Connect with us

NAZARI

Yadda Iyaye Za Su Yi Riga-kafin Alkaba’in Fyade

Published

on

Kodayake ba ni da shekaru masu yawa a duniya zuwa yanzu, amma tun ban iya bambanta abubuwa ba nake jin batun fyade, wanda hakan yake alamta cewa wannan mummunar dabi’a ta jima ana aikata ta a cikin al’umma. Na kawo misali da shekaruna ne saboda watakila idan aka ce wa wani ya kawo shekarun da aka fara aikata wannan mummunar ta’asa a duniya, zai yi wuya a samu wanda zai bayyana alkaluman daidai.

A ‘yan shekarun da suka gabata a zamanin mulkin tsohon shugaba Jonathan, kungiyoyin fararen hula da na mata da sauran masu ruwa da tsaki sun yi hobbasar ganin an tabbatar da takamaimiyar doka da za ta tsananta hukunci a kan masu aikata fyade. Wannan ta sa majalisun dokokinmu na tarayya a Nijeriya da bangaren zartasawa suka amince da hukuncin daurin shekara 15 a gidan gyaran hali da tara (idan ta kama) ga duk wanda aka same shi da laifin aikata fyade.
Kamar abin ya yi sauki a lokacin, sai dai kash! Ana murna bako ya tafi, ashe mugun yana nan labe a bayan gari. Ma`ana masu aikata ta’asar labo suka yi, ba dainawa ba.
Daga farkon makon da ya gabata zuwa lokacin da nake wannan rubutun, batun karuwar yawaitar fyade ya tayar da hankulan al’umma matuka a kasar nan. Wadanda aka sani suka fito fili sun hada da fyaden da aka yi wa wata dalibar Jami’ar Jihar Benin Vera Omozuwa a Edo, Babban Birnin Jihar Benin da wanda aka yi wa wata dalibar Kwaleji a Jihar Oyo Barakat Bello, wadanda dukkansu suka riga-mu-gidan-gaskiya a sanadiyyar hakan. Sai kuma fyaden da ake zargin wasu karti su 11 da aikata wa wata yarinya ‘yar shekara 12 a yankin Limawa da ke Jihar Jigawa. Kwatsam ba a kai ga kammala jimami da alhinin wannan aika-aika ba, sai kuma ga labarin wasu karti su hudu rufe da fuska da suka fakaici idon iyayen wata yarinya ita ma ‘yar shekara 12 da haihuwa a Legas; suka haura ta katanga suka yi mata fyade. Alkaba’in fyaden bai tsaya nan ba, a Jihar Ogun ranar Alhamis da ta gabata, ‘yan sanda sun tuhumi wani saurayi dan shekara 25 da yi wa wata tsohuwa mai shekara 70 da haihuwa fyade. Wadannan fa duk sun auku ne a tsakanin ‘yan makwanni kurum. Kuma kamar yadda na fada a baya, su ne wadanda aka sani, sauran wadanda ba a sani ba, ba a fito da su fili ba, Allah kadai ya san adadinsu.
karuwar yawaitar fyaden, manuniya ce da ke kiran gudunmawar duk wani mutum nagari a cikin al’umma domin ganin an dakile lamarin. Na tabbata babu wani mahaluki mai digon hankali da zai so a ce an yi wa ‘yarsa ko uwarsa ko ‘yar’uwarsa wannan ta’asa, kenan yakin na kowa da kowa ne. Ba ina nufin sai mutum ya shiga kafafen yada labarai ya yi magana ko ya shiga zanga-zanga ko zuwa ofishin gwamnati don gabatar da kudiri; shi ne kawai ya bayar da gudunmawa ba, a’a, nuna kyamar abin a zuci da nunawa a fili walau mutum shi kadai ko a bainar jama’a duk suna daga cikin gudunmawa.
Bayan haka, ina ganin duk matakin da ya kamata a dauka na yaki da fyade wajen hukunta masu aikatawa ba zai kai daukar matakin riga-kafin aukuwar lamarin muhimmanci ba. Kasancewar masu zancen hikima kan ce “riga-kafi ya fi magani”, idan za a rika kiyaye wani abu kafin aukuwarsa, ya fi duk wani hukunci da za a yi wa mai laifi bayan abin ya faru.
Domin matakin riga-kafi, yana da kyau iyayen yara su ilmantu da duk wani abu da ya shafi fyade. Idan ba ka da masaniya a kan abu, ba zai yiwu ka iya samar masa da riga-kafi ko magani ba.
Da farko, iyaye su san shaidanun alamomin da ka iya jefa ‘ya’yansu cikin fyade. Idan suka ga wani ya fara yi wa ‘ya’yansu wasa da al’aura su san cewa wannan shaidani ne. Su lura da kyau a wannan gabar, ba sai mutumin ya fito fili ya fara taba al’aurar ba, zai iya wasa da al’aurar ta hanyar rungumar yaran fiye da kima ko dora su a cinya ko yi musu wasa da baki a ciki da sauransu. Sannan iyaye su lura da wadanda suke koya wa yaransu kallon finafinan batsa. Mutum zai zo da sunan karrama yara sai ya rika ba su wayarsa suna kallo, lallai iyaye su kula da wane irin bidiyo ne mutumin nan yake nuna wa yaransu. Idan ma ana gudun aukuwar wani abu, kwatakwata a hana yaran nuna sha’awar taba wayar kowa in ba na iyaye ba kuma komai kusancin mutum da su. Saboda akwai nazarin da ya nuna cewa mutanen da aka sani a dangi ko makusantan yara da iyayensu ne suka fi lalata da yaran da kashi 95 a cikin dari.
Iyaye su fahimci cewa, galibin masu yi wa yara fyade a kusa da su suke, wasu abokan zaman haya ne, wasu ma daga cikin dangi, wasu malaman da ke wa yara darasi a gida ne, ko makota. Sai abokan da suke tare da su a makaranta, da wurin kwana, da abokan iyayensu, direbobinsu, malamansu na makaranta, malaman addini marasa tsoron Allah (an sha kamawa ba daya ba; ba biyu ba), da sauran makusanta, ga su nan birjik!

Wakazalika, ya dace iyaye su yi la’akari da wasu abubuwa da suke aikatawa da ke jefa yara cikin sha’awar saduwa wadda ko da an yi musu fyade ba za su iya bayyanawa ba saboda abubuwan da suke gani daga iyayen. Da farko, rashin ilmantar da yara a kan riga-kafin fyade, rashin kula da abin da iyaye suke kallo na bidiyo tare da iyalansu, rashin tsawatarwa a kan sanya tufafin da ba su dace ba, da barin yara su kadai a gida ba tare da kulawar wani ko wata mai amana ba da kuma shafe tsawon lokaci ba tare da yaran ba (ga masu tafiye-tafiye masu nisa).
Yana da kyau iyaye su san cewa, za a iya yiwa yaransu fyade hatta a kan gadonsu (iyayen), a makaranta kamar cikin aji ko bandaki, dakunan kwanan dalibai, wurin shargalle (parties), a dakunan kwanan yaran na gida, wuraren da babu mutane sosai a ciki da kuma wani lokaci da za a iya zuwa a dauke hankalin iyayen. Masu aikata fyade, ‘yar kankanuwar dama suke jira su samu, don haka cikin minti biyar za su iya lalata wa yarinya rayuwarta.
Yana daga cikin dabarun da masu fyade suke amfani da su wajen yaudarar yaran da za su lalata, sukan sa gasa a tsakaninsu, misali su ce idan kin iya yi min kaza zan ba ki kaza, ko bari in yi miki kaza in ga ko za ki iya dauriya? Ko kuma su rika nuna musu sha’awar saduwa a fili ba tare da sun taba koda hannun yarinyar ba har sai ta kawo kanta-da-kanta. Saboda haka yana da kyau, iyaye su zama abokan da yaransu suka fi amincewa da su ta hanyar janyo su a jiki, da nuna musu tausayi da jinkai da kuma kauna mai tsafta.
Yana da matukar muhimmanci iyaye su gane take-taken wadanda suke neman yi wa yaransu fyade. Su lura da kyau, za su ga masu muguwar aniyar suna son zama ko kasancewa a duk inda yaran suke. Yara kan firgita ko su ji tsoro ko nuna dari-dari da zarar sun ga mai neman yi musu fyade. Saboda sharri, galibin masu fyade ba su kin amincewa da karbar hidimar yarinya su yi mata kuma suna iya tsangwamar yarinyar musamman idan suka kasa shawo kanta ta yarda da abin da suke so. Iyaye su lura da kyau, da zarar sun ga wadannan alamomin su tsananta bincike domin rabe zare da abawa.
Haka nan yana da muhimmanci iyaye su san cewa ba baki ko dangi na nesa ne kawai za su iya lalata da yaransu ba, hatta a tsakanin yaran nasu akwai yiwuwar hakan ta faru, don haka a lokacin da yara suka fara girma musamman daga shekara 6 zuwa sama (lokacin da sha’awa za ta fara bulla a al’aura), a rika nuna musu haramcin wasa da al’aura, idan da hali a raba musu daki ko gadon kwanciya. Kuma lallai iyaye su kula da wurin da suke mu’amalar aure ta saduwa a tsakaninsu, domin yaran za su iya kwaikwayon abin da suka ga suna yi. Na taba jin cewa, an kama wasu yara ‘yan biyu Hassan da Hussaina suna lalata a tsakaninsu, da aka tambaye su? Suka ce “haka muke ganin Baba da Mama suna yi”.
Har ila yau, saboda tsoratarwar da masu fyade kan yi wa yara cewa idan sun fada abin da suka yi da su za su kashe su, ko su ce mama ko baban zai mutu, yana da kyau iyaye su koya wa yaransu hanyoyin tsira daga masu fyade. Su sanar da yaran yadda za su yi ihu ko su gudu ko kuma su kai rahoton abin da aka yi musu.
Idan kuma (Allah ya kiyaye) masu fyade sun cimma mummunan burinsu a kan ‘yarku, alamomin da za ku gane hakan sun hada da: yarinya za ta rika ware kanta daga cikin yara, za ta rika nuna damuwa ko firgici, za ku ga tafiyarta ta sauya; tana yi da kyar-da-kyar ko kuma a ga ba ta son yin mu’amala da mutane (har da na gida). Da zarar iyaye sun yi la’akari da wadannan abubuwan, su yi gaggawan daukar mataki.
Sannan hakkin iyaye ne su koya wa ‘ya’yansu sa sutura ta mutunci, da nuna musu abubuwan da ake so a kiyaye na sirri (al’aurarsu). Su dabi’antar da su ladubban shige da fice a gida, kuma a kiyaye gwamutsa su ana musu wanka a tare. Duk wadannan abubuwa na riga-kafi da na ankarar da iyaye a kai, ba a kan ‘ya’ya mata ba ne kawai har da yara maza, saboda kowa ya san cewa su ma yara mazan ba su tsira ba daga alkaba’in ‘yan luwadi.
Iyaye mu dage wajen kula da yaranmu da kuma addu’a, domin akwai nazarin da ya tabbatar da cewa akalla ana samun yarinya daya a cikin hudu da ake lalata ta tun kafin ta kai shekara 18, ta bangaren yara maza kuma ana samun yaro daya a cikin yara 10 da ake lalata da shi kafin shekara 18.
Advertisement

labarai