Yadda Kimiyya Ke Da Tasiri A Rayuwarmu Ta Yau Da Kullum

Kimiyya

Daga Ammar Muhammad,

A wannan makon shafin kimiyyar zamani da ke zuwa muku a duk ranar Lahadi, zai yi duba ne zuwa ga yadda kimiyya ke da tasiri a rayuwarmu ta yau da kullum. A halin yanzu a rayuwar da muke ciki, ba yadda za ka raba ta da kimiyya. Yanzu rayuwa kacokaf ta dogara ne da kimiyya wajen gudanar da ita da kuma ci gabanta. Ko a bukatunmu na yau da kullum wajen gudanar da su muna da bukatar kimiyya domin tabbatar da mun samu nasarar kammala su. Kuma wani abu shi ne a yadda rayuwar ke tafiya, babu wani lokaci da ke nuni da cewa bukatar dan Adam zai ragu daga bukatar wannan kimiyyar, illa ma iyaka karuwa da bukatar ke yi a koyaushe.

Misali; dan Adam a yanzu yana amfani da abubuwan da kimiyya ya samar wajen yin tafiye-tafiyensa na yau da kullum. Dan Adam na da bukatar kimiyya wajen sadarwa, wajen neman ilimi, wajen kasuwanci da kuma ingantattar rayuwa mai cike da walwala. Sai dai duk da amfanin kimiyya a rayuwarmu ta yau da kullum, rashin amfani da shi yadda ya dace yana haifar da dimbin matsaloli tun kama daga gurbacewar iskar da muke shaka saboda yadda kimiyya ya samar da wadansu kayayyaki da ake amfani da su a kamfanunnuka wajen samar da abubuwan more rayuwa, wanda hakan ke gurbata iskar da dan Adam ke shaka. A don haka, yadda ake amfani da kimiyya na da matukar hatsari ga rayuwarmu. Wannan zancen gurbacewar iska a babin kamfanunnuka ma ke nan, banda wadansu bangarori na rayuwa daban-daban. Wadannan dalilan ne ma ya sanya wadansu masana kimiyya suke ganin yanzu lokaci ya yi da ya kamata masana kimiyya su yi nazarin irin duniyar da za a fuskanta a wadansu shekaru masu zuwa. Domin a halin yanzu ci gaban kimiyya gudu yake yi, kuma matsalolin da yake haifarwa ga rayuwa yana da hatsarin gaske.

Bari na ba ku misali; a kimiyyance ana iya amfani da kwayoyoin masara wajen samar da sinadarin ‘ethanol’, shi kuma wannan sinadarin ana iya amfani da shi wajen samar da man fetur. A nan kawai zamu fahimci cewa daga masara a kimiyyance za a iya samar da man fetur, wanda mai din nan za a iya amfani da shi a wurare daban-daban da suka shafi rayuwa jama’a; tun kama daga kan motocin da muke amfani da shi, Janareto domin samar da wutar lantarki, da ma sauran kayayyakin da suke da bukatar man fetur din. Kuma kamfanunnuka za su iya amfani da wannan fasahar cikin kudi mai sauki. Amma idan har aka ce za a komawa wannan fasahar kimiyyar wajen samar da man din, a karshe za a bar dan Adam babu abin da zai ci isasshe, kuma wannan zai haifar da yunwa a duniya. Domin bukatun noman zai kara yawa, kuma sarrafa shi zuwa man fetur din zai karu, wanda a karshe zai zama abinci ya yi karanci a tsakanin mutane, wanda wannan kowa zai fahimci illar da za iya samun mutane.

Domin warware shubuha akan kimiyya bari na yi wannan zance, zancen shi ne kimiyya a kashin kanta, ba ta da illa, sai dai illarta shi ne yadda al’umma ke amfani da kimiyyar domin cimma bukatunsu na rayuwa, inda a karshe yake haifar da matsaloli da za su cutar da rayuwar jama’a. Misali; dan Adam na da bukatar hasken wutar lantarki domin sarrafa wadansu kayayyakin bukatun rayuwar al’umma ta hanyar sarrafa motoci, haskaka gida, amfani da komfuta, da sauran su, amma kuma za ka samu dan adam na amfani da irin wadannan kimiyyar wajen gurbata rayuwar al’umma da haifar da matsaloli.

Daga cikin amfanin kimiyya a rayuwarmu, akwai bangaren noma, wanda idan ba abinci ba rayuwa.  Shiyasa a dangaren sha’anin noma, zamu fahimci yadda kimiyya ke ba da gudummawa sosai wajen saukaka ayyukan noma tun kama daga huda, shuka, gyara, girbi da kuma sarrafa shi zuwa kasuwa ko zuwa gida. Inda yanzu cikin sauki mutane kalilan za su yi amfani da kayayyakin da kimiyyar ta samar wajen yin ayyukan tafka-tafkan gona da zai samar da dimbin abincin ga miliyoyin al’umma domin amfanar su. Yanzu akwai dimbin kayan aiki na zamani da ake amfani da su tun kama daga huda, shuka irin noman, bai wa gonar ruwa (a lokacin noman rani) da kuma cire abin da ka shuka a karshe. Kuma ci gaban kimiyya ne ya sanya yanzu aka kirkiri sabbin irin-shuka da wanda ke saurin girma domin a amfana da shi cikin kankanin lokaci ba kamar a da ba. Kuma yanzu manoma suna da damar amfani da takin zamani da kimiyya ta samar wajen sanyawa shukar su, domin noma lafiyayya kuma ingantattan abinci.

Idan shukar mutum ta kamu da cuta, yanzu kimiyya ta samar da magungunan da ake amfani da su wajen magance wannan cutar. Kuma har wala yau akwai sinadaran da ake amfani da su domin inganta hatta ita kasar da ake amfani da ita wajen yin noman. A halin yanzu, manoman rani za su iya amfani da kimiyya wajen noma ingantaccen shuka kuma cikin sauki ba tare da daukar dogon lokaci ba. Hatta bai wa shukan ruwa, yanzu akwai injinan da dake ba shuka ruwa cikin sauki kuma akan lokaci ba tare da daukar lokaci mai tsawo ba, ko da kuwa kasar busasshiya ce sosai.

Yana da matukar wahala mutum ya dawwana dukkannin amfani da tasirin kimiyya a wannan zamanin namu a shafi jarida guda, amma a takaice, kimiyya a wannan zamanin namu yana da muhimmanci domin tasirinsa da amfaninsa ba kawai ga dan Adam ya tsaya kadai ba, hatta ga muhallin da dan Adam din ke rayuwa tasirinsa yana yin naso.

Zamu ci gaba a mako mai zuwa.

Exit mobile version