Idris Aliyu Daudawa" />

Yadda Mahaifi Ya Kashe ‘Yarsa Don Zai Kara Aure

Labarinj maza suke kashewa saboda soyayya, wani lokaci su kan daure kai, wani kuma a yi tsammanin abin  ba gaskiya bane. Amma kuma abin ya faru ba wasa bane akuma rayuwa, lokacin da Thomson Agena ya kashe wani saboda ya samu soyayyar wata mace. Wannan laifin da ya aikata ya bar iyalai abokai,makwabta, suna ta yin mamakin abin, da kuma shakku, saboda wadda abin ya shafa’yar shekara 6 ce wadda kuma ta rasa mahaifiyarta shekaru biyu da suka wuce.

Soyayya da abubuwan tada hankali

Rayuwar Thompson Agene mai shekar47 wanda dan asalin Karamar Hukumar Awe ne cikin jihar Nasarawa, abubuwa masu daure kai da ban al’ajabi sun jagula ma shi rayuwa. Shi dai Agene kafinta ne, ta hanyar ce kuma yake yin rayuwar shi, tun lokacnn daya kammala makarantar sakandaren kimiyya ta Lafiya a shekarar 1988, ya auri matar shi Cecelia wadda ita kuma ‘yar Karamar Hkumar Obi ce ta jihar Nasarwar a shekarar 2005, sun kuma samu haihuwarsu ta farko, inda suka samu’ya mace da suka sa ma ta suna Mercy a shekarar 2011. Bayan nan kuma sai suka fara samun matsala da samun wata haihuwar, har sai shekarar 2016 ta karasamun wani cikin, amma kuma sai ta kamu da rashin lafiya wadda tayi sanadiyar rasuwarta.

Thompson ya bayyanawa jaridar The Sun ta ranar Asabar cewar, yadda ya rasa matarsa a dalilin mutuwa ta hanyar haihuwa, awatan Afrilu 29, 2016. Cikin matar shi na biyu, sauran ‘yan kwanaki kadan suka rage a haihu, lokacin da ya kai matarshi babban asibitin Lafiya,saboda  a samu taimakawa yadda zata haihu.. Sai ya koma gida domin yin wani tsari, domin shiri na tarbar uwa da jaririya. ‘’Sai n ace wata kanwata ta taimaka mata idan ta dawo gida, nayi ma gida fenti wanda ke da ban sha’awa. Na yi dukkan abubuwan da suka kamata don gani abin ya tafi kamar yadda ya kamata, ga ita matata da kuma abin da Allah zai sa a haifa.’’

A asibiti ta sha wuyar nakuda daga karshe dai ta haifi da namiji mai nauyin kilogiram fiye da hudu, 4.6kg amma kuma sai ta ci gaba da zubar da jini, ta hadu da matsalar da mata kan samu bayan sun haihu, wajen karfe 1 da minti 23 na dare sai ta mutu saboda rashin isasshen jini.

Kamar yadda y ace asibitin basu da magunguna wadanda ake bukata saboda tsayar da zubar da jinin da matar ta shi take yi, ‘Sai  na tafi waje domin  na sawo magani, saboda ba wanda ya fada mani  cewar ta mutu’’.

Lokacin da yake wasi wasin daukar matakin da zai iya kai abin zuwa ga Hukuma, saboda rashin kulawa da kuma rashin sanin aiki, amma sai aka hana shi yin hakan, saboda wasu sun dauki irin wannan matakin.

‘’Na tsayar da shawarar barin komai ga Allah saboda ba wani abin da zan yin a dawo da ita’’

Bayan mako daya akwai wani abin bata rai daya faru sai jaririn yam utu shi kuma nan da nan aka rufe shi a kauyen.

Lokacin da dalilan da suka yi sanadiyar mutuwar matar shi da kuma dan shi, abin ya daure ma shi kai, bai da wata shawarar da zai yanke dangane da hakan.

Rayuwar aure mai daure kai

Shekara daya bayan mutuwar matarshi Angela ya yi rajistar karatun Diploma a kwalejin fasaha ta jihar Nasarawa, inda ya hadu da Joy Orkuma, wadda ‘yar asalin Karamar Hukumar Guma ta jihar Benue, nan da na suka fara soyayya, ba kuma da dadewa bane sai ta samu ciki.

Agena yana matukar son yarinyar da ya hadu da ita, don haka tuni dama ya dauri aniyar yin duk yadda zai iya yi saboda, ya samu kanta ta yarda ya aure ta, sai Orkuma ta ce sai ya kashe ‘yar shi mai shekaru shida.

Da dare ranar 22 ga watan Fabrairu sai Agena ya amince da shawarar sabuwar budurwarshi, ya dauki’yar shi tana cikin barci sosai, ya jefa ta cikin rijiya.

Washegari aka samu gawarta, lokacin dawani manomi da ake kira dasuna Joseph Kula yaso yai amfani da rijiyar, nan da nan sai ya kwarma ihu makwabta suka fito aka ciro gawar yarinyar daga cikin rijiya.

Agena tun lokacin da ‘yansanda suka kama shi da kai shi kotu, sai ya danganta matakin na shi daya dauka akan, saboda tsananin soyayyar da yake yi ma sabuwar budurwar shi, ga kuma maganar rasa ‘yar shi wadda yayi, ya kuma ce  ai tayi ma shi barazanar zata zubar da cikin da take dauke da shi, su kuma bar soyayyar tasu, shi kuma baya son haka din ta faru.

Wanda ya aikata lifin ya bayyana cewar ita budurwar ta shi, ta ce batason ta hada iri da wadda take mayya ce, za kuma ta dauki mataki na zubar da cikin da kuma barin soyayya da shi, idan har ya ki daukar matakin.

lokacin da da jaridar Sunday ta yi magana ta waya da Joy Orkuma wadda yanzun ta gudu, bata nuna wani tausayi ba akan shawarar data bada, cewar ta nuna kiyyayyar ta ce ga yarinyar bmai shekaru 6, da tace halayenta basu dace da shekarun taba,’’Na fada ma shi idan har yana son aure na dole ne ‘yar sa Mercy ta bar gidan mahaifinta’’ haka ta kara jaddadawa. ‘’Saboda koda yaushe ina ganin ta a mafarki na, duk lokacin dana kwan gidan Babanta, lokacin da kuma na samu ciki, sai nayi tunanin idan na haihu a gidan, ita Mrecy na iya kashe abin da na haifa’’.

Ta ce ita bata join wani abu dangane da yarinyar da aka kshe saboda, ita  a cewar ta wannan ba mutum bace, yadda mahifinta ya kashe ta, shine abin da ya kamata ya faru.

Da ganin idanun shi mahaifin Mercy ka san akwai tashin hankali tattare da shi, wanda shi ba wai ya damu bane akan kisan kan da yayi, amma kuma yadda ita matarshi ta mutu, ‘’Matata ba zata taba yafe mani bat un daga cikin kabarinta, bai nuna damuwa da irin soyayyar da take nuna mani ba’’.

Kamar yadda ya bayyana Joy Orkuma ta nuna kiyayya ga ‘ya ta Mercy tun farko, da kuma ci gaba da bada labarun karya, dangane da ita, ‘’ Na yi dana sanin amfani da shawararwarinta marasa kyau

Kanin wanda ya aikata laifin Dabid Agena ya bayyana wasu labarai , wadanda sha bam ban da wadanda aka sani, ya ce, Yayan na shi ba shi ne mahaifin Mrcy ba, ya ci gaba da bayanin cewar marigayiya Crcilia Agena tana da ciki wata biyu, lokacin data auri dan’uwan shi.

‘’Mun san duk yadda wadannan abubuwan suka faru, amma wannan labari ne mai tsawo kamar yadda ya ce,  ‘’Ban son na yi magana dangane da hakan yanzu, ba wani mutum mai hankali, wanda zai kashe’yar shi, saboda budurwar shi, ina nufin ta yaya wani zai abu irin wannan? Cecilia ita ‘yar mutunci ce, mai tsoron Allah da kuma aiki tukuru, mata ce wadda ke son mijinta kwarai da gaske, maganar gaskiya ita ce duk suna son junansu. Ni ina mamakin wannan abin da ya faru’’.

Ya bada bayani akan takaddama dangane da wanene asalin mahaifin Mercy

‘’Akwai samari uku da suka hada da yayana wadanda suke neman Cecelia, amma lokacin data samu ciki, sai abin duk a aka samu rashin kwanciyar hankali, dangane da wanda yake da cikin. Amma sai ta ce dan’uwana ne, wanda saboda soyayyar daya ke mata sai ya yarda, suka yi aure, daga baya mun ji labarin cewar cikin ba nashi bane, daga nan aka fara samun matsala, amma kuma shi yayannawa da marigariayar matar tashi , suna son juna, bai kamata ba yayi abin da ya aikata saboda wata mata’’.

Exit mobile version