Yadda Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Domin Yin Belin Dilan Ƙwaya A Kotu - Rahoto
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Domin Yin Belin Dilan Ƙwaya A Kotu – Rahoto

byMuhammad
2 months ago
Kano

Ana zargin Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, da karɓar kuɗin toshiyar baki har Dala 30,000 daga wani ƙasurgumin dilan ƙwaya, Sulaiman Danwawu, domin yim belinsa a kotu, kamar yadda rahoton da Hukumar Tsaro ta Ƙasa (SSS), ta fitar.

An taɓa ayyana Namadi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo saboda zargin aikata zamba a shekarar 2013, kafin daga bisani Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa shi a matsayin Kwamishina.

  • An Dawo Da Wutar Lantarki A Dukkan Kauyukan Da Aka Tafka Ruwa Da Iska A Beijing
  • Kongo Na Neman Goyon Bayan Nijeriya Kan Shugabancin UNESCO

Majiyoyin SSS daga Abuja sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa an gudanar da bincike a asirce kan batun, kuma hukumar ta shawarci gwamna da ya sauke Namadi daga muƙaminsa.

Yadda Ake Zargin Ya Karɓi Kuɗin

A cewar rahoton, Namadi ya karɓi Dala 30,000 kafin ya amince ya tsayawa Danwawu a kotu.

Wannan na nufin ya ɗauki alhakin cewa Danwawu ba zai tsere ba bayan bayar da shi beli.

Bayan mutane da dama sun nuna ɓacin ransu kan al’amarin, gwamna Abba Yusuf ya kafa kwamiti domin bincikar lamarin, tare da umarnin a miƙa masa rahoton cikin mako guda.

Gwamnan, ya taɓa goyon bayan jami’an tsaro wajen kama Danwawu, kuma ya umarci NDLEA ka da su sake shi.

Wani jami’i ya ce: “Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauki wannan aiki na Kwamishina a matsayin cin fuska ga gwamnatinsa da kuma yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.”

An ruwaito cewar gwamnatin Jihar Kano ta shirya wani shiri a ɓoye domin kama Danwawu, wanda Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Bakori ya jagoranta.

Me Ya Sa Gwamnan Bai Kore Shi Ba?

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi niyyar korar Namadi nan take, amma ya dakatar da hakan bayan ganawa da jagoran NNPP, Sanata  Rabiu Musa Kwankwaso, wanda shi ne ya bayar da sunan Namadi domin naɗa shi a matsayin Kwamishina.

Wasu majiyoyi sun ce gwamnan bai so naɗa Namadi ba tun da farko, amma saboda girmamawa da biyayya ga Kwankwaso ya ba shi muƙami.

Wani hadimina cikin gwamnatin ya ce: “Kwamishinan yana matsala da shugaban ƙungiyar direbobi ta NURTW, Kabiru Labour, saboda ƙoƙarin tilasta musu biyan harajin Naira 500,000 a kowane wata.”

“Haka kuma, Kwamishinan na gudanar da harkokin ma’aikatar ba tare da haɗin kai da sakatarenta Abdulmumin Babani ba. Saboda haka, sama da takardu 30 daga Ma’aikatar Sufuri ba su samu amincewar gwamna ba.”

Majiyar tace saboda rashin jituwa da kuma gazawar shugabancinsa, gwamnan yanke kauce wa hulɗa da ma’aikatar.

Martanin Namadi

Da aka tambayi Namadi, ya ce: “Ban san da wancan zargin ba, kuma ba gaskiya ba ne.”

Sai dai ba da jimawa ba, Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Waiya, ya ce an kawo ƙarshen lamarin.

Cikin fushi ya bayyana cewa: “Wane irin aikin jarida kake yi ne haka? Me ya sa kake bin wannan batun babu ƙaƙƙautawa? Me kake nema ne?”

Yadda Lamarin Ya Samo Asali

A ranar 24 ga watan Yuli, DAILY NIGERIAN ta fyadda Namadi ne ya taimaka wajen belin Danwawu, bayan kotu ta sanya masa sharuɗa masu tsauri.

A ranar 16 ga watan Yuli, kotu ta amince da buƙatar beli, amma ta buƙaci sai an samu Kwamishina a cikin majalisar zartarwa ta Jihar Kano da zai tsaya masa, tare da biyan Naira 5,000,000.

Namadi ne ya tsaya masa, ta hanyar rubuta wasiƙa zuwa kotun a ranar 18 ga watan Yuli, 2025, yana neman a amince masa domin ya tsawa wanda ake zargi.

Wasiƙar da jaridar DAILY NIGERIAN ta samu ta nuna cewa ya ce: “Ina roƙon kotu mai daraja da ta yadda na tsaya wa wanda ake tuhuma da laifi, Sulaiman Aminu, wanda aka bayar da beli kan kuɗi Naira 3,000,000 da kuma wanda zai tsaya masa. Sannan ya ajiye Naira 5,000,000.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya
Labarai

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba
Labarai

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci
Labarai

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Next Post
Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto

Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version