Yadda Matsalar ‘Service’ Ke Gallaza Wa Jama’a A Bankuna

Daga Mohammed Shaba Usman

Al’ummar Nijeriya sun fara bayyana takaicinsu kan yadda sha’anin layukan sadarwa ke haifar musu da matsaloli a galibin lokutan da suke zuwa na’urorin cire kuɗ i da aka fi sani da ATM.

Kalmomi irin su ‘matsalar network’ ko ‘matsalar serɓ ice’ ba kawai an saba da jin sub a ne a wurin masu mu’amala da bankuna, sun ma zama jiki da ƙarfi da yaji.

A ƙa’ida dai, an samar da na’urorin ATM ne domin sauƙaƙa wa jama’a harkokinsu na kuɗ i walau ta gefen biyan buƙatunsu na yau da kullum ko kuma hada-hadar kasuwancinsu amma abin ya zama kamar ‘an gudu ba a tsira ba’ a ‘yan kwanakin nan saboda matsalolin da ke tasowa a rashin ingancin layukan sadarwa da aka fi sani da ‘network’ ko ‘service’.

Sau tari wasu sukan je neman kuɗ i a na’urar a kan gaɓ a ko kuma buƙatar gaggauwa irin su biyan kuɗ in asibiti, biyan bashi, kai saƙo, amma sai buƙatarsu ta ƙi biya a dalilin wannan matsalar. Idan aka yi rashin sa’a, sai matsalar ta janyo asarar rai saboda asibiti sun ƙi taɓ a mara lafiya sai an biya kuɗ i kuma sabis ya ɗ auke a ATM, ko a rasa wata dama ta samun kwangila ko kasuwanci saboda an je neman kuɗ in sufuri a ATM babu sabis mutum ya makara sai a baiwa wani ko kuma haɗ a mutum faɗ a da masu bin sa bashib saboda ya kasa cika musu alƙawari saboda matsalar ATM.

A kan wannan, wakilinmu ya tattauna da wani abokin hulɗ a da Bankin G.T. a yayin da ya same shi a halin ɓ acin rai ya yi tagumi a gaban bankin yana ta zage-zage cewa ba su kyauta mashi ba. Ga kuma mutane su ma zaune duk su na jiran Sabis ya dawo su samu cire kuɗ i ta na’uran da ke ba da kuɗ i a bankin.

A cewarsa, ya shigo Kaduna ne da niyar ya zo ya sayi kaya ya koma a ranar, sai ga shi bai samu cire kuɗ in ba, “Na gaji da maganar rashin Sabis ɗ in nan tun da dai buƙata ta ba ta biya ba har yanzu, ba don tsoron ɓ arayin kan haya ba da na zo da kuɗ ina a aljuhu kawai ga rashin Sabis ga mutane cike a cikin bankin haka, ya sa ban samu cire kuɗ i a cikin bankin ba, jiya Jumma’ah (da ta gabata). Yanzu dai ya zama dole na zauna babu jira ko zan samu na cire kuɗ in yau, gashi gobe Lahadi 9da ta gabata). Ka ga idan ban yi sa’a ba sai ranar litinin kenan, amma gaskiya na gaji.”

Ga wani shi kuma ya ce ya san dai an tura mashi kuɗ i, amma bai ji alamar shigowar saƙon a wayarshi ba, yayanshi ne dai ya tura kuɗ in, “amma ba wannan ba, ni dai buri na samu na cire kuɗ i kawai na je na biya buƙatuna kawai tun da ka ga gobe ne sunan yaron da aka haifa min kuma da kuɗ in na zan sayi rago da kuma waɗ ansu hidimomi, amma ga ni har yanzu babu labari, kuma ba abin na je wani bankin ba ina iya zuwa kuɗ i ya ƙi fitowa. Ko kuma ya nuna min na cire amma kuɗ in ba su fito ba, hannun agogo ya koma baya, domin ya taɓ a faruwa da ni kwanakin baya can da su ka wuce, shi ne ya sa nake tsoron zuwa wani bankin, ga shi yau mako duk abin da ya faru sai ya kai Litanin, na ga kawai dole na yi haƙuri har layi ya zo kaina.

“Maganar Sabis dai a Nijeriya sai a hankali, na ma daina yarda, da akwai yadda za a yi mana (biyan kuɗ i) ba sai da Sabis ba gaskiya da ya fi mana, saboda kullum aikin kenan sai dai Allah ya yaye mana kawai, idan za ka cire kuɗ i wahala, idan ma sawa ne shi ma haka, kuma wannan Matsalar ba wai banki ɗ aya ba ce, kawai duk haka suke sai dai wani ya fi wani. Akwai sanda na je sa kuɗ i a Ecobank ina kan layi sai Sabis ɗ insu ya ɗ auke a nan na tsaya ina jiran su kusan sa a biyu akan abin da bai wuce minti 40 ba, saboda Allah hakan ya yi kyau kenan?,” ya tambaya.

Wani kuma cewa ya yi, “idan ka je wani bankin cire kuɗ i kuma ba bankin ka ba ne katin ka ya maƙale sai su cire su karya shi a maimakon su kai wa bankinka shi ya sa kowa ya gwammace ya tsaya a bankinshi ya cire kuɗ i kawai. Ka ga kuma bankin G.T. a Kaduna guda biyar ne kawai, ga shi wannan ya fi kusa da kasuwa. Muna so don Allah a taimake mu a gaya wa ma’aikatan bankin da su haɗ a kai su daina karya mana katin cire kuɗ inmu idan sun ga ba na bankin su ba ne don Allah”.

Shi ma wani mai suna Garba ya ce, akwai wata rana ya je cire kuɗ i ana gobe sallah ne ma ga layi haka nan ya tsaya sai da aka zo kanshi, ya saka katin sai aka ɗ auke wuta ga katin shi a cikin na’urar cire kuɗ i, ga kuma bankin sun tashi, sai dai “na gode Allah dai ina da wata hanyan kawai idan ba haka ba sai naji kunya. Aboki na ma wai shi ya kai karfe ɗ aya na dare anan kafin ya samu ya cire kuɗ i, to mu dai bamu sani ba ko cigaba ne ko kuma yaya ne to ga shi dai”.

LEADERSHIP A Yau Juma’a ta nemi jin tab akin wani ma’aikacin banki day a nemi a ɓ oye sunansa game da matsalar inda ya yi tsokaci kan yadda lamarin yake.

“Gaskiya ne mutane na kawo kukansu kullum akan sun je cire kuɗ i a na’uran dake ba da kuɗ i, amma kuɗ in ba su fito ba, kuma sun sami alamar saƙo ta wayarsu cewa sun cire kuɗ i, ko waɗ anda katin su ta maƙale a cikin na’uran cire kuɗ in, ba wannan kawai ba, wasu ma sun tura kuɗ i, amma ba su sauka a ma’ajiyar waccan ba, ga shi dai mun tura kuɗ in amma shi wancan bai ji sako ta wayarshi ba, wani ma kuɗ in ya shiga saƙon ne dai ba su gani ba.

“Duk ka ga wannan abubuwan da ke faruwa daga Sabis ne, kuma abu ne wanda kowa ya san da shi, idan dai kana Nijeriya sai dai Allah ya yaye mana. Amma ka ga maganar an tura ma kuɗ i kuma ba kaga saƙo ta waya ba, shawara ta ita ce, ka je bankin da kanka, saboda wani lokacin kuɗ in ya shiga, amma saƙon wayar ne bai zo ba.

“Akan waɗ anda su ka je cire kuɗ i kuma sako ya shiga wayarsu cewa sun cire kuɗ i kuma kuɗ in bai fito ba, su yi hakuri wani kana wurin kuɗ inka za su dawo, idan kuma ka jira na ɗ an wani lokaci bai dawo ba, to ka shiga cikin bankin ka yi mana bayani, In sha Allah za mu san yanda za a yi.

“Sai kuma maganar karya katin cire kuɗ i na ATM gaskiya ban san da ita ba gaba daya, mu dai haƙuri za mu yi ta yi da juna kowa ne lokaci.

“Kuka dai iri-iri wani ma an ɗ auki katin shi an je an cire kuɗ i, idan ya fara bayani sai ka ga bai da gaskiya saboda ya saba ba wani katin ya ciro mashi kuɗ i, wata rana ya yi sakaci wannan ya ɗ auki katin ya cire kuɗ i shi kuma bai sani ba, shi ya sa komai sai mun bi a hankali.

“Abokan cinikayya don Allah ku ƙara haƙuri dai muna nan muna ta gyara, kuma ga wata hanyar da mutane za su bi mafi sauƙi wajen tura kuɗ i ma’abokanan cinikayyarsu, idan dai har kana da waya za ka tura ma wani daga N1,000 har zuwa 1,000,000 ta wayarka muna yin haka ne saboda yadda bankuna ke cika yanzu tunda mun fara ganin cewa Sabis na banki suna samun matsala, wani lokacin, ka ga ko ta na’urar dake ba da kuɗ i za ka iya ajiyar kuɗ inka amma, ba kowa ne ya yarda da shi ba sai dai wadanda suka fahimci na’urar.

“Mafi sauki dai shi ne ta waya ba wai kuma sai babbar waya ba, haka ko da ‘yar ƙaramar waya ce lambobi kawai za ka danna in har ka yi rajista da mu kana gida ba wai sai ka tafi zuwa banki ba. Kullum kana kwance a daɗ inka za ka yi ta biyan bashi sayen abubuwa kamar kuɗ in wata, sayen kaya daga wani kamfani, kuɗ in ruwa, abin kallo duk mai sauƙi ne, kawai kai dai asa maka shi a wayarka. Za ka ga zuwa bankinka zai ragu ba kamar da ba, sai idan ba ka da kuɗ i a ma’ajiyar kuɗ i, kuma za ka sa ma kanka kuɗ i saboda ka samu ka tura ma wasu idan lokacin ya zo. Mu karan kanmu ba wai muna so mutane suke cika bankin ba har wasu ma su zazzauna, mun fi son idan kazu a yi maza a gama ma duk abin da za ka yi nan da nan.” In ji shi.

Dama ba yau kaɗ ai jama’a suke ta fama da irin waɗ annan matsaloli na harkar hada-hadar bankuna ba, wanda akasarinsu talakawa abin ya fi shafa. A wasu lokutan ma kuɗ in mutum ne zai nuna ya fito ga shi har ya ga saƙo, amma sai su maƙale, ya gama jiransa ba su fito ba, kuma bai ji alamar an dawo da su ba, duk da haka idan yaje bankin don a maido masa da su sai a ce masa, sai bayan mako guda ya dawo, da haka dai wani sai ya kusa kaiwa wata guda. A kwai wanda na sani shi sai dai haƙura ya yi da ya gaji da jeka ka dawo. Don haka ya kamata hukuma ta shiga wannan lamarin domin a samu damar shawo kan lamarin.

Exit mobile version