Yadda Matsalar Tsaro Ta Kawo Cikas A Harkar Ilimin Arewa

Ilimin

Daga Muhammad Maitela,

Masana sun sha bayyana fargaba dangane da gibin da tabarbarewar tsaro zai haifar a harkokin ilimi a yankin Arewacin Nijeriya, yankin da kafin hakan ya sha fama da matsaloli daban-daban a fannin ci gaban ilimin wanda ake danganta wa da al’ada, yanayin tsarin zamantakewa da tattalin arziki, tare da halin ko-in-kula da mahukunta ke nuna wa kana kuma wadanda suka dabaibaye tsarin idan an kwatamta da sauran bangarorin kasar nan. Yayin da rikicin ya ta’azzara matsalar koma baya a harkar ilimin, wanda hakan ya jawo fargaba da rashin tabbas a zukatan dalibai da ma iyaye.

Bugu da kari, biyo bayan bayyanar matsalar rikicin Boko Haram da sauran kungiyoyin yan ta’adda wanda ya fadada girman matsalar koma baya a harkar ilimi musamman irin yadda kungiyoyin ke adawa da tsarin karatun boko, wanda suka kaddamar da kai munanan hare-hare a garuruwa tare da kona makarantu da sauran cibiyoyi da gine-ginen jama’a da na gwamnati al’amarin da ya jawo asarar rayuwar dubun-dubatar jama’a da tilasta wa miliyoyi kaura zuwa wasu yankuna, sannan ga asarar dukiya da biliyoyin naira wanda sakamakon haka ya ci gaba da mayar da hannun agogo baya.

Matsalar ta dauki sama da shekara 11 tana gudana wadda ta kawo cikas a kusan kowane bangaren rayuwar al’umma, haka kuma ta ci gaba da rikidewa daga wannan mataki zuwa wancan; daga Boko Haram zuwa barayin shanu, yan bindiga dadi, masu garkuwa da jama’a da sauran su, matsalar da ta keta alfarmar harkokin ilimi ta hanyar kashe malamai, kona daruruwan makarantu da kai wa wasu farmaki tare da yin awon gaba da dalibai don neman kudin fansa, kusan kowane yanki a Arewacin kasar nan.

Har wala yau, makarantu da dama ne wannan yanayin da ake ciki ya tilasta rufe su har sai abinda hali ya yi, wanda kafin hakan dama can makarantun a lalace suke, ga karancin kwararrun malamai, kayan aiki da sauran abubuwan inganta fannin. Al’amarin da ake jingina shi da rashin ko-in-kula daga bangaren wasu gwamnatoci a yankin.

A hannu guda, a karshen makon da ya gabata, shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Lawan, ya nuna fargabar da tabarbarewar tsaro za ta ci gaba da haifarwa, da koma baya a harkar ilimi a Arewacin Nijeriya, musamman irin halin da ake ciki yanzu wanda kullum fuskar ilimin sai dada yankwanewa take.

Sanata Lawan ya kara da cewa, yawan kai wa makarantu farmaki tare da yin awon gaba da daliban hadi da malaman su, sun kara dagula lissafi a fannin ilimi a yankin Arewacin Nijeriya. Sannan ya kara da cewa, matsalar ta kange yara a yankin Arewa damar neman ilimi, musamman yara mata, sakamakon ci gaban da yan ta’adda suke yi wajen kai farmaki tare da awon gaba da dalibai a makarantu.

Duk da wannan, shugaban dattawan ya ce bayan tiya akwai wata caca, ya ce har yanzu akwai fata saboda gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta na aiki tukuru wajen shawo kan matsalar tsaron tare da samun cikakken goyon bayan zauren majalisar domin daukar matakin bai daya na dakile matsalar tsaro a duk fadin kasar nan.

“Ko shakka babu wannan gagarumar matsala ce, kuma nayi imani abu ne da ya shafi kowane dan Nijeriya- ta shafi gwamnatin tarayya, jihohi tare da kananan hukumomi, sannan kuma ta shafi kowace kabila da yanki a fadin kasar nan.”

“Har wala yau kuma, za mu iya canja wannan hali da mu ke ciki na tabarbarewar tsaro a kasarmu. Matsala ce mai matukar sosa rai, musamman irin yadda ta jefa harkar ci gaban iliminmu cikin mawuyacin hali, wanda ya jawo kullum sai sace daliban makarantu, al’amarin da hatta dalibai mata ba su tsira ba.”

“Al’amarin da ya kai jefa harkar ilimin Arewacin Nijeriya cikin mawuyacin yanayin kuma kullum abin kara ci baya yake, wanda ya kai ga baya ga sace daliban sakandire hatta suma daliban makarantun Islamiyya ba su tsira ba.” In ji shi.

Exit mobile version