Abubakar Abba" />

Yadda Jami’an Kwastam Suka Halaka Mai Kai Wa Masu Fasa-Kwauri Tsegumi

Wasu Jami’an hukumar kwastam ta kasa sun hallaka wani mutum da ake zargi mai kaiwa masu yin fasa kauri rahoto ne a dake a cikin jihar Jigawa.

Marigayin mai suna Tasiu Muhammad dan shekaru 22, nazuni ne a Unguwar Gawo, mai nisan kilomita biyar daga garin Babura a jihar Jigawa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, Bala Senchi, ya tabbatar da faruwar lamarin a yayin da yake gana wa da manema labarai, inda ya ce, babu hannun rundunar ‘yan sanda a aikin da ya yi sanadiyar kashe Muhammad.

Mazauna yankin sun ce Marigayin ya dade a cikin jerin sunayen mutanen da jami’an kwastam ke nema bisa zarginsa da bayar da bayanai ga masu shigo da shinkafar waje ta haramtacciyar hanya.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta saboda dalilan tsaro ta bayyana cewa jami’an Kwastam sun harbe mutumin a yayin da yake kokarin gudu wa a lokacin da suka zo kama shi, inda majiyar ta kara da cewa, babu makami a tare da mutumin yayin da yake kokarin gudu wa.

Kakakin rundunar Kwastam na ofishin Kano da Jigawa, Dan-Baba, ya ce ba zai iya yin magana ba a lokacin da aka tuntube shi, saboda yana cikin wani taro ne.

Karamar hukumar Babura ta hada iyaka da Jamhuriyar Nijar, kuma masu safarar shinkafa na amfani da hanyoyin cikin jeji wajen shigo da haramtattun kaya cikin kasar nan.

In za’a iya tunawa, a ranar Litinin, sai da shugaban hukumar kwastam, Kanal Hameed Ali nai ritaya , ya sanar da cewa sun rufe iyakokin Nijeriya ta kasa, watau ba shiga ko fitar da wani kaya daga cikin kasar nan.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taro da manema labarai da ya gudanar tare da takwaransa, shugaban hukumar hana shige da fice ta kasa Muhammad Babandede, a babban birnin tarayyar Abuja.

Exit mobile version