Connect with us

Ka San Jikinka

Yadda Jikin Mutum Ke Aiki (5)

Published

on

’Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa, da ke zayyano muku bayanai game da duniyar jikin dan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu; ku san yadda jikinku ke aiki.

To har yanzu dai ina kan bayani game da yadda jikin dan adam ke aiki, inda a makon da ya gabata, na kawo bayani game da yadda ake daidaita dumi a jikin dan adam. Na tsaya ne a inda nake cewa: Shi jikin dan adam kamar wani ‘inji’ ne wanda ke motsawa, a ke yi masa sabis, garanbawul, da juye kamar yadda a ke yi wa abin hawa irinsu babur da Mota. Idan kukayi nazari, za ku gasgata batu na saboda idan kun lura da kyau, duk wani inji da ya ke aiki, ya kan dauki zafi bayan ya dauki wani lokaci ya na aiki. To, tun da jikin dan adam kullum cikin aiki ya ke, matukar ya na da rai, ashe ba za a raba shi da yin zafi ba. To amma wannan zafin ya na da daidaitaccen ma’auni kamar yadda na fada, wanda ya tsaya a 37 a ma’aunin Celsius ko kum 98.6 a ma’aunin Fahrenheit.

Bisa tsarin wannan siga (mai dankwafe zarcewar sauyin da ya samu a jiki) duk lokacin da dumin jiki yayi kasa da 37, to za a daga darajar dumin jikin har sai ta koma 37 din. Haka kuma idan sama yayi da 37,to za a dinga rage dumin jiki har sai ya dawo kan daidaitaccen ma’auninsa na 37.

Zafi ko dumin jikin dan adam kan yi kasa da 37 a lokacin da mutum ya tsinci kansa a muhallin da ya ke da sanyi.

Da zarar ya yi kasa da 37 to sai cibiyar da ke daidaita dumamar jiki da ke zaune a wata halitta da ake kira “hypothalamus” ta fara shirya gabbai masu kula da dumama jiki da kuma taskance zafinsa. Wannan cibiya mai daidaita dumin jiki wato “hypothalamus”, a cikin kwakwalwatake. Bayan daidaita dumin jiki, ta na kula da cin abinci, shan ruwa, da sha’awar jima’i.

A gefe guda kuwa, gabban da ke kula da dumamar jikin su ne fata, tsokar nama, da kuma jijiyoyin jini wato “blood bessels”. A nan na tsaya yanzu kuma zan dora.

Za a umarci jijiyoyin jinin da ke karkashin fata da su tsuke, domin hakan zai rage yawan jinin da ke gudana a cikinsu. To sauran jinin kuma sai a tura shi cikin hanyoyin jini da ke can kasan fata da kuma wadanda su ke baibaye da tsokar nama.

Hikimar a nan ita ce; bayan sinadarai masu tarin yawa da jini ke dauke da su yana zagayawa a cikin hanyoyinsa ko jijiyoyinsa, akwai kuma rawar da ya ke takawa wajen daidaita dumin jiki. Jini ya na dauko dumin jiki wanda ya samo asali daga ayyukan kwayoyin halitta yayin mommotsawarsu lokacin gudanar da ayyuka irinsu: narkar da abinci, magana, tafiya, motsa jiki, hada sinadarai, da sauransu.

Yayin da wannan jini mai dumi ya biyo hanyoyin jinin da ke karkashin fata, ya kan sadaukar da wannan dumi da ya ke dauke da shi, saboda haka sai dumin ya fice daga jijiyoyin jini ya bi ta kafofin gashi da sauran kafofin da ke tsakanin kwayoyin halittar fata ya bar jikin dan adam.

Idan kuwa a ka rage yawan jinin da ke gudana a cikin jijiyoyin jinin da ke karkashin fata, to an rage yawan dumin da ke fita daga jikin mutum kenan.

Abu na gaba shi ne za a umarci tsoka da ta fara mommotsawa da karkadawa domin dumi ya samu. Wannan mommotswar fata shi muke kira da ‘rawar dari.’ Kar ku manta na ce jikin mutum kamar inji ya ke; motsin da inji ke yi, shi ya ke samar da zafi. To haka anan ma, motsawar tsokar cikin sauri (rawar dari) za ta kara gejin dumamar jiki. Bin wadannan matakai guda biyu zai daga darajar dumin da ke jiki a daidai wannan lokaci. Domin a cika aiki, za a yi ta umartar tsoka da jijiyoyin jini da suci gaba da aiwatar da wadannan ayyuka,har sai yanayin dumamar jiki ya daidaita,wato ya koma 37 a ma’aunin Celsius.

Daga nan kuma sai waccan cibiya da ke kula da da daidaituwar dumin jiki wato “hypothalamus” wadda ta ke a kwakwalwa ta dakatar da duk wani umarni da take bayarwa ga jijiyoyin jinin da ke karkashin fata DA kuma tsokar nama da zarar an samu daidaiton da ake so.

Idan kuwa akasin haka a ka samu, wato awon dumin jiki ya ketare daidaitaccen ma’auninsa na 37, to akan bi irin hanyoyin da na wassafa a sama, amma da akwai dan bambanci kadan.

Zafin jiki, ko yanayin dumin jiki kan yi sama da 37 a lokacin da dan adam ya tsinci kansa ko kanta a muhalli mai zafi. Idan hakan ta faru, cibiyar daidaita dumamar jiki wato “hypothalamus” za ta shirya gabbai masu kula da saita gejin zafin jikin dan adam. Sai dai a wannan lokacin, ana umartar jijiyoyin jinin da ke kasan fata da su shika, a madadin su tsuke. Sannan kuma ana umartar halittun masu feso da gumi da ake kira “sweat glands”da su fara aiki.

A maimakon jijiyoyin jinin su tsuke ( abinda ke faruwa lokacin da mutum ya ke a muhalli mai sanyi), sai su shika; ma’ana su sakata su wala domin isasshen jini wanda ya ke da dumi ya shiga cikin jijiyoyin. Shigar wannan jini ke da wuya cikin jijiyoyin jinin kasan fata, sai ya fara sadaukar da dumin da ya ke tare da shi izuwa fata, daga nan kuma izuwa duniyar da ke kewaye da mutum. Ta haka, sai zafin da ke cikin jikin dan adam ya ragu.

Daya hanyar kuwa, ita ce umarni ga halittu masu feso da gumi (sweat glands) da su fara gabatar da aikinsu. Shi yasa mutumin da ke cikin zafi za ku ga yana yin zuffa/gumi.

Akwai hikima boyayyiya ta fitar gumi yayin da dan adam ya tsinci kansa a muhallin da ya ke da zafi. Na farko: gumi yana sanya fata tayi danshi kuma ya sanyaya jiki yayin da aka tsinci kai a waje mai zafi. Na biyu, gumi ya na sanyaya fata. Da zarar dumin ya fito kuma yabi iska, sai saman fata yayin sanyi, wanda hakan kan taimaka wajen raguwar zafi ko dumamar jiki har sai ya dawo kan daidaitaccen ma’auninsa na 37. Na uku kuw, gumin yana rage yawa dattin fata ta hanyar wanke shi.

Ina fatan mun fahimci wannan misali na yadda ake daidaita dumi a jikin dan adam. Idan zafi yayi yawa a jikin dan adam za a bi wannan tsari domin sauko da darajarsa da kuma sanyaya jikin; haka kuma idan sanyi ya yi yawa a muhalli (wato dumin jiki yayi kasa), jikin mutum zai sake bin wannan tsari ingantacce domin dumama jikin.

Anan za mu gane cewa, jikin dan adam ya na dankwafe cigaban sauyin da faru, ta hanyar kawo tsari wanda ya ke kishiyar sauyin da aka samu a jikin dan adam wato “negative feedback”.

Idan da akwai wani topic da kike/kake so nayi rubutu a kai, to ku tura sakon kar-ta-kwana da sunan maudu’in zuwa lambar wayar da aka bayar,ko kuma ta adireshina na email.

‘Yan uwa, ku tara a mako mai zuwa da Yardar Sarkin halitta, domin ci gaba da kawo muku bayani akan yadda jikin dan adam ke aiki.  Kafin nan nake cewa, ku huta lafiya.

Advertisement

labarai