su a kai nan gaba.
Daga karshe ya ja hankalin Matasa da su tsaya a kan hanyar neman ilimi domin samar da ci gaba a karamar Hukumar Jalingo da Jihar Taraba, da ma kasa baki daya.
Shi ma da ya ke na sa jawabin a wajen. Galadiman Muri kuma Hakimin Jalingo, Alhaji Tukur Abba Tukur, ya yi fatan kada taron ya tashi haka ba tare da an dauki darasin da ya ke cikin sa ba. Don haka ya ke cewa”mu za mu samar wa kan mu ci gaba ba wani ba ne zai zo ya samar mana, kuma mu za mu samar wa kan mu zaman Lafiya ba wani ba ne zai zo ya samar mana, don haka mu za mu taru domin mu sama wa kan mu mafita, don haka mu dauki wannan taro da muhimanci, domin mu samar wa kan mu ci gaba mai dorewa.
Jama’a da dama da suka halarci wajen taron, sun nuna jin dadin su da yadda taron ya gudana kuma sun yi fatan alheri, da godiya ga Shugaban karamar Hukumar ta Jalingo Alhaji Abdulnaseer Bobboji saboda hanyoyin da ya ke bi na samar wa karamar Hukumar ci gaba.

Exit mobile version