Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Yadda Karuwa Ta Saci Naira Miliyan Daya Daga Asusun Saurayinta

Published

on

Masu karin magana sun ce wanda baiji bari ba yaji hoho. Wannan karin maganar ta yi dai da yadda wata karuwa ta sacewa saurayin ta dan kasuwa kudin sa har naira miliyan daya ta hanayar yin amfani da katin sa cire kudi na ATM.
Karuwar mai suna Thelma Kimberly, wadda kuma take da zma a gari Fatakwal cikin jahar Ribas ta kaiwa saurayin nata mai suna Olugbenga a gidan sa dak yankin Bictoria Island a cikin jahar Legas a ranar 17 ga watan Mayun 2018.
Wakilin muya jiwo cewar, masoyan sai da suka shiga gari suka dan shakata kafin su dawo gidan dan kasuwar don su kwana su hole.
Dan kasuwar dan shekara 45, an ruwaito cewar, sakamakon doguwar holewar da ya yi da karuwar ‘yar shekara 22 ya hadu da barci mai nauyi, inda karuwar ta yi amfani da damar ta zare katin nasa na ATM da kuma wayar sa ta tafi da gidan ka.
Ance karuwar ta fitar da kudi da tura su da kuma yin siyayya ta ha hanyar PoS don sayen kaya a babban shagon dake Lekki.
Dan kasuwar ya kai rahoton ne a ofishin ‘yan sanda na ginduma dake yankin Ikoyi, inda daga baya ‘yan sandan suka cafko Kimberly a cikin wannan watan.
Wata majiya a ofishin ‘yan sandan ta ce, kafin a cafko ta, an tura sako ga bankin da ta yi amfanui dashi wajen fitar da kudin akan cewar a sanya ido ga wanda zai fitar da kudi daga asusun dan kasuwar.
Dan kasuwar ya kuma tura naira 100,000 a cikin asusun ta na ajiya a banki da nufin ko data je kwashe kudin don a samu cafke ta, sai dai, ta yi nsarara kwashe kudin , inda har ta dauki hoton umarnin na ‘yan sanda ta kuma turawa saurayin nata ta hanayar sakon WhatsApp.
‘Yan sandan sun rubutawa bankin takardar tuhuma akan akan me yasa aka biya ta kudin duk da umarnin su.
A bayanin da matar ta rubutawa ‘yan sandan ta amsa laifin ta amma ta maido da wayar tafi da giddan ka dan kasuwar ta hanayar manajan gidan abinci din dake yankin Bictoria Island.
A cewar ta, ta hadu da dan kasuwar ne a 2016 a garin Fatakwal lokacin da ya kaiwa wani babana ta ziyara wanda abokin sa ne, inda a ranar 17 ga watan Mayu da misalin karfe 8:00 na dare ta kai masa ziyara a gidan sa dake yankin Bictoria Island ya kuma fita dani yawo ya saya mini kaya kuma yasha kwana dani.
Ta ce,’ na tafi da katin sa na ATM da wayar sa inda na kuma fitar da naira 150,000 mashin din na ATM dake Obalende dake yankin Ikeja na kuma wuce zuwa babban shago dake Lekki Phase I na kashe naira 363,000 ta hanyar yin amfani da PoS.
A cewar ta, “ na kuma tura kudi naira 250, 000 zuwa ga asusun ajiya na banki na wani da kuma baiwa wasu kudi.
KAKAKIN RINDINAR ‘YAN SANDAN JAHAR CSP CHIKE OTI YACE WADDA AKE ZARGIN ZA’A A GURFANAR DA ITA A GABAN KOTU.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: