Mahdi M Muhammad" />

Yadda Magidanci Ya Yi Tattakin Kilomita 420 Bayan Samun Sabani Da Matarsa

Wani magidanci dan kasar Italiya da ya fita shan iska a wajen harabar gidansa don huce zuciyarsa bayan samun sabani da matarsa an same shi kilomita 420 daga gidansa, bayan ya yi tafiyar tsawon mako guda.

Mutumin mai shekaru 48 daga Como, wani gari a arewacin Milan na kasar Italiya, an ba da rahoton cewa, ya yi rikici da matarsa wata rana a karshen watan jiya, kuma ya fice daga gidan don shan iska a waje da kuma wanke zuciyarsa. Ba zako ba tsammani, kawai sai aka ji labarin yana tafiya ba tsaya wa. An samo nasarar tsayar da shi kawai bayan mako guda, a inda ‘yan sanda suka dakata da shi da motar su a Gimarra, a gabar tekun Adriatic, kilomita 418 daga garinsu.
Rahotanni sun ce, ‘yan sandan suna sintiri a kan titunan garin Gimarra, don tabbatar da cewa mutane suna bin dokar hana yawo a duk fadin kasar da aka sanya a Italiya, lokacin da suka lura da wani mutum shi kadai da ke tafiya da karfe biyu na dare. Sun tsayar da motar, suka yi masa ‘yan tambayoyi, sannan suka karasa da shi ofishin ‘yan sanda da ke yankin, inda suka gano cewa matarsa ta neme shi ta rasa. A dai-dai wannan lokacin ne mutumin ya basu labarin tarihin tafiyarsa.
Mutumin ya ce, ya yi fada da matar sa ne mako guda, a inda ya bar gidan ya fita waje don shan iska yana tafiya da kuma huce zuciyarsa,  tafiyar da bai tsaya ba kenan sai a wurin da aka tsince shi. Ba tare da daukar kowane irin jigilar kaya ba, mutumin ya yi tattakin kusan kilomita 420 a kafa, cikin kwanaki bakwai kawai. Wannan matsakaici kenan na kilomita 60 a rana.
A cewarsa, “Ban yi amfani da kowace hanyar sufuri ba. Duk tsawon kwanakin nan na rayu a kan abinci da abin sha ne da mutane masu kirki suka ba ni a kan hanya. Ina lafiya tare da dan gaji ne kawai.”
Bayan sun ji bayanin nasa da ba a saba gani ba, sai ‘yan sanda suka yanke shawarar su sake shi, amma sai da suka fara sanar da matarsa, da kuma cin sa tarar Yuro 400 ($ 490) saboda karya dokar hana yawo. ‘Yan sandan sun samar ma shi da daki a wani otal da ke yankin, inda ya kwana har sai da matarsa ta zo ta dauke shi.

Exit mobile version