Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Kawo Karshen Rikicin Ukraine A Siyasance
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Kawo Karshen Rikicin Ukraine A Siyasance

byCMG Hausa
2 years ago
Kasar Sin

Kasar Sin ta hannun wakilinta na musammam mai kula da harkokin Turai da Asia, Li Hui, ta yi tuntuba mai zurfi da ma musayar ra’ayi da dukkan bangarori, game da warware rikicin Ukraine a siyasance.

A ra’ayina, wannan yunkuri ya sake tabbatar da matsayin kasar Sin na son ganin tabbatuwar zaman lafiya a duniya da kaucewa goyon bayan wani bangare ko ruruta wutar rikicin.

Zuwa yanzu, an ga yadda mummunan tasirin rikicin na Ukraine ya bazu zuwa sassan duniya, tare da jefa al’ummomin da ba su ji ba, ba su gani ba cikin rudani.

Tun bayan barkewar rikicin, ake kokarin shafawa kasar Sin bakin fenti, cewa wai ta na goyon bayan wani bangare, sai dai, muradin Sin a ko da yaushe shi ne, tabbatar da wanzuwar zaman lafiya. Kuma ziyarar Li Hui kasashen Ukraine da Poland da Faransa da Jamus da Rasha da hedkwatar EU, ya tabbatar da hakan, domin ya tuntubi dukkan bangarori ba tare da ware wani ba. Adalci shi ne sauraron ra’ayin kowanne bangare tare da kokarin samar da maslahar da za ta karbu ga kowa, cikin ruwan sanyi ba tare da zubar jini ba.

Maimakon marawa Sin baya wajen yi wa tufkar hanci tare da fitar da duniya daga halin da ta shiga, kasashen duniya dake kiran kansu manya, sun nuna karara cewa, ba sa kaunar zaman lafiya ko kwanciyar hankalin duniya. An ga yadda tun bayan barkewar rikicin, Amurka da kawayenta ke ci gaba da samar da makaman yaki ga Ukraine, tare da kakabawa Rasha takunkumai.

Ko a baya bayan nan, sun tashi taron kungiyar G7 da matakan kara sabbin takunkumai kan Rasha.

Shi wannan ba bangaranci ba ne? Shin makaman da suke samarwa ba zubar da jini da asarar rayuka za su haifar ba? Shin takunkuman da suke sanyawa, ba kunchin rayuwa za su haifar ga al’umma ba?.

Ba sai an fada ba, hanyar da kasar Sin ta dauka ita ce za ta kai ga samar da zaman lafiya da takaita asarar rayuka da dukiya. Yayin da tallafin soji da takunkumai za su kai ga ci gaban yaki da asarar rayuka da kara dagula yanayin duniya. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Next Post
Na Gaji Bashin Biliyoyin Kudi -Sabon Gwamnan Zamfara

Na Gaji Bashin Biliyoyin Kudi -Sabon Gwamnan Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version