Yadda Karancin Unguwarzoma Ke Sanadin Mutuwar Mata Da Jarirai A Duniya

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewar miliyoyin mata da jarirai ne suke mutuwa, yayin da kuma wasu miliyoyin suma suke fama da rashin lafiya ko kuma rauni saboda ba a dauki shi al’amarin nasu da muhimmanci ba,wa ko fifita bukatun mata masu Juna biyu da kuma ba su Unguwannin zaoamr na gargajiya a basu wata horarwa ta zamani, da zata sa su, suma su kai ga  kwarewa.

Ta ce a halin da ake ciki yanzu duniya tana fama da karancin Unguwanninzoma dubu 900,000 abin wanda kuma wannan shi ne yake wakiltar kashi daya cikin uku na irin masu sana’ar tasu ake bukata a duniya.

A cewarta annobar korona ita ce ta kara ruruta shiga halin kaka nika- yi da ta’azzara su wadannan matsaloli, saboda ta batar da bukatun lafiyar na mata data jarirai.

Wannan ma wani bangare ne na muhimman al’amuran da suke kunshe cikin rahoton halin da aikin ko sana’ar Unguwarzoma suke ciki a shekara ta 2021 a duniya, na asusun kula da yawan jama’a na majalisar dinkin duniya da Hukumar lafiya ta duniya da kuma kungiyar Unguwarzomai da ya yi nazari akan kasashe 194.

Irin wannan karanci na Unguwarzoma ko kuma masu amsar haihuwa, ko kulawa da wadda zata haihu, abin ya na kawo nakasu a kokarin da ake yi wajen rage yawan mace-macen mata masu Juna biyu da kuma jarirai.

Wani rahoto da aka wallafa a mujallar Lancet ya nuna cewa idan aka inganta fannin nan da shekarar 2035 za a iya samun raguwa a yawan mace macen mata masu juna biyu da kashi 67, da kuma na jarirai da kashi 64.

Rahoton ya yi kiyasin cewar rayuka fiye da miliyan hudu za a ceto a kowacce shekara.

Sai dai kuma duk da damuwar da aka nuna a rahoton da aka fitar a shekarar 2014, wanda ya bada shawara kan yadda za a shawo kan matsalar, har yanzu matsalar ta kasance ne kamar wanda ke ginin rijiya, yana kara yin kasa, amma yana maganar ya ci gaba, tunda bayan shekaru takwas har yanzu ana inda ake tun farko..

Bugu da kari kuma rahoton na bana ya ce ci gaban da za a samu zai kai shekarar 2030, shi ma din sai sa’ar gaske za ayi wani abin  azo a gani.

Exit mobile version