A yayin da masu maganin gargajiya ke cigaba da bada gudunmawarsu ta hanyar bayar da magunguna ga marasa lafiya shekaru dubbai da su ka gabata a Najeriya da sauran sassan duniya, wani maganin gargajiya da ke zauna a garin Jos, babban birnin jihar Filato, mai suna Malam Hassan Ahmed Mu’azu, a kullum ya na duba marasa lafiya sama da mutum 200 tare da ba su magungunan cututtukan da su ke damun su ba tare da fada mu su abinda za su biya ba, sai dai kawai abin da su ka yi niyya su ka ba shi.
A lokacin da Wakilin LEDERSHIP A YAU ya isa wajen da Malam Hassan da ke duba marasa lafiya tare da ba su magunguna a garin na Jos, ya ganewa idonsu yadda mutane maza da mata su ka yi layi, don karbar magani a yayin da Hassan tare da sauran ma’aikatansa ke kokarin bai wa mutanen magungunan cututtukan da su ka zo karba.
Da ya zantawa da wakilinmu, Malam Mu’azu ya bayyana cewa a kalla ya kai kusan shekara 40 ya na bayar da maganin gargajiya a wannan gari.
‘’Kamar yadda ka ganewa idonka, abin da muke yi. Mu bama tsawala masu zuwa karbar magani, saboda ba mu ne masu maganin ba, Allah ne da maganin. Don haka duk abin mutum, ya bayar haka muke karba. Wani zai zo da N100, wani zai zo da N50, wani ma zai zo babu kudin, amma sai mu bashi maganin ya tafi, mu dai albarka mu nema’’.
Ya ce, ya na samo wadannan magungunan gargajiya ne, daga wurare daban daban, kamar daga Gombe da Filato da Kano da Sakkwato wasu har daga Nijar, ake kawo su a motoci, a sauke a wannan waje.
Ya ce, ya na da kyakyawar dangantaka da likitocin zamani. Domin idan abu yafi karfinsa, ya kan ce aje wajensu. A maganin gargajiyar ma tun da kowa akwai inda yafi kwarewa, idan aka zo ya kan ce aje wurin wane.
‘’Babu abin da zai cewa ubangiji, kan wannan sana’a sai dai godiya. Domin tun da na fara wannan sana’a, kullum cikin nasara nake, har ya zuwa wannan lokaci. Domin a kalla ina da ma’aikata sama da 30, maza da mata. Kuma ina biyansu kullum, suna zuwa su ciyar da iyalansu’.
Ya ce babu shakka maganin gargajiya yana da matukar mahimmanci. Domin ko a cutar annobar Kurona, an fahimci mahimmancin maganin gargajiya, a duniya. Don har yanzu ba a ce ga maganin wannan Annoba na asibiti ba, sai dai na gargajiya. Don haka wannan abin alfahari ne, a wajen masu sana’ar maganin gargajiya.
Ya ce babban burinsa, shi ne ya kafa asibitin maganin gargajiya, don ya cigaba da taimakawa al’umma’’.
Da yake zantawa da wakilinmu, daya daga cikin ma’aikatan wannan wuri, mai suna Muhammad Sani Abdullahi Dari, ya bayyana cewa ya kai sama da shekara 23, yana aiki a wannan waje.
Ya ce a wannan waje, suna da wadanda suke aiki da rana, kuma suna da wadanda suke aiki da dare, har zuwa karfe 9 na dare.
Ita ma da ta ke zantawa da wakilinmu, daya daga cikin matan da suke aiki a wannan wuri, mai suna Zainab Muhammad Inuwa cewa ta yi, ta dade tana aikin bayar da magani, a wannan waje.
Ta ce mata sun fi zuwa wannan waje da safe, a yayinda maza suka fi zuwa, da yamma.
Da take zantawa da wakilinmu, wata mata da ke zuwa wannan waje karbar magani, mai suna Rabi Inuwa Abdullahi, ta bayyana cewa ta kai sheraka 4. Tana zuwa wannan waje kabar maganin cutattukan mata da dai sauransu. Ta ce, a na samun nasara, kuma ta na bayar da sadaka ne kawai.
Shi ma Sulaiman Abubakar ya shewada wakilinmu cewa, ya kai wata daya yana zuwa da iyalansa, karbar maganin ciwon yara a wannan waje. Kuma suna jin dadi, kuma tun da yake zuwa, ba a taba ce masa ya kawo kaza ba, sai dai ya bayar da abin da ya yi niyya.