Yadda Matan Karkara Za Su Amfana Da Shirin Noma

Kananan Manoman Nijeriya

Daga Abubakar Abba

Sashen samar da kudade da  ciyar da aikin noma gaba na Majalisar dinkin Duniya (IFAD) ya bayyana cewa, abinda a yanzu yake kara bunkasa mata da alummar dake a karkara  a wasu jihohin dake cikin kasar nan shine shigar su cikin shirin  sarrafa shinkafa  da a turance ake kira  ‘Out grower ‘ inda hakan ya sanya abin ya kara janyo ra’ayin su  na shiga noman shinkafa  a dsukacin fadin Nijeriya.

Shirin dai wata hadaka ce da akayi tsakanin Gwamnayin Tarayya da kuma kamfanin Olam dake a Nijeriya inda suka samar da shirin a shekarar  2015.

Shirin na  (VCDP) dabara ce ta sarrafa shinkfa a karkara inda manoman suka kafa kungoyoyin noma. Manoman zasu dinga tura ingantacciyar shinkafa su a kuma dinga basu damar samun kudi da adana ta da safarar ta  zuwa cibiyoyin da za’a dinga sayen ta wadanda kuma tuni an basu horo kan tsarin  (GAP) da kuma sayen shinkafar tasu.

Har ila yau, Kamfanin sarrafa Tumatir na dangote dake a cikin jihat Kano, ya yo irin wannan jarjejeniyar da manoman Tumatir  dake a jijar Kano.

Yadda shirin na sarrafa shinkafar na  out-grower yake yin aiki shine, kamfanin  Olam dake a Nijeriya shine yake samarwa da manoman kayan aiki, inda su kuma manoman, zasu samu damar samun kudi da adana shinkafar su da kayan da zasu yi jigilarta ta zuwa cibiyoyin da za’a sayi ta.

Ana sayen shinkafar ta manoman a cibiyoyin daidai da yadda farashin kasuwa ya kama, inda kuma ake turawa manoman kudin su a cikin asusun ajiyar su na bankuna a cikin awanni  48 bayan an gama ciniki.

Kamfanin da ya siya zai kuma ssrrafa ta zuwa yadda zata yi inganci don amfani da ita.

A cewar Mataimakin shirin aikin noma na kamfanin Olam Mista Reji George, tsarwar da akayi ta sayen shinkafar, jami’an gonar  Olam dake a cinkn surkukin kauyuka sune suke tafiyar da kungiyoyin.

Mataimakin shirin aikin noma na kamfanin Olam Mista Reji George, ya ce, “Wadannan jami’an su 30, sun bude asusuna a banki ga ko wanne manomi daya, yadda za’a dinga adanawa da kuma samun damar tare da tura kaya da kuma horon da aka bayar ga manomin dake cikin kungiyoyin.”
“Suna taimakawa ne don kada a karkatar da amfanin da kuma  kaucewa ayyukan yan na kama wadanda suke ci da gumin manoman.”
A cewar Mataimakin shirin aikin noma na kamfanin Olam Mista Reji George, shirin ya kama kwamitin kayyade farashi da kwamitin hadaka da ya kunshi daukacin masu ruwa da tsaki harda walilan manoman da aka dorawa nauyin yanke farashi kan yadda kasuwa ta kasance. Ya ci gaba da cewa,  manoman da suka shiga cikin shirin, sun amfana da tallafin kayan aikin gona na zamani da shirin ya tanadar   ta hanyar daukin kudi daga shirin ofishin jakadanci na kasar Japan.
Mataimakin shirin aikin noma na kamfanin Olam Mista Reji George, ya ce, shirin ya bunkasa tattalin arzikin manoman kuma an fara  bCDP ne a shekarar 2015 da manima guda  475, amma a yanzu,  sun kai yawan 22,734 idan akayi dubi kan  yadda suka karu zuwa manoma  35,000 kafin nan da shekarar 2020.

“A shekarar  2015, shirin ya yiwa mata manoma 106 rijista, inda kuma adadin ya karu zuwa    5,336 a shekarar 2019.
Mataimakin shirin aikin noma na kamfanin Olam Mista Reji George, ya ci gaba da cewa,
“Yawan manoman da suka shiga cikin kungiyoyin, suma sun karu   zuwa 1,164 daga 30 a shekarar 2015 kuma ayyukan na bCDP, anga yadda sarrafa shinkafar ya karu zuwa tan 3.68 sabanin kamar yadda aka tsara a 2 tan a shekarar 2015.”
A cewar Mataimakin shirin aikin noma na kamfanin Olam Mista Reji George, an samu karin kudin shiga numa yadda ake samu kan ko wacce kadada daya, sjima ya karu zuwa dala 1,115/Ha da kuma dala  673/Ha baki daya ga manoman dake a karkara.

Mataimakin shirin aikin noma na kamfanin Olam Mista Reji George, ya bayyana cewa,“Shirin ya kuma samar da dimbin ayyukan yi da ya kai 60 Mds/Ha, har ila yau, a shekarar 2018, ya tara  tan 47,418 na ingantacciyar shinkafa ga kamfanin na  Olam na satrafa shinkafar.

Exit mobile version