Ibrahim Ibrahim" />

Yadda Makarantar HAMI Ta Dade Tana Daukar Nauyin Karatun Marayu Kyauta

Makarantar tunawa da Margayiya Hajiya Hauwa’u, wanda a turance ake kira da Hauwa’u Memorial International School (HAMI), dake kan layin Alkalawa Tudun Wada dake Karamar hukumar kaduna ta kudu, makarantar ta kwashe tsawon shekaru 5 tana daukar nauyin karatun Yara Marayu, wadanda suka rasa Iyayensu, da kuma ‘Ya’yan marasa galihu.

Makarantar wanda wani bawan Allah mai suna Alhaji Musa Bello Abdullahi, ya samar sadakatul jariya domin tunawa da Mahaifiyarsa Margayiya Hajiya Hauwa’u Bello,  a dalilin hakan ne ya gina makarantar domin daukar nauyin karantar da Yara marayu da kuma marasa gajihu, wanda a halin yanzu makarantar na da tsawon shekaru 5 kenan da kafuwarta, kuma a zuwa yanzu makarantar ta sami nasarar  yaye Dalibai kima dubu 2000, tun bayan kafuwarta, sannan a halin yanzu akwai sama da Dalibai dari 300, dake karatu a matakin ajin karatun  firamari a cikin wannan makaranta.

LEADERSHIP A Yau, ta yi tattaki na musamman domin kai ziyarar gani da ido a wannan makaranta.  A inda  ta sami damar zantawa da Shugaban Malaman Makarantar, Hajiya Hauwa Salanke, wanda ta shaidawa wakilinmu cewa, “Alhamdulillah! Cikin ikon Allah, a halin yanzu muna samin nasara sosai, musamman irin gudunmuwar da muke samu daga shi kansa wanda ya gina wannan makaranta wato Alhaji Musa Bello Abdullahi, domin a ko da yaushe kafarsa a bude take domin ganin ya na ci gaba da tallafa ma daukacin Daliban da suke karatu a wannan makaranta, ta fanin ganin sun wadatu da litattan karatu, kayan makaranta, abinci da ake basu idan sun fita hutun rabin sa’a, da dai sauran tallafin yau da kullum.”

Hajiya Hauwa Salanke, ta kara da bayyana cewa, “ an gina wannan makaranta domin daukar nauyin karantar da Yara marayu wadanda suka rasa Iyayensu, da kuma yara wadanda Allah bai hore ma Iyayensu abin da zasu dauki nauyin karatunsu ba. Kuma a halin yanzu wannan makaranta na da tsawon shekaru biyar kenan da kafuwarta, sannan a tsawon wannan shekaru, mun sami nasarar yaye Dalibai a kalla guda dubu 2000, wanda suka hada da Yara Maza da Mata, kuma a halin yanzu akwai sama da Dalibai dari 300 dake karatu a cikin wannan makaranta.”

Wakilinmu ya tambayi Malama Hauwa Salanke cewa ko akwai wani tallafi da suke samu daga bangaren gwamnati ko wasu Al’umma?

“Gaskiya babu wani tallafi da muke samu, domin wannan makaranta na karkashin Gidauniyar tallafa wa Marayu da masu karamin karfi, wanda a turance ake kira da foundation, kuma wannan gidauniya ita ke daukar nauyin duk wasu abubuwa da suka shafi kula da wannan makaranta da kuma su kansu Malamai da Dalibai.”

Itama da take nuna godiya da kuma nuna farin cikinta , daya daga cikin Iyayen Daliban, Malama Hasiya Rabiu, ta bayyana ma wakilinmu cewa,” Gaskiya babu abin da zamu ce sai dai Allah ya saka ma wannan bawan Allah da alkhairinsa, domin mu ya share mana hawayen rashin mazajenmu, saboda a maganar nan da nakeyi da kai, akwai ‘Ya ta dake karatu a wannan makaranta, domin kusan shekara uku kenan muna neman ma yarta wannan makaranta, amma Allah bai nufa ba, sai a wannan karo Allah ya nufa kanwarta za ta samu, domin duk shekara muna zuwa amma a makare an riga an rufe daukar adadin Yaran da za’a dauka.”

Malama Hasiya Rabiu, ta kara da bayyana cewa, “ Muna kira da sauran masu hannu da shuni wadannan Allah ya hore masu dukiya, da su yi koyi da wannan bawan Allah, wajen ganin sun sadaukar da dukiyoyinsu domin gina aikin Allah, saboda gobe lahira su sami yardar Allah, saboda duk mutumin da ya taimaka ma maraya, tamkar ya gina gida ne a cikin Aljanna. Gaskiya babu abin da zamu ce, fa ce Allah ya biyashi da gidan Aljanna.”

Shima a nasa bangaren, Malam Umar Zakariyya, wanda ya kasance daya daga cikin Iyayen Daliban, ya shaida ma wakilinmu cewa,” Muna godiya da irin wannan karamci da bawan Allah nan yayi mana, domin ya taimake mu sosai ta hanyar ganin ya baiwa ‘ya’yanmu ilimi kyauta fisabilillahi, gaskiya muna godiya, Allah ya biya shi da gidan Aljanna, Allah ya kuma jikan Mahaifiyarsa Hajiya Hauwa’u da gafara.”

Itama da take bayani, Malama Khadija Ibrahim Muhammad,  wanda ta kasance daya daga cikin tsofaffin Malaman wannan makaranta, ta bayyana ma wakilinmu cewa, tun farkon kafa wannan makaranta da ita a ka fara har zuwa wannan lokaci. Sannan ta bayyana irin jin dadinta da kuma godiyarta ga shi Shugaban wannan makaranta, a bisa irin jajircewarsa da kuma gudunmuwar da yake baiwa Al’umma a ko da yaushe. A cewarta, wannan ba karamin sadakatul jariya ba ce, wanda babu iya wanda ya san yawan ladarsa akan wannan aiki da yakeyi, sai dai Allah shi kadai.

Shima a nasa bangaren Shugaban sashin koyar da harshen turanci a makarantar, Malaman Kabir Bello, ya bayyana cewa, duk da kasancewarsa ba bahaushe ba, amma yana jin dadin yadda wannan bawan Allah ke tafiyar da dukiyarsa wajen taimakon Al’umma.  Sannan ya kara da bayyana cewa, suna samin nasara sosai wajen zakulo Dalibai masu hazaka da ilimi, wanda a cewarsa, a kusan kullum suna samin takardun daukan aiki daga bangarorin Malamai daga ko ina a fanin wannan jiha. Domin a cewarsa, ba wani abu ya janyo hakan ba, Illa irin kyakkyawar karamci na Shugaban wannan makaranta.

Tahir Aminu, dan shekara 8 da haihuwa, ya kasance daya daga cikin Daliban wannan makaranta wanda ya na aji biyu, ya shaida ma wakilinmu cewa, “ Ina jin dadi sosai idan ina karatu, sannan na gode ma wanda ya gina mana wannan makaranta, kuma muke yin karatu kyauta a ciki.”

Shi ma  da yake tofa albarkacin bakinsa, daya daga cikin makwabta wannan makaranta, Malam Abubakar Musa, ya bayyana yadda suke jin dadi da irin abin ci gaba na alkhairi da wannan bawan Allah ya kawo masu wannan unguwa.

Malam Abubakar Musa, ya kara da bayyana cewa, akwai daukacin masu hannu da shuni da yawa a cikin wannan Unguwa, amma babu wani wanda ya taba tunani gidana masu makaranta fisabilillahi kamar yadda wannan bawan Allah ya yi. Sannan ya bayyana cewa, irin taimakonsa ba a wannan makaranta kawai ya tsaya ba, hatta su wadanda suke makwabtaka da wannan makaranta yana bin su gida gida, yana basu tallafi a ko da yaushe.

Exit mobile version